Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-29 17:44:03    
Sabon shugaban kasar Kongo Kinshasa yana fukskantar da dama da kalubale

cri

Ran 27 ga wata, kotun koli ta kasar Kongo Kinshasa ta yi watsi da daukaka kara da Mr. Jean Pierre Bemba mataimakin kasar ya yi a dangane da sakamakon babban zabe da hukumar zabe ta bayar, inda ta tabbata da cewa, Mr. Joseph Kabila shugaban yanzu shi ne ya lashe zaben zagaye na biyu da aka yi a ran 29 ga watan Oktoba.

Masu bincike suna ganin cewa, akwai jan aiki a gaban shugaba Kabila wanda shekarunsa 35 ne a duniya, bayan haka kuma wannan kasar ta taba fadawa da yake-yake da dama kuma tana yin fama da talauci.

Matsala ta farko ita ce yaya shugaba Kabila zai daidaita huldar da ke tsakaninsa da Mr. Bemba abokan gasa nasa. Tun daga farkon babban zabe, Bemba ya nuna ra'ayin kiyyaya sosai, kuma ya nuna wannan ra'ayin kiyyaya ta hanyar soja yadda yake ga dama. Kafin a fitar da sakamakon babban zabe na zagaye na farko, an taba yin batu kashi a tsakanin dakarun Bemba da masu tsaron lafiyar Kabila. Bayan an fitar da sakamakon babban zabe na zagaye na biyu, Mr. Bemba ya nuna cewa, wai zai yi adawa da wannan sakamako "ta hanyar doka", amma, mutane da yawa suna ganin cewa, Bemba shi da kansa ya shirya tashin hankali da ta faru a ran 21 ga wata, da al'amarin sa wuta wa kotun koli. Ran 28 ga wata, Bemba ya bayyana cewa ya karbi sakamakon da kotun koli ta tsai da wato Kabila ya ci babban zabe, kuma zai shiga bangare mai adawa.

Wani kalubalen daban da shugaba Kabila zai fuskanta shi ne yaya zai iya samun goyon baya daga jama'an da ke yankin yamma cin kasar. An haife shi a yankin gabas, bayan ya hau karagar mulkin kasa a shekarar 2001, ya yi kokari sosai don warware rikicin da ke yankin gabas, kuma ya sami goyon bayan jama'an da ke wurin, shi ya sa, yawancin matune masu goyon bayansa suna yankin gabas. Amma, a yankin yamma fa ba yawa. Ban da haka kuma, shekarunsa 35 ne kawai, wannan abin kyau kuma abin laifi ne, saboda kullum ana ganin cewa, ba shi da ilmin jagorar kasa.

Na uku, kafa sojojin gwamnati zai zama wata matsala mai wuya. An yi babban zabe a karkashin halin ba a sake tsara duk rundunonin kasar ba. Bisa shirin da aka yi, ya kamata gwamnatin kasar Kongo Kinshasa ta sake tsara duk rundunonin bangarorin dabam daban kafin karshen shekarar 2005, da kuma kafa wata rundunar soja ta gwamnati mai mambobi dubu 100. yanzu, bayan Kabila ya kama karagar mulkin kasa, wannan matsala ta sake bullo. Kafa wata rundunar soja ta gwamnatin kasa yana da ma'ana mai muhimmaci kwarai da gaske ga ayyukan raya kasa da bunkasuwar tattalin arziki, amma wannan bukatar shugaba Kabila ya yi shawarwari da dakaru dabam daban, kuma sake tsara musu, wannan zai zama wata matsala sosai.

Ko da yake akwai jan aiki a gaban shugaba Kabila, amma akwai wasu dama da goyon baya a gabansa.

Da farko, sakamakon babban zabe ya nuna ra'ayin jama'a, jama'a za su goyon baya gwamnatin da suka zabi. Wannan sau na farko ne da kasar Kongo Kinshasa ta yi babban zabe ta hanyar dimokuradiyya tun daga ta sami 'yancin kasa kafin shekaru 46, kuma wannan sau na farko ne da jama'an kasar Kongon Kinshasa su dandana dimokuradiyya.

Na biyu, kasar Kongo Kinshasa tana da albarkatun kasa da yawa, akwai kashi daya cikin kashi uku na duk ma'adinin Cobalt na duniya da ma'adinan jan karfe da zinariya da nu'u-nu'u da yawa a yankunan yamma da tsakiya na wannan kasa. Idan a haka wadannan al'barkatu yadda ya kamata, za a kafa wani tushe mai kyau ga ayyukan raya kasa.

Na uku, sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya da Kungiyar gammayar kasashen Turai za su cigaba da kasancewa a kasar Kongo Kinshasa. Za su yi wa tasiri mai yakini ga zaman karko na kasar. Yanzu, akwai sojojin kiyaye zaman lafiya fiye da dubu 17 na Majalisar dinkin duniya suna kasar Kongo Kinshasa, wannan wani aikin mafi babba da MDD ta yi wanda ta aika da sojoji mafi yawa a tarihi. Ban da haka kuma, kungiyar gammayar kasashen Turai sun aika da wata runkuni mai mambobi dubu 2.4 zuwa kasar Kongo Kinshasa don biyan bukatar da MDD ta yi. Bayan Mr. Kabila ya kama karagar mulkin kasa, wadannan sojojin kiyaye zaman lafiya za su taimaka masa wajen kafa ikon mulkinsa mai karko.