Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-06 16:23:59    
Ofishin jakadancin kasar Sin a Kenya ya ba da taimakon gina wata makaranta a kasar

cri
A gun taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a watan da ya gabata, kasashen Sin da Afirka sun yi shawarwari har sun tabbatar da wasu matakan hadin gwiwasu a fannonin al'adu da kiwon lafiya da ilmi da dai sauransu, a halin yanzu dai, gwamnatin kasar Sin tana kokarin daukar matakai, don cika alkawarin da ta dauka dangane da ba da taimako ga Afirka.

A ran 5 ga wata da safe, an yi ta wake-wake a hedkwatar MDD da ke birnin Nairobi, ashe, daliban makarantar Mcedo da ke birnin Nairobi su ne ke wake-wake da raye-raye don bayyana farin cikinsu, sabo da ofishin jakadancin kasar Sin a Kenya ya tsai da kudurin ba da kudade wajen gina azuzuwan makarantar. An dai kafa makarantar firamare ta Mcedo a shekara ta 2001, kuma makarantar tana wata unguwar matalauta mafi girma ta Nairobi, wato unguwar Mathare. Mazaunan unguwar su da kansu ne suka ba da kudaden gina wannan makaranta, amma sabo da mazaunan ba su da arziki, shi ya sa kudaden da suka bayar ba su isa ba. Sabo da karancin kudade, dakunan makarantar sun lalace, ba damar a yi amfani da shi, yanzu 'yan makarantar sama da 200 suna hayar azuzuwa domin karatu.

Bayan da ofishin jakadancin kasar Sin a Kenya ya sami wannan labari, sai ya yanke shawarar ba da kudaden taimako da yawansu ya kai dallar Amurka dubu 25, wajen gina dakunan makarantar, don kyautata irin wannan halin da ake ciki.'ina fatan taimakon da muka bayar zai iya samar da wani kyakkyawan muhallin karatu ga dalibai, haka kuma ya kara ba da taimako ga unguwar Mathare. Ina imani da cewa, wadannan dakunan karatu ba ma kawai za su iya amfana wa yaran da ke unguwar Mathare ba, haka kuma za su zamanto wata alamar zumuncin da ke tsakanin Sin da Kenya.'

A gun bikin ba da taimakon, mataimakin ministan ilmi na kasar Kenya, Kilemi Mwiria ya ce,'Ina son yin amfani da wannan dama, in nuna sahihiyar godiyarmu ga jama'ar kasar Sin ta bakin jakadan kasar Sin, sabo da a halin yanzu, kasarmu ba ta da karfin raya unguwannin matalauta, kuma gwamnatin Kenya tana bukatar taimako daidai a wannan fanni.'

A halin yanzu dai, kashi daya daga cikin uku na 'yan makarantar sama da 200 marayu ne, sauran kashi daya kuma sun zo ne daga iyalan da ke ba tare da ma'aurata ba, amma a wannan rana, sun manta da damuwarsu, suna wake-wake da raye-waye, suna cikin murna.'yau muna farin ciki sabo da makarantarmu na da azuzuwan karatu na kanta, inda za mu iya yin wasanni yadda muka ga dama.'

Sabo da taimakon da kasar Sin ta bayar, mai kula da harkokin unguwar Mathare ya tsai da kudurin cewa, za a canja sunan makarantar daga Mcedo zuwa makarantar Mcedo-Beijing, kuma labarin ya burge jakadan kasar Sin sosai, ya ce,'a ganina, wannan babbar karamawa ce ga jama'ar kasar Sin, a sa'i daya kuma, ya kara dora mana nauyi, ya kamata mu kara ba su taimako, mu kara inganta huldar aminci da hadin gwiwa a tsakanin jama'ar kasashen biyu, ta yadda za a kara inganta tushen hadin gwiwar aminci da ke tsakanin Sin da Afirka da kuma Sin da Kenya'.(Lubabatu)