Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 20:31:43    
Bayani kan tarihin Rediyo Kasar Sin don murnar cikon shekaru 65 da kafa shi

cri

Ranar 3 ga watan Disamba rana ce ta cikon shekaru 65 da kafa gidan rediyo kasar Sin wato CRI. Yau da shekaru 65 da suka wuce, wayar gidan rediyonmu maras karfi ta tashi daga Yan'an, wani karamin gari da ke arewa maso yammacin kasar Sin, daga nan dai rediyonmu ya soma watsa shirye-shirye cikin harsuna da yawansu kullum ke kara karuwa sannu a hankali, muryar rediyonmu ya kara yaduwa zuwa wurare daban daban, sa'an nan kuma aminai da suka kulla abuta da rediyonmu kullum sai kara karuwa suke yi. Ya zuwa yanzu, aikin watsa labaru ta rediyo yana daya daga cikin hanyoyi da yake bi don bautawa masu sauraronmu. Duk wadannan an same su ne cikin dogara da ci gaban kimiyya da fasaha kuma domin biyan bukatu da ake yi wajen watsa labaru da yin ma'amala, abin da ya fi muhimmanci kuma shi ne domin kara yin ma'amala da masu sauraronmu da kyau da bauta muku.

A farkon shekarun 1940, kasar Sin ta gamu da hare-hare masu tsanani da makiyan kasashen waje suka kawo mata. A cikin kazamin yaki, rundunar sojojin da ke karkashin shugabancin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin sun zama wata runduna mai mihimmanci ga yakin kin Fascism na duniya. Don baki 'yan kasashen ketare su kara fahimtar ra'ayoyin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kan kin mahara Japanawa, Jam'iyyar ta kafa wani gidan rediyo da ke watsa shirye-shirye cikin harsunan waje, don bayyana halin da ake ciki a gida da waje a wancan lokaci, da yin kira ga bangarori daban daban na gida da waje da su kubutar da al'ummar Sin daga mawuyacin hali, da mayar da kwanciyar hankali a duniya.

A ran 2 ga watan Disamba na shekarar 1941, gidan rediyonmu ya fara watsa shirye-shirye cikin Japananci ga sojoji mahara na kasar Japan da ke girke a kasar Sin, yana gaya musu ainihin yaki da hakikanan abubuwansa. Marigayiya madam Hara Kiyoshi, 'yar kasar Japan wadda ke adawa da yakin kai hari da kasar Japan ta tayar a kan kasar Sin ta zama ta farko wajen karanta labaru cikin Japananci. A wancan lokaci, dakin daukar murya na rediyonmu wani daki ne da ba na a zo a gani ba a garin Yan'an.

Gidan rediyo ya kan watsa labaru cikin mintoci 15 a ko wace rana. Tsoho Lu Rufu wanda ya shafe shakaru da yawa yana aiki a sashen Japananci na rediyo kasar Sin ya bayyana cewa, muryarta da ke fitowa daga Yan'an wani babban makami ne ga wargaza rundunar sojojin Japan a wancan lokaci. Ya ce, "da muryarta ta gaya wa Japanawa ainihin yakin da gaskiya, ta shawo kansu sosai, ta kawo tasiri sosai ga Jajanawa da yawa. Daga bisani, kwararru Japanawa da yawa da suka taba aiki a redioyonmu dukansu sojojin Japan ne a wancan lokaci. Wasunsu sun ba da kai, wasunsu sun gudu zuwa wajenmu. Da ma Michiyuki Ogi, malamin koyarwarta shi ma wani sojan kasar Japan ne a wancan lokaci. Kuma ya dade yana aiki a sashen Japananci na rediyo kasar Sin. "

Rediyonmu ya kafa sashen Turanci ne bayan da aka ciwo nasarar yakin kin harin Japan. A wannan lokaci, gidan rediyonmu ya fara amfani da manyan injuna wajen watsa labaru zuwa Asiya ta kudu da ta kudu maso gabas da Turai da arewancin nahiyar Amurka da sauransun wurare na duniya.

A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, gidan rediyo kasar Sin ya watsa labaru zuwa wurare daban daban na duniya kai tsaye cewa, Jamhuriyar Jama'ar Sin ta kafu.

A sakamakon ci gaba da kasar Sin ta samu wajen gudanar da harkokin waje, gidan rediyonmu ma ya yi ta samun bunkasuwa. Ya soma watsa labaru cikin harsuna da yawansu ya yi ta karuwa, yana watsa shirye-shiryensa zuwa wurare masu nisa na duniya, yana bayyana wa duniya sauye-sauyen siyasa da tattalin arziki da zamantakewar al'umma da sauransu.

