Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 17:45:30    
Sakonnin taya murna daga masu sauraro

cri

A ran 3 ga watan Disamba na shekara ta 1941 ne, aka kafa gidan rediyon kasar Sin, wato CRI, wato daidai da ran 3 ga watan nan da muke ciki ke nan, CRI ya cika shekaru 65 da kafuwa. A kwanakin baya, bi da bi ne masu sauraronmu suka rubuto mana wasiku, inda suka taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa.

Don taya mu murnar cika shekaru 65 da kafuwa, shugaban kungiyar masu sauraron CRI ta Gombawa, malam Mohammed Idi Gargajiga ya rubuto mana cewa, da farko, ina sanar da ku cewa, a madadin dukkan masu sauraro na kungiyar COMBAWA CRI LISTENERS CLUB mai mambobi 1612 kuma bisa matsayina na shugaban club, muna taya CRI murnar cika shekaru 65 da kafuwa.

Muna mika babbar gaisuwa tare da jinjinawa da nuna fatan alheri da kuma sahihiyar godiya ga CRI da kuma 'yan uwa aminanmu ma'aikatan sashen Hausa na CRI. Muna fatan ubangiji Allah ya kara muku basira da hazaka da kwarin gwiwar tsayuwa kan duga-duganku na fadar gaskiya, kuma Allah ya kara muku koshin lafiya da kwanciyar hankali da wadatuwa.

A gare ni da dukan abokaina da 'yan uwana, CRI shi ne sahihin amininmu da muke sauraro a kullum kuma bisa muhimmancin CRI, ba za mu iya rabuwa da shi ba, domin shi wani haske ne mai haskakawa ga duk al'ummar duniya wajen fadakarwa da nishadantarwa da ilmantarwa, da kulla zumunci da aminci na gaskiya da jama'ar kasar Sin da na sauran kasashen duniya. Mun yi farin ciki da bude sashen Hausa a CRI, sabo da ta hanyar sauraron CRI, mun fahimci kasar Sin sosai, kuma jama'ar kasar Sin sun fahimce mu, yanzu mun zama 'yan uwa sosai, duk da cewa, muna nesa da juna, amma muna son juna.

Cikin shekaru masu yawa na can baya da suka gabata, muka soma sauraron gidan rediyon sabuwar kasar Sin na Yan'an da ya zama Rediyon Peking zuwa Rediyo Beijing zuwa CRI. Sabo da muhimmancin shirye-shiryen gidan rediyon CRI ne muka kafa wannan club namu cikin shekara ta 1979, bisa manufarmu ta kulla yin kyakkyawan zumunci sosai da jama'ar kasar Sin tare da ingiza ci gaban harshen Hausa a duniya. Domin fahimtar juna da samun ci gaba mai amfani ta fuskar musayar ala'du da kuma tabbatar da zama cikin aminci da lumana tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

CRI ta hanyar sauraronka muke iya sanin duk irin halin da duniya ke ciki a kullum. Kana sanya mana farin ciki da kyawawan shirye-shiryenka masu dadin ji. CRI kana ba da babbar gudunmawa wajen gina gada ta kulla zumunci da aminci na gaskiya tsakanin jama'ar kasar Sin da na sauran kasashen duniya.

Ba za mu iya mantawa da 'yan uwa aminai ma'aikatan sashen Hausa na CRI ba, lallai kun taka rawar gani, kuma kun cancanci babban yabo, sabo da kuna ba da fifitattun taimako na dukkan fannoni daban daban, da kuma sanya babban kokari wajen dada inganta tsarin shirye-shiryen sashen Hausa tare da kara kyautata yin hulda da mu masu sauraron CRI. Wannan ya dada ba mu sha'awa da kuma kara faranta mana zukata sosai, sabo da haka, muna kara nuna babban yabo da goyon baya na hakika tare da fatan alheri a gare ku.

Yanzu fata muke a kullum mu ga CRI ya dada ci gaba sosai kuma ya kara cimma nasarori masu muhimmanci. A nan za mu kara da cewa, muna sonka CRI, so na zahiri kuma muna taya ka murnar ranar cika shekaru 65 da kafuwa.

A madadin dukan ma'aikatan CRI, musamman ma ma'aikatan sashen Hausa, ina mika godiyarmu ga wadannan aminai masu sauraronmu, sabo da goyon bayan da kuka ba mu, wanda ya sa mana kaimi, kuma ya taimaka mana wajen kyautata shirye-shiryenmu. Nan gaba za mu kara yin kokari, don jin dadinku.(Lubabatu)