Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-05 18:40:54    
Shan kofi zai ba da taimako wajen magance cutar hanta sakamakon shan giya

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku da bayani kan cewa, shan kofi zai ba da taimako wajen magance cutar hanta sakamakon shan giya, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka: Aikin koyar da ilmin sana'a na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri. To, yanzu ga bayanin.

Manazarta na kasar Amurka sun gano cewa, shan kofi zai ba da taimako wajen magance cutar hanta sakamakon shan giya, idan aka sha kwaf din kofi guda, to za a iya rage hadarin kamuwa da cutar hanta har kashi 20 cikin dari.

Yayin da ake gudanar da wani shirin kiwon lafiya a birnin Auckland na jihar California ta kasar Amurka, manazarta sun yi bincike kan mutane dubu 26, daga baya sun samu sakamakon da aka ambata a baya, kuma sun buga shi a cikin mujallar Imin likita na cikin jikin dan Adam ta kasar Amurka.

Mutanen da aka gudanar da binciken sun hada da maza da mata daga jinsi daban daban inda daga cikinsu akwai mashaya giya sosai yayin da wasu daga cikinsu sam ba su shan giya ko kadan. Kuma sakamakon binciken jini da aka gudanar kansu ya bayyana cewa, hantunan mutane da suke shan kofi suna da kyau ko da kuwa suna shan giya ko a'a. Shan kwaf din kofi guda a ko wace rana zai iya rage hadarin kamuwa da cutar hanta sakamakon shan giya har kashi 20 cikin dari, kuma idan ake shan kwaf din kofi hudu a ko wace rana, to za a iya rage hadarin har kashi 80 cikin dari.

Ban da wannan kuma a cikin rahoton, an bayyana cewa, an riga an gano cewa, akwai wani sanadari a cikin kofi da ke iya magance cutar hanta sakamakon shan giya, amma ba a gano takamaiman wannan sinadari ba. Bugu da kari kuma, Shan kofi tare da kirim da madara da sukari da sauran abubuwa da 'yan kasar Amurka su kan sanya cikin kofi yana ya ba da taimako sosai ga lafiyar jikinsu.

Bisa labarin da muka samu, an ce, ta sauran nazarin da aka gudanar kan wannan lamari, an kiyasta cewa, watalika sinadarin da ke cikin Kofi wanda ke ba da taimako wajen kare hanta shi ne caffein. Amma a cikin nazarin, ba a gano cewa, shan shayi zai ba da taimako wajen kare hanta ba, sabo da caffein da ke cikin shayi ya yi kadan idan an kwatanta shi da wanda ke cikin kofi.

A waje daya kuma manazarta sun nuna cewa, ba dukkan mutane masu shan giya za su iya kamuwa da ciwon hanta ba. Ko da yake shan kofi zai ba da taimako wajen kare hanta, amma dabara mafi kyau wajen magance cutar hanta sakamakon shan giya ita ce shan giya kadan ko kuma a daina shan giya sam a maimakon shan kofi da yawa.