Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-03 18:41:16    
An taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin

cri

Yau da shekaru 65 da suka wuce, wata wayar rediyo ta fito daga wani kogon da ke arewa maso yamma na kasar Sin. Wannan ne karo na farko da gidan rediyo na Xin Hua da ke garin Yan'an ya watsa shirinsa da harshen Japan. Gidan rediyo na Xin Hua da ke garin Yan'an, tsohon suna ne na gidan rediyon kasar Sin na yanzu. A cikin shekaru 65 da suka wuce, sha'anin watsa shirye-shirye ga kasashen waje na jama'ar kasar Sin yana ta samun cigaba. Gidan rediyon kasar Sin ma yanzu ya zama wani gidan rediyon da ke daya daga cikin muhimman gidajen rediyo na duniya wadanda suke yin tasiri sosai a duniya. Yau, ran 3 ga wata, an shirya bikin taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin a nan birnin Beijing.

An yi wannan shagali ne cikin halin fara'a sosai. Mutane daruruwa na kasar Sin da na waje sun halarci wannan shagali domin taya murnar ciko shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin.

Mr. Li Changchun, memban zaunennen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya aika da wata wasika, inda ya taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin, ya kuma gai da ma'aikatan gidan rediyon kasar Sin.

A gun bikin, a cikin nasa jawabi, Mr. Liu Yunshan, memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda ke kula da aikin ba da labaru a kasar Sin ya yaba wa gudummawar da gidan rediyon kasar Sin ya bayar a cikin shekaru 65 da suka wuce. Mr. Liu ya ce, "Aikin watsa labaru ga kasashen waje yana tabbatar da sunan kasar Sin a duk duniya cikin hali mai kyau. A waje daya kuma, yana bayar da muhimmiyar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da neman bunkasuwa tare a duk duniya."

Ba ma kawai shugabanninmu na kasar Sin sun taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin ba, har ma shugabannin kasashen waje, ciki har da Jacques Chirac, shugaban kasar Faransa da Durao Barroso, shugaban kwamitin kunigyar Tarayyar Turai da Traian Basescu, shugaban kasar Romania da Vladimir Voronin, shugaban Jamhuriyar Moldova da Romano Prodi, firayin ministan gwamnatin kasar Italiya da madam Gloria Arroyo, shugabar zagaye na kunigyar hada kan kasashen da ke kudu maso gabashin Asiya kuma shugabar kasar Phillippines da Mr. Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya da Jakaya Kikwete, shugaban kasar Tanzania da shugaba Hadj Omar Bongo na kasar Gabon da madam Ellen Johnson-Sirleaf, shugabar kasar Liberia da shugaba James Michel na kasar Seychelles da Navinchandra Ramgoolam, firayin ministan kasar Mauritius da sauran kasashen duniya sun kuma aika da wasiku ko sun rubuta kalmomi domin taya wa gidan rediyon kasar Sin murna.

Sa'an nan kuma, wakilan masu sauraro 15 wadanda suka zo daga kasashen Amurka da Canada da Rasha da Kenya da Jamus da Indiya da kuma kasar Afghanistan sun zo nan birnin Beijing musamman domin taya wa gidan rediyon kasar Sin murna. Wata mai sauraro ta kasar Amurka ta ce, "Ina taya murnar cikon shekaru 65 da kafuwar gidan rediyon kasar Sin. Tun daga shekarar 1999 ce na fara sauraran shirye-shiryen gidan rediyon kasar Sin. Na samu ilmomi iri iri game da kasar Sin daga shirye-shiryenku. Yau, ina farin ciki sosai domin samun damar halartar wannan biki."

Yanzu, gidan rediyon kasar Sin yana watsa shirye-shirye iri iri ga masu sauraro da ke zama a duk duniya da harsunan waje 38 tare da yaren kasar Sin 4. Jimlar sa'o'in shirye-shiryen da yake watsawa a kowace rana ta kai fiye da dubu 1 da dari 1. Sabo da haka, Mr. Wang Taihua, ministan da ke kula da harkokin sinima da rediyo da talibijin na kasar Sin ya ce, "Kungiyoyin masu sauraro da miliyoyin masu sauraro wadanda suke zama a duk fadin duniya sun saurari shirye-shiryen gidan rediyon kasar Sin domin suna da sha'awa sosai kan al'adun kasar Sin. Suna kuma mai da hankali sosai kan makomar gidan rediyon kasar Sin. Yanzu, sun riga sun zama wani karfin da ke ciyar da gidan rediyon kasar Sin gaba."

Jama'a masu karatu, yanzu ba ma kawai gidan rediyon kasar Sin yana watsa shirye-shiryensa da gajerun zango ba, har ma yana da shafin Internet da jarida da shirye-shiryen talibijin da mujalla. Bugu da kari kuma, tun daga ran 28 ga wata Janairu na shekarar da muke ciki, ya kafa wata tashar FM ta farko a birnin Nairobi na kasar Kenya. Sa'an nan kuma, a ran 19 ga watan Nuwamba da ya wuce, gidan rediyon kasar Sin ya kafa tashar FM ta biyu a birnin Vientian na kasar Laos. Bisa shirin da aka tsara, nan da shekaru 5 masu zuwa, gidan rediyon kasar Sin zai kafa tasoshin FM dari 1 a duk fadin duniya.

Amma, muna ganin cewa, idan mun kwatanta da gidajen rediyon duniya na kasashe masu arziki, gidan rediyon kasar Sin yana bayansu sosai. Sabo da haka, Wang Gennian, shugaban gidan rediyon kasar Sin ya ce, za a raya tsarin zamani na watsa labaru ga duniya. Mr. Wang ya ce, "Ma'anar tsarin zamani na watsa shirye-shirye ga duniya ita ce, ya kamata a yi amfani da tunanin zamani wajen tsara da watsa shirye-shiryenmu, shirye-shiryen da muke watsawa kuma suna dacewa da halin da ake ciki a duniya. Sa'an nan kuma dole ne mu dauki hanyar zamani domin yada shirye-shiryenmu." (Sanusi Chen)