Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-13 16:18:49    
Kungiyar wasan daukan nauyi ta kasar Sin ta fuskanci lambobin zinariya cikin natsuwa

cri
Yanzu ana ci gaba da rahoto kan taron wasannin motsa jiki na Asiya a birnin Doha, babban birnin kasar Qatar. Za a yi takara don neman samun lambobin zinariya guda 15 a cikin gasannin daukan nauyi a wannan kar. An sa aya ga dukan gasannin daukan nauyi a ran 6 ga wata bisa agogon wurin, 'yan wasan daukan nauyi na kasar Sin sun kwashe lambobin zinariya 10, sun kuma karya matsayin bajimta a cikin gasanni 4. Saboda kasar Sin tana kan gaba a fannin wasan daukan nauyi a duk duniya, shi ya sa ba a ji mamaki ba da ta sami maki mai kyau a Asiya. Amma bayan da ta gama ayyukanta a Doha, kungiyar wasan daukan nauyi ta kasar Sin ta bayyana cewa, tana fuskantar matsaloli.

A gun taron wasannin motsa jiki na Asiya da ake yi a Doha, kungiyar wasan daukan nauyi ta kasar Sin ta lashe manyan 'yan takararta na Asiya wato kasashen Thailand da Korea ta Kudu. Amma dukan malamai masu horas da wasanni da kuma 'yan wasan daukan nauyi na kasar Sin ba su ji farin ciki sosai ba, a maimakon haka, suna ganin cewa, a zarihi kuma, kasar Sin tana fuskantar matsaloli a fannin wasan daukan nauyi a yanzu. Mataimakin babban malami mai horas da wasanni na kungiyar wasan daukan nauyi ta mata ta kasar Sin Ma Wenhui ya takaita fasahohin da kungiyarsa ta samu a Doha, ya ce,'Muna yin takara da 'yan wasan kasar Korea ta Kudu a cikin gasannin daukan nauyi na ajin kilo 75 ko fiye, mai yiwuwa ne za mu yi takara da 'yan wasan kasashen Kudu maso Gabashin Asiya a cikin gasannin daukan nauyi na azuzuwa na kasa-kasa, amma 'yan takararmu na sauran azuzuwa ba su zo daga kasashen Asiya ba, ga misali, 'yan takararmu na azuzuwan matsakaita sun zo daga kasashen Turai. Kada mun yi tsammani cewa, mun sami lambobin zinariya a wannan karo, babu shakka za mu sami lambobin zinare a gun taron wasannin Olympic, ba haka ba ne, dukan 'yan takararmu sun zo daga kasashen Turai. Taron wasannin motsa jiki da ake yi a Doha ba na wasannin Olympic ba ne. '

'Yan takararmu ba su iso Doha duka ba a wannan karo. Wani dalili daban da ya sanya kungiyar wasan daukan nauyi ta kasar Sin ta ta da hankali kadan shi ne domin ko da a cikin gasannin daukan nauyi na taron wasannin motsa jiki na Asiya na Doha, ba a iya cewa, kasar Sin ta fi yin fintikau sosai ba. A cikin gasar karshe ta tsakanin mata ta ajin kilo 75 ko fi da aka yi a ran 6 ga wata, 'yar wasa Mu Shuangshuang ta kasar Sin ta lashe shahararriyar 'yar wasa Jang Miran ta kasar Korea ta Kudu, wadda zakara ce ta taron wasannin Olympic, Mu Shuangshuang ta kuma karya matsayin bajimta na duniya na snatch. Ko da yake haka ne, babban malami mai horas da wasanni na kungiyar mata ta kasar Sin Li Shunzhu ya amince da cewa, a gaskiya kuma Mu Shuangshuang ba ta fi Jang Miran karfi ba. Ya ce,'Jang Miran ta fi mu karfi, mun lashe ta ko da a zarihi ba mu fi ta karfi ba. Amma mun ci nasara daga karshe saboba hikimarmu duka, mu malamai masu horas da wasanni mun tsara madaidaittun dabaru.'

Ya kamata mu amince da cewa, ko da malamai masu horas da wasanni na kungiyar kasar Sin sun fi nuna hikima wajen tsara dabara, amma 'yan wasan kasar Sin ba su fi na sauran kasashe karfi ba a cikin wasu gasanni.

Ainihin dalilin da ya sa kungiyar kasar Sin take fuskantar matsaloli shi ne domin kasashen duniya suna kyautata karfinsu a fannin wasan daukan nauyi cikin sauri. A cikin shekarun baya da suka wuce, kasashen Asiya sun kara zuba kudi kan gasannin wasan daukan nauyi, da kuma kyautata horar da kuma shigar da malamai masu horas da wasanni daga kasashen waje. A sa'i daya kuma, kasashen duniya sun sami babban ci gaba wajen nazarin wasan daukan nauyi. Sun kuma dauki matakan musamman don lashe 'yan wasan kasar Sin a cikin gasanni 15 na wasan daukan nauyi a cikin taron wasannin Olympic, sun tattara karfinsu don lashe kasar Sin a cikin wata gasar da suka fi yin fintikau. Saboda haka, Ma Wen Guang, wani jami'in kwamitin wasan Olympic na kasar Sin ya bayyana ra'ayin da kungiyar wasan daukan nauyi ta kasar Sin ke tsayawa a kai, ya ce,'Ba mu san yadda kungiyarmu za ta nuna ba a gun taron wasannin Olympic na shekara ta 2008, ba mu iya cewa, tabbas ne za mu ci nasara a cikin gasanni na wadanne azuzuwa ba. Amma kada 'yan wasanmu su fid da rai, tilas ne mu nuna aniya ga makomarmu, duk da haka, a takaice dai, za mu fuskanci takara mai tsanani a nan gaba.'(Tasallah)