Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 20:33:31    
Bari mu raya wani kafar watsa labaru ta zamani tare

cri

Jiya wato ran 3 ga wata, an yi bikin taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin da yake kasancewa tare da ku a kowane lokaci. Lokacin da aka kafa shi a wani kogon dutse a garin Yan'an da ke arewa maso yammacin kasar Sin yau da shekaru 65 da suka wuce, ya watsa labaru ga masu sauraro da harshe daya, wato harshen Japan kawai. Amma, yanzu ba ma kawai yana watsa labarun kasar Sin da na duniya da harsuna 43 ba, har ma yana tsara da watsa labaru ta rediyo da na talibijin da shafin internet da jarida, wato ya riga ya zama wata kafar watsa labaru ta zamani. Yanzu, a cikin shirinmu, za mu gabatar da shugaba Wang Gennian na gidan rediyon kasar Sin a cikin dakinmu na daukar murya. Mr. Wang zai bayyana muku yadda ake raya wannan kafar watsa labaru ta zamani. A waje daya kuma, Mr. Wang, wani tsohon manemin labaru ne na gidan rediyonmu, amma yanzu shugaban rediyon, zai raba abubuwan farin ciki da ku game da tarihin gidan rediyon kasar Sin. Mr. Wang ya ce, "Lokacin da muke murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin, a madadin dukkan ma'aikatan gidan rediyon da kuma kaina, ina gaishe ku, dukkan masu sauraro da masu karatu. A nan, ina nuna muku godiya domin kun dade kuna kulawa da gidan rediyonmu da saurarar shirye-shiryenmu da kuma nuna mana goyon baya. Ina fatan ku da iyalanku duka kuna nan lafiya."

A karshen shekara ta 2004 ne Mr. Wang ya zama shugaban gidan rediyon kasar Sin. Bayan hawarsa kan mukaminsa na yanzu da kwanaki 25 kawai, ya shiga dakin daukar murya ya gai da masu sauraronmu domin sabuwar shekarar 2005. Lokacin da yake tabo dangantakar da ke tsakanin gidan rediyon kasar Sin da masu sauraronmu, ya taba fadin wata magana. To, yanzu, ga wannan maganar da Mr. Wang ya taba fada. "Bukatun da masu sauraronmu ke nema bukatu ne da muke nema. Darajanta masu sauraro da kiyaye su da kuma tsara shirye-shiryen da ke dacewa da su, wadannan abubuwa ne da suke sa kaimi wajen raya shirye-shiryenmu."

Jama'a masu karatu, ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin da yawa suna ganin cewa, maganar da Mr. Wang ya fada tana jawo hankulan mutane sosai. Gidan rediyon kasar Sin yana samun wasiku fiye da miliyan 2 a kowace shekara. Mene ne ganin Wang Gennian game da masu sauraronmu? Mr. Wang ya ce, "Dalilin da ya sa na fadi cewa 'Bukatun da masu sauraro suke nema bukatu ne da muke nema' shi ne masu sauraro suna da muhimmanci kwarai ga wani gidan rediyo. Dole ne mu sani cewa, bukatun da masu sauraro ke nema ma'auni ne ga kasancewar wata kafar watsa labaru. Samun wasiku da amincewa daga masu sauraro, su kyaututuka ne daga masu sauraronmu, kuma suna bayyana yadda muke yin aikinmu kai tsaye. Tun da haka, ma'anar wata wasika daga mai sauraro tana nan kamar yadda muke tsara wani shiri mai kyau.

A waje daya kuma, na ce, dalilin da ya sa na ce 'darajanta masu sauraro da kiyaye su da kuma tsara shirye-shiryen da ke dacewa da su' shi ne, dole ne mu kara sanin masu sauraronmu da kulawa da abubuwan da suke bukata. Gidan rediyon kasar Sin yana da miliyoyin masu sauraro a duk fadin duniya. Sun dade suna saurarar shirye-shiryenmu da karanta labarunmu a shafin internet namu domin yunkurin sanin kasar Sin da shirya ayyukan sada zumunci a tsakaninsu da kasar Sin. Sabo da haka, na ce, idan masu sauraronmu ba su bukace mu ba, shi ke nan, gidan rediyon kasar Sin ba zai samu cigaba ko kadan ba."

Jama'a masu karatu, gidan rediyon kasar Sin yana kokarin tsara shirye-shiryen da ke dacewa da masu sauraronsa. Shekara ta 2006 shekara ce ta musamman ga masu sauraro.

