Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, za ta ba da kyautar kayayyakin da ake amfani da su wajen kayyade haihuwa da kula da lafiyar haihuwa wadanda darajarsu ta kai kudin Sin yuan miliyan 10 ga kasashen da ke cikin kungiyar abokai masu hadin gwiwa kan yawan jama'a da raya kasa, kuma za ta ba da taimakonta ga kasashen a fannonin horaswa da kuma yin musanyar fasaha.
Don sa kaimi ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa a fannin yawan jama'a da raya kasa, wasu kasashe ne suka kafa wannan kungiya ta abokan hadin gwiwa kan yawan jama'a da raya kasa a shekara ta 1994. Ya zuwa yanzu, akwai kasashe 21 a cikin kungiyar, wadanda yawan jama'arsu sun dau fiye da rabi na jama'ar duk duniya.
Tun bayan da kasar Sin ta shiga kungiyar a shekara ta 1997, tana kokarin ingiza mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa a fannin yawan jama'a da raya kasa, a wajen horaswa ne kawai ta horar da ma'aikata kusa dubu wadanda ke kula da harkokin lafiyar haihuwa da kayyade haihuwa da ba da taimakon fasaha a wannan fanni ga kasashen da abin ya shafa. A gun taron shekara shekara da kungiyar ta shirya a kwanan baya a nan birnin Beijing, kasar Sin ta kuma yi alkawarin ba da sabbin taimako a jere ga sauran kasashen kungiyar nan da shekaru biyar masu zuwa.
Shugaban kwamitin kula da yawan jama'a da tsarin iyali na kasar Sin, Mr.Zhang Weiqing ya ce, nan da shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta shirya wa kasashen kungiyar kwasa kwasai guda biyu a ko wace shekara dangane da yawan jama'a da raya kasa, kuma za ta ba su kyautar kayayyakin da ake amfani da shi wajen kula da lafiyar haihuwa wadanda darajarsu za ta kai kudin Sin yuan miliyan 10.Ya ce, 'Ko da yake taimakon da kasar Sin ta bai wa kasashen kungiyar kadan ne, amma muna bayar da taimakonmu cikin sahihanci kuma ba tare da ko wane sharadi na siyasa ba. Muna son hada gwiwarmu da kasashen kungiyar abokan hadin gwiwa kan yawan jama'a da raya kasa, don neman mayar da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen kungiyar a fannin yawan jama'a da bunkasuwa a matsayin kyakkyawan misali na hadin gwiwar kasashe masu tasowa.'
Alkawarin da kasar Sin ta dauka ya kuma sami yabo daga kungiyoyin duniya, ciki har da asusun kula da yawan jama'a na MDD da kungiyar tsarin iyali ta duniya, wadanda suka halarci taron. Shugabar kungiyar ciniki da masana'antu ta kungiyar tarayyar kasashen Afirka, Madam Elizabeth Tunku ta ce, yawancin mambobin kungiyar abokan hadin gwiwa kan yawan jama'a da raya kasa kasashen Afirka ne, kuma suna godiya ga taimakon da gwamnatin kasar Sin ta ba su a fannin yawan jama'a da hadin gwiwa. Ta ce,'ina son yin amfani da wannan dama, in nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da jama'arta, don yi musu godiya a kan jerin matakan da suka dauka a wajen aiwatar da shirin yawan jama'a da raya kasa na Sin da na Afirka, kokarin na da muhimmanci.'
Ban da wannan, wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Mr,Hua Jianmin ya kuma yi kira ta musamman ga kasashe daban daban da su inganta shawarwari da hadin gwiwa a fannin yawan jama'a da raya kasa, kuma a kara ba da taimako ga kasashe masu tasowa. Ya ce,'Ya kamata kasashe daban daban su dauki hakikanan matakai, don kara tura albarkatun raya kasa zuwa kasashe masu tasowa. kasar Sin tana fatan kasashe daban daban za su cika alkawaransu kamar yadda ya kamata, a mai da hankali a kan taimaka wa kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka, ta yadda zuwa shekara ta 2015, za su cimma burin tabbatar da kowa na iya jin dadin ingancin lafiyar haihuwa da kuma tabbatar da manufar bunkasuwa na shekaru dubu cikin lokaci'
|