Zuwa shekarar 1965, gidan rediyo kasar Sin ya kasance cikin sahon gaba a duniya wajen yawan harsuna da tsawon lokacin shirye-shirye. A tsakiyar shekaun 1970, rediyo kasar Sin ya soma watsa shirye-shirye cikin harsuna 43, ya zama wata babbar gada da ke hada kasar Sin da kasashen waje.

Ya zuwa karshen shekarun 1970, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bude wa kasashen waje kofa, nan take rediyo kasar Sin ma ya kama hanyar bude wa kasashen waje kofa da samun bunkasuwa. Wata mujallar kasar Jamus da ake kira "Radio-kurier" ta buga bayani cewa, shirye-shirye da rediyo kasar Sin ke watsawa cikin Jamusanci tamkar iska ce mai kanshi da ke buguwa daga kasar Sin mai nisa sosai. Kuma ta ce, "rediyo kasar Sin rediyo ne da ake kaunarsa ainun."

Don kara watsa labaru kan Sin da duniya daga duk fannoni kuma cikin gaskiya, tun daga shekarun 1980, rediyo kasar Sin ya soma kafa ofisoshin wakilansa a kasashe daban daban. Malam Wang Zuozhou, kwararen edita na rediyonmu yana daya daga cikin wakilai da rediyon ya aika da su zuwa ofisoshinsa a kasashen waje, ya bayyana cewa, "ya kamata, a ce, tun daga ranar farko da rediyonmu ya kafa ofishin wakilansa a kasar waje, sai wakilanmu suka yi kokari sosai wajen neman labaru a wurare da al'amura ke faruwa. Mun kawar da wahalhalu, mun shiga wurare da labaru ke faruwa, ta yadda rediyonmu ke watsa labarun cikin lokaci. Alal misali, na shiga aikin neman labaru kan yarjejeniyar zaman lafifyar Afghanistan da aka rattaba hannu a kai a birnin Geneva, bayan sama da mintoci 20 da na aika da labarun, sai rediyonmu ya watsa su".

A da, yawancin aminanmu sun iya saurarar rediyonmu ne ta hanyar gajeren zango kawai, amma a ran 27 ga watan Febrairu na shekarar nan, rediyo kasar Sin ya kaddamar da tasharsa ta FM a hukunce a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya, tashar nan tashar FM ce ta farko da rediyonmu ya kafa a kasashen waje.

Ranar nan ta cancanci zama ranar da za a tuna da ita a cikin tarihin kasar Sin kan watsa wa kasashen waje shirye-shirye. Bayan haka a ran 19 ga watan jiya, gidan rediyon kasar Sin ta kaddamar da tasharta ta FM a hukunce a birnin Vientiane, hedkwatar kasar Laos. Tashar nan ta zama tashar FM ta biyu da rediyonmu ya kafa a kasashen waje.

Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin wanda ke yin ziyara a kasar Laos a wannan rana tare da takwaransa na kasar Laos Mr Choummaly Sayasone sun halarci bikin kaddamar da tashar. Shugaba Hu ya bayar da jawabi ta wannan tashar FM, inda ya isar da dubun gaisuwarsa zuwa ga jama'ar Laos, kuma ya ce, "kasashen Sin da Laos kyawawan makwabta ne da ke iyaka da juna. Kuma tun fil azal ya kasance da amincin gargajiya mai zurfi a tsakanin jama'ar kasashen biyu. Kaddamar da tashar FM ta rediyo kasar Sin a birnin Vientiane zai kafa wata sabuwar gada da ke kara jawo fahimtar juna da dankon aminci a tsakanin jama'ar kasashen biyu, zai ba da taimako wajen cudanyar jama'ar kasashen biyu, da dankon amincinsu daga zuriya zuwa zuriya yadda ya kamata." Bayan haka, a cikin harshen Laso, shugaba Hu Jintao ya bayyana cewa, " Zumuncin da ke tsakanin kasashen Sin da Laos zai ci gaba a kulli yaumin!"

Da Malam Wang Gengnian, shugaban gidan rediyo kasar Sin ya tabo magana a kan makomar rediyon, sai ya bayyana cewa, "manufar rediyonmu na bunkasuwa ita ce, mu yi aikin watsa labaru ta rediyo da telebijin da Internet da makamatansu wajen biyan bukatu da masu sauraronmu na kasashen waje ke yi wajen samun labarun kasar Sin. Haka nan kuma bisa matsayinsa na wata gadar da ke tsakanin Sin da duniya, za mu taimaka wajen fahimtar kasar Sin sosai, kuma za mu ba da taimakonmu ga jama'ar Sin don kara fahimtar duniya da kyau. " (Halilu)