Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-12-01 15:57:04    
Ana daukar masu aikin sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing

cri

Bisa matsayin wani muhimmin kashi dake cikin aikin share fage ga taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a shekarar 2008, a ran 28 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, a hukunce ne aka soma yin aikin daukar masu aikin sa kai domin taron wasannin motsa jiki na Olympic da taron wasannin Olympic na nakasassu na shekarar 2008. Wato ke nan tun daga wannan rana ne ,masu aikin sa kai wadana suke son ba da taimakonsu ga wadannan tarurrukan wasannin Olympic guda biyu za su iya yin rajista.

A gun taron watsa labarai da aka shirya a wannan rana, mataimakin shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing Mr. Li Binghua ya bayyana shirin karbar masu aikin sa kai. Ya furta, cewa:

' Bayan da aka yi bincike da nazari, an tsaida kudurin daukar masu aikin sa kai da yawansu ya kai kimanin 70,000 domin yin aikin hidima ga taron wasannin Olympic na 29; ban da wannan kuma , akwai masu aikin sa kai da yawansu ya kai kimani 30,000 da za su yi aikin hidima ga taron wasannin Olympic na 13 na nakasassu. Za a rarraba wadannan masu aikin sa kai zuwa filaye da dakunan gasanni 31, da kuma guda 14 da ba na gasanni ba, da filaye da dakunan horon wasanni sama da 40, da otel-otel da kuma tashoshin sufuri dake cikin birnin Beijing har da filaye da dakunan wasannin motsa jiki daban daban na sauran birane 6 wadanda za su ba da taimako ga gudanar da taron wasannin Olympic na shekarar 2008. Wadannan masu aikin sa kai za su yi aiki ne a fannin ayyukan shirya gasanni, da yin hidima ga 'yan kallo, da tsaron zirga-zirga, da karbar manyan baki, da yin hidima cikin harsunan waje, da watsa labarai da kuma na yin ceto da jiyya da dai sauran fannoni kusan 80.

Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya fayyace, cewa muhimmin sharadin rajistan masu aikin sa kai, shi ne wanda shekarunsa ya cika 18 da haihuwa a wata daya kafin a gudanar da bikin taron wasannin Olympic a shekarar 2008 kuma ba tare da kayyade yawan shekarun haihuwa ba. Ban da wannan kuma, an bukaci wadanda suka yi rajista da su bayyana sharudan da suke da su cewa: su shiga ayyukan hidima ga taron wasannin Olympic na Beijing da kuma taron wasannin Olympic na nakasassu bisa son ransu; kuma su nuna biyayya ga dokokin shari'a na kasar Sin, da shiga harkokin horaswa da kuma sauran harkokin da abun ya shafa kafin a gudanar da gasanni; kuma su yi hidima na sama da kwanaki 7 a duk tsawon lokacin da ake gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing da taron wasannin Olympic na nakasassu; sa'annan su rike karfin iyawa na yin amfani da harsuna da kuma fasahohi da ilmi na sana'ar musamman wadanda suka wajaba ga yin hidima bisa son ransu.

An labarta, cewa tun daga ran 28 ga watan Agusta, masu aikin sa kai na shiyyar Beijing suka soma yin rajista ; kuma daga watan Disamba na shekarar da muke ciki, masu gabatar da roko na larduna, da jihohi masu cin gashin kansu da kuma birane mallakar gwamnatin tsakiya kai tsaye dake waje da Beijing za su yi rajista; Dadin dadawa, tun daga watan Maris na shekara mai zuwa, 'yan-uwa na yankin Hong Kong ,da Macao da kuma na Taiwan, da Sinawa 'yan kaka-gida da kuma dalibai dake dalibta a ketare har da baki na kasashen waje za su yi rajista. Ban da wadannan kuma, za a dauki masu aikin sa kai na birnin Qingdao, da birnin Tianjin, da birnin Shanghai, da birnin Shenyang, da birnin Qinghuangdao da kuma yankin Hong Kong wadanda suka ba da taimako wajen gudanar da taron wasannnin Olympic na Beijing daidai bisa manufofin da hukumomin shirye-shirye na wadannan wurare suka tsara.

Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya kuma shelanta, cewa ban da masu aikin sa kai da yawansu ya kai 100,000 da za su yi aikin hidima a dakuna da filayen wasannin Olympic na shekarar 2008, ana kuma bukatar samun masu aikin sa kai da yawansu ya zarce dubu goma na birane, wadanda za a rarraba su kan tituna manya da kanana domin karbar baki daga duk kasar da kuma duk duniya cikin murmushi. Za a soma daukar masu aikin sa kai na birane ne a farkon shekara mai zuwa.

Mr. Liu Qi, shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya siffanta, cewa murmushin masu aikin sa kai ya kasance tamkar kati ne mafi kayatarwa na Beijing, ya kuma yi lale da mutanen dake neman zama masu aikin sa kai na taron wasannin Olympic na Beijing. ( Sani Wang )