Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-08 17:49:04    
Mr. Li Fuyu ya ba da karin haske ga wasan tseren keke wato bicycle kan hanyar mota a kasar Sin

cri

Ko da yake kasar Sin tana da kekunan hawa mafi yawa a duniya, amma Sinawa sun kasa samun maki mai kyau a fannin wasan tseren kekuna kan hanyar mota. Yanzu, wani dan wasan tseren keke ya soma yin kokari matuka don cimma babban burin 'yan wasan tseren kekuna kan hanyoyin mota na samun maki mai kyau a taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Sunansa Li Fuyu, wanda takwarorin sana'arsa a duniya suka rigaya suka amince da karfin da yake da shi. Daya daga cikin mashahuran kungiyoyin wasan tseren keke na duniya wato kungiyar wasan keke da ake kira " Discovery Channel Team" ta kasar Amurka ta rigaya ta gayyaci dan wasa mai suna Li Fuyu don ya yi aiki a cikin kungiyar din. A gun gasa ta farko ta tseren keken hawa kan hanyar mota dake kewayen tsibirin Hainan na kasar Sin a kwanakin baya ba da jimawa ba, dan wasa Li Fuyu ya yi fintinkau a gun gasar, inda ya jawo hankulan mutane.

Dan wasa mai suna Li Fuyu yana da shekaru 28 da haihuwa, shi dogo ne kuma siriri ne kuma yana da dogon gashi kai, wanda shi ke kama da wani mawaki saurari na " Rock'n roll". Da zarar ya hau kan keken bicycle da darajarsa ta kai kudin dola 20,000 sai ya gwada fuskar jagoran wasan tseren keke kan hanyoyin mota na kasar Sin.

A gun gasa ta farko ta tseren keke kan hanyar mota dake kewayen tsibirin Hainan da aka yi a kwanakin baya ba da dadewa ba, ko da yake dan wasa Li Fuyu ya sha kaye daga hannun abokin karawarsa a karshe, amma lallai ya nuna gwaninta a gun gasar. Da ya tabo magana kan dalilin da ya sa ya sha kaye a gun gasar, sai ya fadi cewa, ya sha kaye ne ba wai domin karfin da yake da shi bai isa cin nasara ba, ai domin abokansa na kungiyar suka kasa samar masa da babban karfi lokacin da yake bukatar samunsa. Game da wannan dai, Mr.Zhang Hongquan, alkalin wasa na wannan gasa shi ma ya yi hasashen cewa, mutum shi kadai ba zai iya lallasa kungiyoyin wasa ba ko da yana da babban karfi. Dan wasa mai suna Sergey Kolesnikov na kasar Rasha,wanda ya zama lambawan a gun gasar tseren keke kan hanyar mota dake kewayen tsibirin Hainan ya fada wa wakilinmu, cewa ba zai iya zama zakara a gun gasar ba muddin bai samu taimako daga abokansa na kungiyar da ake kira " Ominbike Dynamo Moscow" ba.

Dan wasa Li Fuyu shi ma ya gane cewa, da kyar ya daga matsayinsa a fannin wasa kuma mai yiwuwa ne zai yi baya-baya idan ya dade yana cikin wata kungiyar wasa da ba ta da karfi sosai. Amma ya yi sa'a saboda hadaddiyar kungiyar wasan keken bicycle ta kasar Sin ta cimma burinsa na yin ciki a kungiyar wasan ta kasashen ketare. Babban sakataren hadaddiyar kungiyar wasan tseren keke ta kasar Sin Mr. Jiang Guofeng ya bayyana, cewa dan wasa Li Fuyu ya shiga gagaruman gasanni sau tari a cikin shekaru biyu da suka shige. Don haka, ya yi ta kara samun fasahohi a fannin wasa. A 'yan kwanakin baya dai, kungiyar da ake kira " Discovery Channel Team" ta Amurka tana mai sha'awar gayyace shi don ya yi aiki cikin kungiyar. Mu kam har kullum muna himmantuwa wajen goyon bayan 'yan wasa don su yi aiki a cikin kungiyoyin kasashen ketare.

A zahiri dai, tuni a shekarar 2005 ne dan wasa Li Fuyu ya shiga cikin kungiya ta farko ta wasan tseren keke na sana'a ta kasar Sin wato kungiyar Marco Polo. A cikin lokaci na tsawon shekaru biyu da yake aiki cikin wannan kungiyar wasan, dan wasa Li Fuyu ya samu dama sau da yawa ya kuma dace da sabon yanayin da yake ciki a fannin kula da harkokin wasa ta hanyar sana'a, da horaswa da kuma salon da akan bi wajen gudanar da gasa.

Yansu, dan wasa Li Fuyu ya samu sabuwar kyakkyawar damar shiga cikin kungiyar da ake kira " Discovery Channel Team" ta Amurka wadda shahararren dan wasa mai suna Lance Armstrong wanda har sau bakwai ne ya zama zakara a gagarumar gasar tseren keke kan hanyar mota dake kewayen kasar Faransa ya taba yin aiki a cikinta. Lallai dan wasa Li Fuyu yana da kyakkyawan buri bayan an shigar da shi cikin shahararriyar kungiyar wasan tseren keke ta duniya. Ya ce, kila tun farko bai dece da sabon muhalli ba, amma ba damuwa zai iya nuna gwaninta a gun gasa idan ya dace da yanayin kungiyar sana'a dake da matsayin koli a fannin wasa. ( Sani Wang )