Jama'a masu karatu, kun sani, a da, gidan rediyon kasar Sin yana watsa shirye-shirye ta gajerun zango kawai, ku ma kun iya samun shirye-shiryenmu ta gajerun zango kawai. Amma a shekarar da muke ciki, bi da bi ne gidan rediyon kasar Sin ya kafa tasoshin FM a birnin Nairobi na kasar Kenya da birnin Vientian na kasar Laos. Masu sauraron da ke zama a wadannan birane biyu yanzu suna sauraran shirye-shiryenmu ta zango na FM domin sanin kasar Sin da duk duniya cikin sauki.

Jama'a masu karatu, ba ma kawai yanzu muna watsa shirye-shirye ta gidan rediyo ba, har ma muna watsa shirye-shirye da labarun duniya kan shafin internet namu mai suna "CRI Online". Masu karatun shafin internet namu suna da sha'war shafinmu kwarai da gaske. Musamman, yawan mutanen da suke sauraran labaru daga rediyon da ke shafin Internet yana matsayin farko a duk duniya. A ganin Wang Gennian, shugaban gidan rediyon kasar Sin, gidan rediyon kasar Sin yana zama wata kafar watsa labaru ta zamani.

"A ganina, sha'anin rediyo yana da wata makoma mai kyau a nan gaba. Rediyo yana da kyawawan halayen musamman, wato farashin rediyo yana da arha, ana amfani da shi cikin sauki, kuma za a iya tafiya da shi a ko'ina. A waje daya kuma, za a iya watsa labaru masu dumi-dumi cikin sauri. Sa'an nan kuma, yanzu yawancin mutanen duniya suna da karfin sayen akwatunan rediyo. A cikin dukkan kafofin watsa labaru irin na lantarki, rediyo ya fi jawo hankulan mutane. Ko da yake fasahohin watsa labaru suna ta samun cigaba, amma ko shakka babu, rediyo yana da wadannan kyawawan halayen da ake bukata kuma ba za a iya maye su ba wajen watsa labaru. Mun sani, rediyo yana kuma dacewa da fasahohin zamani. Yau, lokacin da ake bunkasa sabbin fasahohin zamani na watsa labaru, ciki har da shafin internet da GSM, idan mun hada irin wadannan fasahohin zamani da rediyo, tabbas ne gidan rediyo zai kuma kara samun cigaba kamar yadda ake fata yayin da ake samun bunkasuwar zaman al'umma da fasaha."

Mr. Wang ya kara da cewa, raya tsarin watsa labaru ta fasahohin zamanin yanzu muhimmin aiki ne da yake daya daga cikin dukkan ayyukan da ke shafar film da na talibijin da makamatansu. Yanzu, muhimmin nauyin da ke wuyanmu shi ne, kafa wani tsarin watsa labaru ta fasahohin zamani. Muna fatan ba ma kawai gidan rediyon kasar Sin zai iya watsa labaru ta hanyar gajeren zango da na FM ba, har ma zai iya watsa labaru ta fasahohin zamani, kamar su shafin internet da hanyoyin sadarwa daban-daban. Sakamakon haka, muna fatan gidan rediyon kasar Sin zai zama wata sabuwar kafar watsa labaru da ke da suna da kuma karfin yin takara sosai a duniya a cikin 'yan shekaru masu zuwa."

Jama'a masu karatu, wayar rediyo da ba za mu gan ta ba tana hada mu da ku, kuna zama a wuraren da ke nesa da mu sosai. Muna tare kamar muna zama a cikin wani babban gida. Yanzu, dukkanmu ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin muna jin sauye-sauyen da ke faruwa a rediyon. Mu kan fadi cewa, gidan rediyon kasar Sin wuri ne da ke cimma mafarkinmu. Masu sauraronmu da ke zama a ketare sun kuma samar wa gidan rediyon kasar Sin kyaututtuka kamar su muhimman litattafai da hotuna nasu. Game da wannan babban gidan da ke cike da iyalai, Mr. Wang ya ce, "Ga masu sauraronmu, za mu ci gaba da watsa muryar kasar Sin ga duk duniya ta wayarmu, kuma za mu yi kokarin sada zumunci a tsakaninmu da masu sauraro domin kara saninsu kan kasar Sin. Sabo da haka, loakcin da muke tsara shirye-shiryenmu, dole ne mu watsa shirye-shiryen da ke dacewa da halin da ake ciki a kasar Sin yanzu da biyan bukatun da masu sauraronmu na ketare suke nema da kuma dacewa da al'adarsu ta sauraran rediyo da suke sabawa da su. Muna fatan za mu iya tsara shirye-shirye domin jin dadin masu sauraro. A kan hanyar watsa shirye-shirye, za mu yi kokarin kusantarmu da masu sauraronmu." (Sanusi Chen)