Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-08 17:51:24    
Malam He Shanxi, dan kasuwa na Taiwan ya kafa masana'antunsa a birnin Xi'an na kasar Sin

cri

A shekarar 1958, an haifi Malam He Shanxi ne a birnin Taipei, ya fara ganam ma idonsa babban yankin kasar Sin ne a shekarar 1988. A wancan lokacin shi ne karo na farko da hukumar Taiwan ta amincewa jama'ar Taiwan su fara zuwa babban yankin kasar don gaida danginsu. Bisa matsayinsa na dan jarida. Malam He Shanxi ya zo birnin Beijing tare da tawagar mutanen Taiwan masu gaida danginsu don neman labaru. Daga nan dai ya kan zo babban yankin kasar Sin a ko wace shekara. Babban ci gaba da aka samu wajen bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma a babban yankin kasar Sin, ya jawo hankalinsa kwarai da gaske.

Kafin Malam He Shanxi ya fara zuba jarinsa a birnin Xi'an, ya taba yin rangadin aiki a manyan biranen Beijing da Shanghai da sauransu tare da abokan aikinsa. Daga baya, ya gano cewa, bai kware wajen zuba jari a wadannan manyan birane ba, sabo da tsadar filaye da 'yan kwadago. A zahiri ne, bai tsaya a kan matsayi mai rinjaye na zuba jari ba, don haka ya yanke shawara a kan zuba jarinsa a birnin Xi'an, inda farahin filaye da 'yan kwadago ke da rahusa, idan an kwatanta shi da na manyan biranen nan. Ya bayyana cewa, "da ma a ganin mutanen Taiwan, birnin Xi'an a baya-baya yake, babu wani abu da muke tunawa da shi, sai tudu mai launin rawaya. Amma da na sa kafa a cikin birnin Xi'an, sai na fada wa kaina, birnin Xi'an ba wani birni ne da ba a zo a gani ba. Daga bisani kuma, na gano cewa, a hakika dai, akwai 'yan kimiyya da fasaha masu dimbin yawa a birnin nan."

Malam He Shanxi yana ganin cewa, birnin Xi'an yana kan matsayi mai rinjaye na binciken kimiyya da fasaha, 'yan kasuwa na Taiwan kuma suna kwarewa wajen gudanar da harkokin masana'antu da na kasuwanni. Idan bangarorin nan biyu sun hada kansu, to, tabbas ne, za su sami sakamako mai kyau wajen gudanar da harkokin kasuwanci. Sabo da haka a shekarar 2003, Malam He Shanxi ya kafa wani kamfanin binciken kayayyaki masu tsimin makamashi na zamani a birnin Xi'an. A cikin shekarun nan uku da suka, yanzu kamfanin nan ya riga ya fitar da kayayyakinsa zuwa kasashe da yankuna sama da 10. Ya ce, yanzu, kamfaninsa yana binciken wani irin gilas mai tsimin makamashi da ake kira "Nanometer" a turance. Ya kara da cewa, "gilas iri na "Nanometer" wani irin muhimmin gilas ne da ma'aikatar gine-gine ta kasar Sin za ta bukata wajen yin tagogin gine-gine a nan gaba. Yanzu, yawancin gilas da ake amfani da su wajen yin tagogin gine-gine ba su iya tsimin makamashi ba, don haka muna fatan irin gilas na "Nanometer" da muke bincikensa zai magance hasken rana, ko hana dumi fita daga dakuna zuwa waje."

A lokacin da Malam He Shanxi ya ke son kafa wani yankin masana'antu na zamani, sai ya sami goyon baya daga wajen gwamnatin birnin Xi'an. Yanzu kuma za a kaddamar da wannan yanki a watan Disamba mai zuwa. Malam Chen Baogen, magajin gari na Xi'an yana ganin cewa, birninsa da Taiwan za su raya masana'antunsu bisa matsayinsu mai rinjaye, don cin nasara tare, a yankin masana'antu na zamani na birnin Xi'an. Ya kara da cewa, "na daya, makamashi da kwararru suna yawa a birnin Xi'an. Na biyu, yanzu ana bunkasa tattalin arzikin birnin cikin sauri, don haka ana bukatar kudin jari mai dimbin yawa da ake zubawa, 'yan kasuwa na Taiwan suna da kudin jari mai yawa, suna neman wurare da suke zuba musu jari. Na uku, Taiwan ya sami ci gaba wajen yin manhaja, sa'an nan kuma aikin manhaja aiki ne da ake bunkasuwa a birnin Xi'an."

Ban da Malam He Shanxi, akwai 'yan kasuwa na Taiwan da yawa wadanda ke ganin cewa, za su sami babbar zama wajen raya masana'ntunsu a birnin Xi'an. (Halilu)