Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-11 16:09:01    
Wani sabon salo na ayyukan koyar da sana'o'i a kasar Sin

cri

Yanzu wani sabon salon aikin koyar da sana'o'i ya samu yaduwa sosai a ko 'ina a kasar Sin. Dalibai suna iya samun damar yin gwajin aiki lokacin da suke karatu a makarantu ta wannan sabon salo na aikin koyarwa wanda ake kiransa "sauya lokutan aiki da na karatu". Kuma kwarewar daliban da suka gama karatunsu ta wannan salon koyarwa wajen aiki tana da kyau kwarai da gaske, shi ya sa kamfanoni suke karbar su sosai.

A cikin jihar Hunan da ke tsakiyar kasar Sin, makarantun koyar da sana'o'i na birane da gundumomi 38 suna yin amfani da wannan sabon salo na "sauya lokatan aiki da na karatu". Daliban da ke cikin wadannan makarantu sun iya zabar fannoni 14 da suke sha'awa kamar gudanar da otel otel da rarraba kayayyaki a zahiri da dai sauransu. A cikin shekaru 3 da suke makaranta, an kasa ko wace shekara kashi biyu, wato suna yin karatu a rabin shekara, daga baya kuma su shiga kamfanonin domin gwajin aiki na sauran rabin shekara, kuma suna iya samun 'yan kudade alamus. Haka kuma bayan da suka gama karatu da gwajin aiki na shekaru 3, za su iya samun takardar fasahar sana'a a kalla guda, kuma sun iya shiga kamfanonin da suka daddale yarjeniyoyi tare da makaranta don aiki.

Yang Dongliang, shugaban kwalejin koyar da sana'o'in kimiyya da fasaha na jihar Hunan ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, makarantarsa ta riga ta daddale yarjenoyoyi tare da kamfanoni 5 wajen daukar daliban da suka gama karatunsu bisa salon koyarwa na "sauya lokutan aiki da na karatu". Kuma ya ce,

"Mun tsara shirin horar da dalibai bisa bukatun kamfanoni, shi ya sa a hakika dai kafin dalibai su gama karatunsu daga makaranta, kamfanoni sun riga sun amince da daukar su aiki. Yanzu muna cikin shirin daukar dalibai kusan 2000 a shekara mai zuwa. "

Sabo da daliban da suka gama karatunsu daga makaranta ta sabon salon aikin koyarwa na "sauya lokutan aiki da na karatu" suna iya dacewa da yanayin guraban aiki sosai, shi ya sa kamfanoni ke yi musu maraba sosai. Wani kamfanin sayar da abinci mai suna" kahohin shanun zinariya " da ke birnin Changsha, hedkwatar jihar Hunan ya daddale yarjejeniyar daukar dalibai tare da kwalejin koyar da sana'o'in kimiyya da fasaha na jihar Hunan. Madam CaiYan, manajar kamfanin ta bayyana cewa, bisa matsayinsa na wani kamfani, ya amince da wannan salon koyarwa, kuma yana son sa hannu a cikin ayyukan horar da dalibai. Kuma ta ce,

"za mu aika da malamai a fannin 'yan kwadago zuwa makaranta domin horar da dalibai, ta haka wadannan dalibai za su iya dacewa da yanayin ayyuka na kamfaninmu cikin sauri sosai."

Haka kuma wakilinmu ya gano cewa, ta yin amfani da salon koyarwa na "sauya lokutan aiki da na karatu", kafin su gama karatunsu daga makarantun koyar da sana'o'i, dalibai sun riga sun samu fasahohin gudanar da ayyukansu. Sabo da haka yawan daliban bai iya biyan bukatun yawan ma'aikatan da kamfanonin ke nema ba. Yan Hui, wani dalibi na makarantar koyar da sana'o'i na gundunar Fengkai da ke jihar Guangdong ya gaya wa wakilinmu cewa, daliban da suka gama karatunsu daga makarantar sun fi saukin samun aikin yi idan an kwatanta su da wadanda suka gama karatunsu daga jami'o'i. Haka kuma ya ce,

"yanzu da kyar daliban da suka gama karatunsu daga jami'o'i suke iya samun aikin yi, amma muna karatu muna gwajin aiki, shi ya sa neman aikin ya fi sauki gare mu."

Bisa labarin da muka samu, an ce, kasashe masu ci gaba sun riga sun yi amfani da wannan salon koyarwa na "sauya lokutan aiki da na karatu" har shekaru fiye da dari. A kasar Jamus, a ko wane mako, dalibai su kan yi aiki na kwanaki uku, da yin karatu na kwanaki biyu, kuma daliban da yawansu ya kai kashi 60 cikin dari suna shiga irin wannan salo na koyar da sana'o'i. A kasar Amurka, daliban da suke makaranta suna iya samun damar samun aikin yi a lokacin hutu a yanayin zafi. Kwararru sun bayyana cewa, yin amfani da salon koyarwa na "sauya lokutan aiki da na karatu" yana iya daga matsayin dalibai wajen aiki, da rage yawan kudin da makarantu su kan zuba wajen kayayyakin karatu da horar da malamai, da kuma sassauta nauyin biyan kudin makarantar dalibai daga iyaye, ta yadda za a iya taimaka wa daliban da suke yaki da talauci wajen karatu da samun aikin yi.

Amma a halin yanzu da ake ciki a kasar Sin, salon koyarwa na "sauya lokutan aiki da na karatu" yana fuskantar matsaloli da yawa. Alal misali, ana kasancewa da ra'ayin dora muhimmanci kan hasahe da kuma rashin mai da hankali kan horar da fasahohi a kasar Sin. Sabo da haka makarantu iri daban daban na kasar Sin su kan mai da hankulansu kan horar da hasashe lokacin da suke tsara darussa, ba su samar da dama da yawa ga dalibai wajen gwajin aiki ba. Game da wannan, Yu Guangzu, kwararre na cibiyar nazari kan ilmin koyar da sana'o'i na ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ya bayyana cewa, ya kamata makaratu iri daban daban na koyar da sana'o'I na kasar Sin su koyi salon koyarwa na "sauya lokutan aiki da na karatu" wajen horar da kwararrun da ke da ilmi a fannin fasaha.(Kande Gao)