A nan birnin Beijing, da akwai wani dakin yin taron tattaunawa kan fasaha , sunansa shi ne " Alamar tunawa da Afrika" wanda a ciki ake nuna fasahohi da al'adu na kasashen Afrika. Masu dakin taron nan su ne wani namiji mai suna Li Sonshan da matarsa mai suna Han Rong wadanda suka yi zaman rayuwa a kasar Tanzaniya cikin dogon lokaci. Malam Li Sonshan da matarsa suna kokarin nazari kan kayayyakin da Makonde ke sassakawa ta hanyar yin amfani da katako da kuma tanada irin wadannan kayayyaki, ba ma kawai sun kafa wani gidan baje koli na nuna kayayyakin fasaha na Makonde a kasar ba, hatta ma tare da masu fasahohi na kasar ne suka kafa wata hadadiyyar kungiyar fasahar Makonde ta kasar Tanzaniya.
Kabilar Makonde tana zama a kudu maso gabashin kasar Tanzaniya da arewacin kasar Mozambique, kabilar ita ce kabilar da ke da fasahohi sosai a kasashen Afrika, mazan kabilar suna kan aikin gargajiya na sassaka, kayayyakin fasahohin da suka sassaka , mutanen kasashen waje sun nada sunayensu da sunan kabilar, wato Makonde.
Mr Li Sonshang yana da shekaru 65 da haihuwa a shekarar da muke ciki, matarsa Han Rong tana da shekaru 61 da haihuwa. A cikin shekaru fiye da 20, sun tattara kayayyakin fasahar Makonde da aka yi ta hanyar sassakar katako da yawansu ya kai dubu goma.
Ina dalilin da ya sa Mr Li Sonshang da matarsa Han Rong suke da nasaba da fasahohin Makonde?
A shekaru 60 na karnin da ya shige, Mr Li Sonshang da matarsa sun yi karatu a wata jami'a don koyon harshen Swahili, a karshen shekaru 70 zuwa shekaru 80 na karnin da ya shige, ba sau daya ba ba sau biyu ba gwamnatin kasar Sin ta aika musu zuwa kasar Tanzaniya don shiga ayyukan ba da taimakon tattalin arziki. To a daidai wannan lokaci ne suka yi karo da kayayyakin fasaha na Makonde, a shekarar 1984, Mr Li Sonshang ya yi aikin fassara ga nunin fasahohin sassakar katako na Makonde a gidan baje kolin kayayyakin fasaha na kasar Sin, wannan ne karamin nunin da kasar Tanzaniya ta shirya a kasar Sin, amma ya burge 'yan kallo na kasar Sin sosai. Mr Li sonshang ya waiwayo cewa, al'amarin nan ya yi girgiza ni sosai, tun lokacin da nake aiki a kasar Tanzaniya, na soma kaunar irin kayayyakin fasaha sosai da sosai, shi ya sa na tattara su da yawansu ya wuce 100, na ji cewa, irin kayayyakin na da kyaun gani sosai, daga nan sai na kara tattara su.
Mr Li Sonshang tare da matarsa suna ci gaba da tattara irin kayayyaki, kuma sun kafa wani dakin tattaunawa da kayayyakin fasaha na kasashen Afrika, matar Li Songshang madam Han Rong ta bayyana cewa, muna son samar wa samarin kasar Sin damar shiga ko kuma fahimtar abubuwan kasashen Afrika, mu ne muke iya zama masu jagoranci gare su, ko masu gabatarwa gare su a kan kayayyakin fasaha na kasashen Afrika, ina son dakin tattaunawa ya zama wani dandalin tattaunawa da samarin kasar Sin suke kaunarsa wajen yin nazari kan kayayyakin fasahohin kasashen Afrika.
A shekarar 1990, Mr Li songshang da matarsa sun kaura zuwa kasar Tanzaniya, a kasar , sun yi harkokin kasuwanci , bisa taimakon arzikin da suka samu daga kasuwanci ne, suna ci gaba da tattara kayayykin fasaha na Makonde, sun taba shan wahalhala da yawa, amma ba su katse ba, kuma sun kulla aminci da masu fasahohi na kabilar Makonde. A ganin Mr Li Sonshang, kayayyakin fasaha na Makonde arziki ne na duk 'yan Adam. ya bayyana cewa, a duk tsawon lokacin raya sha'aninmu da bunkasa sa, mun sha wahaloli da yawa, amma a gaskiya dai ne muka sami sakamako da yawa. Za mu nemi damar bayar da su a kyauta ga zamantakewar al'umma da kasarmu, duk saboda su ne kayayyakin fasaha na 'yan Adam.(Halima)
|