Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 20:38:37    
Bayan haka, wani kulab na masu sauraron gidan rediyon kasar Sin wato JEKADAFARI YOUTH RADIO LISTENERS ASSOCIATION ya rubuta wata wasika gare mu

cri
Bayan haka, wani kulab na masu sauraron gidan rediyon kasar Sin wato JEKADAFARI YOUTH RADIO LISTENERS ASSOCIATION ya rubuta wata wasika gare mu, shugaban kulab MUSA ADAM ABUBAKAR da sakatarensa SA'AD IBRAHIM GOMBE da kuma mataimakin shugaban kulab din MOH'D YERO (TEA-MAKER) sun taya murna musamman ga cikon shekaru 65 na CRI, sun ce haka,

'Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan kuna lafiya kamar yarda muke a nan Gomben Nigeria lafiya. Allah yasa haka Amin.

Mu kungiyar JEYRALA muna taya ku murnar cika shekaru sittin da biyar (65) da kafa gidan radio CRI,wanda a tattare da wannan ne muka yi tsokaci da wadannan kalmomi:-

**Duk gidan radio mai gaskiya, babu shakka zai kai gaci, musamman CRI.

**Duk gidan radion da bayb nuna kyashi, to babu shakka a kullum zai ci gaba, kamar CRI.

**Duk gidan radio mai kiyaye hakkin masu sauraronsa, babu shakka shine a sama,

kamar yadda CRI take.

****Duk gidan radion dake karantar da darasin zaman duniya, shi kowa yake bida (BUKATA), irin su CRI.

****Duk gidan radio mai son kowace kabila ko yare ta amfana da sanin me ke faruwa a fadin duniya, itace akan gaba, musamman CRI mai watsa shirye-shiryenta sama da yare 48.

****Duk mutum mai son gaskiya, yasan CRI itace akan gaba wajen ingantattun shirye-shirye.

****Duk mutum mai son gaskiya, yasan CRI itace gidan radion dake da kayan kayan zamani da kuma ginin zamani.

Da wannan mu JEYRALA muke tuna muku cewa:-

1.Kuci gaba da watsa shirye-shiryen ku kamar yadda kuka saba, amma kada ku manta da shirinku na safe na sashin hausa don muhimmancinsa.

2.kada ku manta da martaba masu sauraron ku komin dadewarsu

Daga karshe ga wata rubutacciyar waka da kungiyar JEYRALA ta shirya don murnan cika shekaru sittin da biyar(65) da kafa CRI.

=To Bismillahi Sarki Mai duka,

Sarkin duniya kuma Sarkin gaskiya.

=Yau ga CRI tana magana duka,

Kowa ya saurare ta don jin gaskiya.

=Babu karkata agaresu balle rarraka,

Sai tsantsar gaskiya babu masgaya.

=Shekara sittin da biyar kuna ta daka,

Lallai CRI kuna kofar gaskiya.

=Internet da F.M hanyar kuce duka,

Ballantana radiyon ku dakin gaskiya.

=Ya ku Jama'a kuzo ku jiya duka,

CRI shekara sittin da biyar a duniya.

=Sashin Hausa shima baya rarraka,

Balle mu masu sauraron sa musha kunya.

=Kima shekara arba'in da uku kun daka,

Babu lankwasa acikin sa balle tirjiya.

='Yan uwana idan kuna bidar darasi duka,

Sai ku saurari CRI tashar duniya.

=Mu kungiya JEYRALA mun sani duka,

Batun gidan radion darasi sai CRI gaskiya.

=Dukkan mai rabo yayi tsayuwar daka,

Domin yaga ci gaban CRI na gaskiya.

=Har abada JEYRALA na yaba muku,

Tun da kunce maganarku itace gaskiya.

=Balarabe,Ramatu,Dogon yaronku ko,

Lubabatu,Bello,Halima duk suna halin lafiya.

=Ga su Ado, Amina Jamila 'Yan daka,

Ballantana Halima,Lawan Mamuda duk daya.

=Kar ka manta da Alin,Usmanu,Umarun mu duka,

Domin CRI ta shirya masu gaskiya.

=Mu JEYRALA muna adu'a agareku duka,

Akan aminci,lafiya, ci gaban gaskiya.'