Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-29 16:56:51    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(23/11-29/11)

cri
Ran 20 zuwa ran 22 ga wannan wata, a nan Beijing, an yi taron kara wa juna ilmi kan yin mu'amala da hadin gwiwa kan aikin bayar da kariyar tsaro da yaki da ta'addanci domin taron wasannin Olympic na Beijing. Cibiyar ba da umurni kan bayar da kariyar tsaro ta taron wasannin Olympic na Beijing da kwalejin nazarin aikata laifuffuka a shiyya-shiyya da dokoki ta Majalisar Dinkin Duniya sun shirya wannan taro cikin hadin gwiwa. Kwararru 12 masu ilmi ba da kariyar tsaro na kasashen waje sun yi hakuri sun amsa tamayoyin da kasar Sin ta bayar yadda ya kamata, sun kuma ba da shawarwari masu yakini da yawa kan aikin bayar da kariyar tsaron domin taron wasannin Olympic na Beijing.

Ran 24 ga wata, tawagar wakilai ta 'Fuwa ta kawo wa duniya fatan alheri' ta isa birnin Helsinki, babban birnin kasar Finland, inda ta shirya harkokin mu'amalar al'adu a jere a wurin. Wannan tawaga tana kula da aikin yayata abubuwan nuna fatan alheri na taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 wato Fuwa a duk duniya. Aikin 'Fuwa ta kawo wa duniya fatan alheri' wani aikin yayata al'adu ne don yada ra'ayin wasan Olympic da kuma kawo wa duniya fatan alheri.

Ran 23 ga wata, a Hong Kong, an fara daukar masu aikin sa kai domin gasar wasa da dawaki ta taron wasannin Olympic na karo na 29 a hukunce. Za a dauki masu aikin sa kai daga duk duniya, dukan mutanen da suka iya shigi da fici daga Hong Kong a lokacin horo da kuma lokacin taron wasannin Olympic, sa'an nan kuma sun zama ko yada zango a Hong Kong suna iya yin rajista.

Ran 25 ga wata, wutar yula ta taron wasannin motsa jiki na Asiya na Doha ta koma kasar Qatar. An yi kwanaki 55 ana bai wa juna wannan alamar zumunci da zaman lafiya a tsakanin kasa da kasa. A wannan rana, wannan wutar yula ta isa wata tashar jiragen ruwa da ke arewacin kasar daga birnin Manam, babban birnin kasar cikin wani jirgin ruwa. An fara bai wa juna wannan wutar yula a wannan kasa. Dubban mutanen kasar suna maraba da ita da hannu biyu biyu. Wannan wutar yula ta fara tafiyarta daga birnin Doha tun daga ran 10 ga watan Oktoba, ta ratsa kasashe da yankuna 15 na Asiya, nisan tafiyarta ya kai kilomita fiye da 50,000, wanda ya fi tsawo a cikin tarihin taron wasannin motsa jiki na Asiya.(Tasallah)