Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-05 18:42:07    
Gidan ibada na tunawa da Zhuge Liang da kuma wurin shakatawa na hasumiyar Wangjianglou

cri

Jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa a cikin shiri namu na yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko dai za mu karanta muku wasu abubuwa game da wuraren shakatawa 2 na lardin Sichuan, wato gidan ibada na tunawa da Zhuge Liang da kuma wurin shakatawa na hasumiyar Wangjianglou. Daga bisani kuma, sai wani bayanin musamman mai lakabi haka 'wurin tarihi na Sanxingdui mai ban mamaki'.(music)

Gidan ibada na tunawa da Zhuge Liang mai fadin murabba'in mita 37,000 yana kusa da birnin Chengdu a kudu, babban birnin lardin Sichuan na kasar Sin. An gina shi ne bisa salon gine-ginen zamanin da na kasar Sin. An gina shi ne don tunawa da marigayi Zhuge Liang, wani shahararren dan siyasa da kuma mai tsara dabaru na zamanin daular Sanguo na kasar Sin, wanda ya zama wata alama ce ta hikima a cikin almarar kasar Sin. Marigayi Zhuge Liang ya ba da babban taimako wajen kafa gwamnatin daular Shu, ya kuma zama firayin minista. Ban da wannan kuma, ya ba da babbar gudummawa wajen dinkuwar kudu maso yammacin kasar Sin gaba daya da kuma raya tattalin arziki da al'adu.

Akwai kushewar marigayi Liu Bei a nan, wanda shi ne shugaba na farko na gwamnatin karamar kasar Shu. An sassaka mutum-mutumi na Zhuge Liang da Liu Bei da kuma labarunsu a kan tulunan da aka yi da tagulla da kwararrawa da katako da sauran kayayyaki. Irin wadannan kayayyaki suna da muhimmanci wajen nazarin tarihin daular Shu.

Wurin da ke kusa da wannan gidan ibada na tunawa da Zhuge Liang a gabas shi ne wurin shakatawa na hasumiyar Wangjianglou mai fadin murabba'in kadada 12.

An dasa kwarran gorori a gefunan hanyar da aka shimfida zuwa wannan hasumiya ta zamanin da. Furanni da kuma gorori iri daban daban sun yi yalwa a cikin wannan wurin shakatawa. Wasu daga cikin wadannan gorori ana samunsu ne a cikin lardin Sichuan kawai, yayin da saura kuma suka zo daga kudancin kasar Sin da kuma kasar Japan. An dasa gorori a gefunan dukan hanyoyi a wannan wurin shakatawa, sa'an nan kuma, an dasa bishiyoyi a kewayen dukan hasumiyoyi. Shi ya sa hasken rana ya zama kore saboda ya ratsa tsakanin wadannan gorori.

To, jama'a masu sauraro, muna muku godiya saboda sauraren shirinmu, kuma muna fatan za ku ci gaba da sauraren shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wurin tarihi na Sanxingdui mai ban mamaki, ya fi kyau ku karkade kunnuwanku don amsa tambayoyin da muka yi muku