Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-30 16:21:49    
Cibiyoy da hukumomin na kasar Sin wadanda ke kula da harkokin Afrika, babi biyu

cri

Yang Dongliang , mataimakin shugaban birnin Tianjin shi kuma ya yi jawabi , inda ya bayyana cewa , A ran 14 ga watan Agusta a nan birnin Tianjin , An rufe taro na 4 na Majalisar Wakilan Jama'ar birnin Tianjin ta 10 . Taron ya zartas da Shirye-shiryen raya tattalin arzikin birnin da zaman al'umman Tianjin a shekaru 5 masu zuwa da rahoton aikin gwamnati .

Bisa shirye-shiryen da aka zartas , an ce , a cikin shekaru 5 masu zuwa , yawan madaidaicin karuwar tattalin arzikin birnin Tianjin na shekara-shekara zai kai kashi 9.5 cikin 100 . Kuma an tabbatar da makasudin rage yawan makamashin da za a yi amfani da rage yawan gurbatattun abubuwan da za a fitar . A cikin shekaru 5 masu zuwa , aikin kafa sababbin kauyyuka da hanzarta gyare-gyaren tattalin arziki da ciyar da yalwatuwar unguwoyi da gundumomi cikin daidaici , za su zama tsarin musamman da manyan ayyukan birnin Tianjin .

Mr. Yang ya ce , a birnin Tianjin za a kau da haramtattun aikace-aikacen cinikin litattafai da faye-faye masu satar ikon mallakar ilmi .

Ning Wanglu , mataimakin shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta birnin Tianjin ya bayyana cewa , tun daga farkon wannan shekara sassa daban daban na Hukumar ta riga ta yi binciken al'amuran keta ikon lambobin kasuwanci .

Mr. Ning , mataimakin shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta birnin Tianjin ya sanar da wannan labari ne a gun taron manema labarun da Ofishin watsa labaru na Gwamnatin birnin Tianjin ya shirya .

Jama'a masu sauraro , yanzu sai ku 'dan shakata kadan, daga basani kuma za mu dawo domin karanta shirinmu na Me ka sani game da kasar Sin .

Mr. Ning , mataimakin shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta birnin Tianjin Ya yi nuni da cewa , a wajen kiyaye ikon musamman na lambobin kasuwanci da aka rajista , Birnin Tianjin tana mai da hankali sosai kan lambobin kasuwanci na kasar Sin da na kasashen waje .

Ya kuma bayyana cewa , A cikin aikin mun kara karfin musamman don kiyaye ikon mallakar ilmin lambobin kasuwanci na kasashen waje .

Mr. Ning ya bayyana cewa , a cikin shekaru 5 da suka shige , mun dauki aikin kiyaye shahararrun lambobin kasuwanci na kasashen waje kamar wani muhimmin aiki na bnirnin Tianjin na kasar Sin . Musamman ma daga shekarar 2004 zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara , Ofishin lambobin kasuwanci da Kwamitin duba lambobin na hukumar sun yi amincewa da shahararrun lambobin kasuwanci guda 30 na kasashen waje .

Kasar Sin tana daya ce daga cikin kasashe masu fama da lambobin jebu a duniya . Bayan da aka shiga sabon karni , kasar Sin ta dauki matakan magance laifufkan kera lambobin jebu .

A gun taron manema labarun da Ofishin watsa labaru na Majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya a ran 15 ga wata a nan birnin Beijing , Li Dongsheng , shugaban Hukumar kula da aikin masana'antu da kasuwanci ta birnin Tianjin ya ce , kasar Sin ta yi na'am da wadannan shahararrun lambobin kasuwanci kuma tana kiyaye ikon mallakar ilminsu , ta sami yabo sosai daga masana'antu masu yawa musamman ma wasu manyan kamfanonin ketare kuma sun karfafa amincewar aikin kiyaye ikon mallakar ilmin lambobin kasuwanci na kasar Sin . Saboda haka , kasar Sin ta jawo hankulan kasashe masu yawa su zo nan kasar Sin don rajista lambobinsu . Mu ma haka , birnin Tianjin zai aiwatar da manufar gwamnatin kasar Sin , kuma za mu mai da hankali sosai kan kananan fannoni.(Ado)