Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-12 15:58:00    
Daki mai rufi na ciyayi na Du Fu

cri

A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan daki mai rufi na ciyayi na wani fitaccen mawaki na zamanin da na kasar Sin wai shi Du Fu, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, fahimtar addinin Buddha a manyan duwatsun Emeishan da Leshan.

An gina daki mai rufi na ciyayi a bayan birinin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan na kasar Sin daga yamma. An haifi Du Fu shekara ta 712, ya rasu a shekara ta 770, ya yi suna sosai a matsayin mawaki na zamanin daular Tang na kasar Sin. A shekara ta 759, Du Fu mai shekaru 47 da haihuwa ya sake gida zuwa wannan daki inda babu kayan alatu da yawa saboda talauci da kuma rashin sa'a daga Chang'an, babban birnin gwamnatin daular Tang, wato birnin Xi'an na yanzu. A cikin dukan wakoki misalin 1400 da aka samu a yanzu, Du Fu ya rubuta wakoki fiye da 240 a cikin misalin shekaru 4 da yake zaune a nan.

Gwamnatin daular Tang ta fara lalacewa a cikin rayuwar Du. Babban juya juyin hali ta fuskar zaman al'ummar kasa ya sanya Du Fu shan wahala sosai, haka kuma ya sanya masa fahimtar zaman al'ummar kasar na lokacin sosai. Ya bayyana wahalar da fararen hula ke sha da kuma ra'ayinsa a cikin wakoki da yawa da ya rubuta. Abubuwa masu yawa da ya tanadi kan zaman al'ummar kasa a cikin wakokinsa da kuma nagartacciyar fasaharsa ta fuskar yin waka sun taimake shi wajen zama kan gaba a cikin dukan mawaka na zamanin daular Tang.

Akwai wani mutum-mutumin Du Fu a cikin wannan daki. An kuma nuna kofa kofai fiye da 150 na wakokinsa, wadanda suka hade da wasu da aka buga da kuma rubuta da hannu na zamanin da, da wadanda aka buga bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, da kuma wadanda aka buga a cikin Turanci da Faransanci da Rashanci da harshen Japan da sauran harsuna 11. Ban da wannan kuma, akwai bayanan musamman da kananan littattafai da kuma bayanan karin haske kan ransa. Dukan kayayyakin da aka ajiya a cikin daki mai rufi na ciyayi na Du Fu sun nuna cewa, Du Fu ya ba da babbar gudummawa a fannin kyautata adadi na kasar Sin da na duniya.

Yanzu an dasa bishiyoyi da furanni masu fadin kadada 20 a kewayen daki mai rufi na ciyayi na Du Fu. Furanni sun fid da fure a duk shekara, shi ya sa iska cike take da kamshinsu.(Tasallah)