Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-30 14:58:35    
An bude taro na 3 na hukumar kare hakkin dan adam ta M.D.D.

cri

A ran 29 ga wata a birnin Geneva, an bude taro na 3 na hukumar kare hakkin dan adam ta M.D.D. A gun taron za a tsara tsare-tsare da dokokin ayyukan da za a yi cikin majalisar da kuma tattaunawa kan matsalolin gaggawa da ake fuskanta yanzu a fanning hakkin dan adam na kasashen duniya. Yanzu sabane-sabanen da ke tsakanin kasashe masu sukuni da na masu tasowa cikin majalisar sai kara bayyanuwa suke.

A gun bikin bude taron, Madam Louise Arbour, babbar jami'i mai kula da hakkin dan adam na M.D.D. ta karanta wata wasikar da Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya rubuta zuwa ga babban taron, cikin wasikar, Mr. Annan yana fatan hukumar kare hakkin dan adam za ta iya kira wani taron musamman kan matsalar Darfur ta Sudan. Ya bayyana cewa, tun bayan kafuwar majalisar, an riga an kira tarurruka sau 3 musamman kan hargitsin da ake yi tsakanin Larabawa da Isra'ila, bai kamata wannan matsala ta hana a daidaita sauran matsalolin kasashen duniya ba. A ran 29 ga wata, masu halartar taron sun saurari rahoton ayyukan da Madam Arbour ta yi, wanda a ciki ta bayyana cewa, halin haki hari kan hakkin dan adam ya yi tsanani a yankunan Palesdinu da aka mamaye, kuma yana ta kara lalacewa. Ta nemi Palesdinu da Isra'ila da su dauki matakai don hana hauhawar hargitsin da ake yi da karfin tuwo. Cikin jawabin da wakilin kasar Sin ya yi, ya sake yin kira ga sassan da abin ya shafa da su gudanar da kuduran da abin ya shafa na M.D.D. ta yadda za a shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a bangaren Palesdinu da Isra'ila.

Manazarta sun bayyana cewa, ko da yake tsawon lokacin kafuwar hukumar kare hakkin dan adam ta M.D.D. bai kai rabin shekara ba, amma sabane-sabanen da ke tsakanin kasashe masu sukuni da na masu tasowa kan wasu matsaloli sun riga sun bayyanu, musamman ma kan wadannan matsaloli 2, wato na farko shi ne, kan yadda za a kira taron musamman. Wasu ra'ayoyin jama'a na kasashen yamma sun bayyana cewa, tun bayan kafuwar majalisar, an riga an kira tarurruka sau 3 musamman kan hargitsin da ake yi tsakanin Larabawa da Isra'ila, kuma an kai suka sosai kan Isra'ila bisa laifinta na kai hari kan hakkin dan adam, amma "ana zuba ido ana kallo kawai" a gaban halin keta hakkin dan adam da gwamnatin Sudan ke yi. Sun ce, dalilin da ya sa aka yi haka shi ne sabo da kasashe masu tasowa sun nuna "rashin adalci". Amma kasashe masu tasowa sun bayyana cewa, matsaloli 2 wato hargitsin da ake yi tsakanin Larabawa da Isra'ila da matsalar Darfur halinsu ya sha bamban sosai. Matsala ta farko ita ce kai hari daga waje wato Isra'ila ta nuna karfin soja ta keta hakkin dan adam na jama'ar Palesdinu, amma matsalar Darfur ita ce harkokin da ke cikin wata kasa kawai, ya kamata kasashen duniya sun sa kaimi ga bangarorin 2 da su ajiye makamansu bisa harsashin girmama mallakar kan kasar Sudan, kuma a daidai hargitsin ta hanyar yin shawarwari.

Sabani na 2 da ke tsakanin kasashe masu sukuni da na masu tasowa shi ne, bambancin ra'ayin da suka dauka kan ikon kwararru masu 'yanci da kungiyoyin aiki da masu ba da rahoto na musamman a fannin hakkin dan adam na M.D.D.

Manazarta sun bayyana cewa, a da kasashen yamma sun mai da hakkin dan adam a matsayin kayan aiki na siyasa don matsa wa kasashe masu tasowa lamba, kwamitin hakkin dan amma ya zama wurin da yin dagiya tsakanin kasashen kudu da na arewa wajen siyasa, har kwarjininsa ya zube kwata-kwata. Sabo da haka, da kyar wasu kasashen yamma za su bar tunaninsu da hanyoyin da suka bi a da cikin gajeren lokaci ba. Ba shakka za a gamu wa da tarin wahalhalu cikin yunkurin yin kwaskwarima ga hukumar kare hakkin dan adam. (Umaru)