Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-28 18:29:41    
Sanarwa

cri

Jama'a masu karatu, yanzu ga wata muhimmiyar sanarwa game da wata gasar kacici-kacici ta samun kyautattuka watakila ba ku san lardin Sichuan na kasar Sin sosai ba, amma idan an ambaci Panda, to, kowa ya kan nuna babbar sha'awa ga irin wannan kyakkyawar dabba. Garinta yana lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.

Jama'a masu karatu, idan kuna son ku kara saninku kan Sichuan a fannoni daban daban, ku san wuraren shakatawa masu kyau, to, sai ku saurari shirye-shiryenmu na musamman. Gidan rediyon kasar Sin zai watsa muku shirye-shiryen musamman mai lakabi haka 'Garin Panda---lardin Sichuan' tun daga ran 28 ga watan Nuwamba ta hanyoyin rediyo da kuma internet, sa'an nan kuma, zai gabatar da gasar kacici-kacici ta jarrabawa ilmin yawon shakatawa a lardin Sichuan. Muna maraba da shigarku cikin wannan gasa da hannu biyu biyu.

Kamar yadda muka yi a da, a karshen ko wane shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin da mu kan gabatar muku a ko wane ranar Talata, za mu yi muku tambayoyi 2, sai ku amsa wadannan tamboyoyi a kan wasikun da muka aika muku. Za mu kammala karbar wasikunku a ran 15 ga watan Afril na shekarar 2007, bisa agogon wurin. Za mu zabi mutanen da za su zama na daya dana biyu da na uku da kuma wadanda za su samu yabo na musamman daga cikin wadanda suka amsa tambayoyin.

To, jama'a masu karatu, muna fatan za ku sami maki mai kyau.