Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-11 16:02:36    
Takaitaccen bayani game da kabilar Zhuang

cri

Kabilar Zhuang karamar kabila ce wadda ke da mutane mafi yawa daga cikin dukkan kananan kabilun kasar Sin. Yawancinsu suna da zama jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gabashin kanta da shiyyar Wenshan ta kabilun Zhuang da Miao ta lardin Yunnan. Amma wasu daga cikin suna da zama a lardunan Guangdong da Hunan da Guizhou da Sichuan da dai sauran wuraren kasar Sin.

Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Zhuang ya kai fiye da miliyan 16 da dubu dari 1. Suna magana da yaren Zhuang. A shekarar 1955, a karkashin taimakawar gwamnatin tsakiyar kasar Sin, an kirkiro bakakken yaren Zhuang bisa bakakken Latin. Daga baya, a shekarar 1982, an yi kwaskwarima kan bakakken yaren Zhuang da yanzu ake yin amfani da su sosai.

Kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, al'ummar Zhuang tana cikin zaman al'ummar mulkin kama karya. Mutanen kabilar sun yi zama a lardin Guangxi, sai a ran 15 ga watan Maris na shekarar 1958 aka kafa jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kanta. A cikin shekaru kusan 50 da suka wuce, tattalin arzikin jihar ya samu cigaba sosai. Yanzu jihar tana yin ciniki da yawancin kasashe da yankunan duniya.

Mutanen kabilar Zhuang sun fi iya waka da rawa. Su kan shirya bukukuwan rera wakoki da taka rawa. A cikin bukukuwansu iri iri, bikin ran 3 ga watan Maris na kalandar gargajiya ta kasar Sin ya fi muhimmanci a gare kabilar Zhuang. A gun wannan biki, mutane dubbai sun taru sun shiga gasar rera wakoki iri iri, ciki har da wakokin roko da na ban kwana da na soyayya da dai sauransu. A waje daya kuma, lokacin da ake shirya bikin, samari da 'yan mata na kabilar Zhuang su kan jefa kwallon zane a tsakaninsu domin neman masoyi ko budurwa.

Bisa al'adar kabilar Zhuang, a da iyaye ne suka nemi wa yaransu aure. Amma kafin a shirya bikin aure, yara suna da 'yancin neman soyayya. A sa'i daya kuma, a da, masu ariki namiji su kan auri mata ba daya kadai ba, amma sauran maza sun saba da al'adar "miji daya, mata daya". Bugu da kari kuma, bisa al'adar kabilar Zhuang, bayan ango da amariya sun yi bikin aure, ba dole ba ne amariya ta yi zama a gidan ango kafin ta dauki ciki. Amma, yanzu matasan kabilar Zhuang suna neman soyayya da aure cikin 'yanci.

Yawancin mutane suna bin addinan gargajiya nasu, kamar suna girmama al'ajabin tsauni da al'ajabin ruwa da na kasa da dai sauransu. Wasu mutanen kabilar suna bin addinan Buddha da Daoist da Kirista.(Sanusi Chen)