Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-04 17:26:57    
Takaitaccen bayani game da kabilar Kazak

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanmu da sake saduwa a cikin shirinmu na yau na Kananan kabilun kasar Sin. A cikin shirinmu na yau, da farko dai za mu bayyana muku wata karamar kabilar kasar Sin, wato kabilar Kazak kamar yadda muka saba. Sa'an nan kuma, za mu bayyana muku yadda wata malamar kasar Sin take taimakawa dalibanta wajen karatu. To, yanzu ga bayani game da kabilar Kazak.

Yawancin mutanen kabilar Kazak suna zama a shiyyar Yili ta kabilar Kazak mai cin gabashin kanta da gandumar Mulei ta kabilar Kazak da gandumar Balikun ta kabilar Kazak a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta. Wasu ba da yawa ba suna zama a gandumar Akesai ta kabilar Kazak mai cin gashin kanta ta lardin Gansu da shiyyar Haixi ta kabilun Mongoliya da Kazak mai cin gashin kanta a lardin Qinghai. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Kazak ya kai kimanin miliyan 1 da dubu 250. Suna da yaren Kazak. Har yanzu ana nazarin kalmomin yaren Kazak, amma ba a same su ba tukuna.

A da, mutanen kabilar Kazak sun yi zama a filin ciyayi na Kazak da yankunan da ke kudu da gabas da tafkin Barkash inda ke karkashin mulkin janar Yili na daular Qing ta kasar Sin. Amma a tsakanin shekarar 1864 da ta 1883, daular kasar Rasha ta tilasta gwamnatin daular Qing ta kasar Sin da ta sa hannu kan jerin yarjejeniyoyin sacin yankunan kasar Sin ta hanyoyin munafunci da karfin tuwo. Wannan yankunan da kasar Rasha ta sata yankuna ne da mutanen kabilar Kazak suka yi zama. Amma bayan shigowarsu a hannun tsohuwar gwamnatin Rasha, ta danne su kwarai. Sakamakon haka, mutanen Kabilar Kazak sun fara gudu daga wadannan yankuna, sun tafi yankunan kasar Sin. A jihar Xinjiang, mutanen kabilar Kazak sun bayar da gudummawa sosai ga bunkasuwar tattalin arzikin yankunan da ke iyakar kasar Sin da kasashen waje.

A da, yawancin mutanen kabilar Kazak suna kiwon dabbobi a ciyayi. Babu masana'antun zamani a yankunan da suke zama. Amma, yanzu, ba ma kawai suna ci gaba da kiwon dabbobi ba, hatta ma suna da masana'antun zamani iri iri, kamar su filin hakar man fetur ta Klamayi da filin hakar man fetur na Dushanzi kuma da masana'antun samar da garin alkama da yawa. Bugu da kari kuma, suna yin ciniki da 'yan kasuwa na kasashen waje domin suna zama a yankunan da ke iyaka a tsakanin Sin da kasashen waje.

Kabilar Kazak tana da al'adun Kazak da ke bayyana yadda ake kiwon dabbobi da yin aikin gona. Al'adun kasar Ukraim da kabilar Tatar da al'adun sauran yankunan kasar Sin sun kai shi tasiri sosai. Bisa kididdigar da aka yi, litattafan wakokin kabilar Kazak ya kai fiye da dari 2.

Mutanen kabilar Kazak suna bin addinin Musulunci. Sabo da haka, babbar sallah da karamar sallah muhimman bukukuwa ne na kabilar Kazak.