Kwanan baya, jami'in gwamnatin kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta dauki matakai iri iri wajen kara saurin raya aikin ba da ilmin sana'a domin daga karfin neman aikin yi da kafa kananan masana'antunsu masu zaman kansu.
A cikin shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin za ta zuba kudaden da yawansu zai kai kudin Sin yuan biliyan 14 wajen aikin ba da ilmin sana'a. Madam Wu Qidi, mataimakiyar ministan ilmi ta kasar Sin ta ce, za a yi amfani da wadannan kudade ne domin kara saurin gina makarantun koyon ilmin sana'a da kafa asusun kudin yabo a makarantun koyon ilmin sana'a a yankuna daban-daban na kasar. Daga cikin wadannan kudade, tun daga shekarar da muke ciki, za a kebe kudin Sin yuan miliyan dari 8 a kowace shekara domin samar da kudin taimakon musamman ga dalibai matalauta wadanda suke karatu a makarantun koyon ilmin sana'a. Madam Wu ta ce, "Daliban da yawansu zai kai kashi 20 daga cikin kashi dari na duk wadanda suke karatu a makarantun koyon ilmin sana'a za su samu wadannan kudaden taimakon da gwamnatin tsakiya da gwamnatocin wuri da makarantu da al'umma za su samar. Wannan kokari zai bayar da gudummawa sosai wajen kara yawan daliban da za su yi karatu a makarantun koyon ilmin sana'a da ciyar da aikin ba da ilmi gaba cikin sauri kuma lami lafiya."
Yanzu, da akwai makarantun koyon ilmin sana'a misalin dubu 1 da dari 6 a duk fadin kasar Sin. Yawan daliban da suka gama karatu daga wadannan makarantu ya kai miliyoyi. A waje daya kuma, ana da makarantun koyon ilmi iri 2, wato makarantun koyon ilmin sana'a da makarantun koyon fasaha wadanda suke matsayin manyan makarantun sakandare da kwalejojin kimiyya da fasaha da makarantun horar da kwararru. A cikin halin da ake ciki yanzu, dalidan da suka gama karatu daga wadannan makarantu suna cikin halin farin ciki wajen neman aikin yi. Amma domin yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana ta samun cigaba cikin sauri sosai, aikin ba da ilmin sana'a yana koma baya. Bai iya biyan bukatun kwararru da ake nema ba.
Lokacin da ake yunkurin raya aikin ba da ilmin sana'a, ba ma kawai za a kara zuba kudade kan aikin ba da ilmin sana'a ba, har ma hukumomin ba da ilmi na kasar Sin za su dauki sabbin hanyoyin ba da ilmin sana'a. Yanzu, wani salon ba da ilmin sana'a yana yaduwa a duk kasar. Irin wannan salo shi ne "Taimakawa juna tsakanin kwalejin koyon ilmin sana'a da masana'antu". Ya zuwa yanzu, kwalejin koyon ilmin kimiyya da fasaha na lardin Hunan da ke daukar irin wannan salo ya riga ya rattaba hannu kan yarjejeniyoyin daukar ma'aikata da masana'antu 5. Mr. Yang Dongliang, shugaban wannan kwaleji ya ce, "Mun tsara shirin horar da dalibai bisa bukatun da masana'antu suke da su. Saboda haka, kafin dalibai su gama karatu, an riga an samar musu guraban aikin yi. Bisa yarjejeniyoyin da muka daddale, a shekara mai zuwa, za mu dauki dalibai 2000."
Ma'anar "Taimakawa juna tsakanin kwalejin koyon ilmin sana'a da masana'antu" ita ce, lokacin da dalibai suke koyon ilmin sana'a, za a samar musu damar yin gwaje-gwaje a masana'antu. Dalibai za su iya zaben ilmin da suke son koya. Bayan sun yi rabin shekara suna koyon ilmi a kwalejin, za su je masana'antu domin gwajin ilminsu, kuma za su biya su albashi. Bayan da suka kawo karshen karatunsu a kwalejoji da makarantun koyon ilmin sana'a cikin shekaru 3, za su iya samun guraban aikin yi a masana'antun da suka daddale yarjejeniya da kwaleji ko makarantu.
Masana'antu da kamfanoni da yawa suna maraba da irin wannan salon ba da ilmin sana'a. Madam Cai Yan, babbar direktar wani kamfanin abinci na birnin Changsha, hedkwatar lardin Hunan ta ce,"Mu ma za mu aiki da masananmu zuwa makarantu da kwalejoji na koyon ilmin sana'a. Sakamakon haka, dalibai za su iya sanin masana'antar da za su je cikin sauri. Bayan hawarsu kan guraban aikin yi, za su san aikinsu cikin kwanaki 3 ko 5 kawai."
Wani jami'in ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ya bayyana cewa, za a kara neman sabbin hanyoyin ba da ilmin sana'a da za su iya biyan bukatun da ake nema. A waje daya kuma, za a kara saurin kyautata ingancin malamai wadanda suke aiki a hukumomin ba da ilmin sana'a. (Sanusi Chen)
|