Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-28 17:30:43    
Cin dafaffen Karas zai ba da taimako wajen samun abubuwa masu gina jiki

cri

Mutane da yawa suna son cin karas ba tare da an dafa shi ba, kuma ana ganin cewa, idan aka dafa karas, to za a iya lalata abubuwa masu gina jiki da ke cikinsa. Wani karamin nazarin da aka gudanar a kasar Japan ya bayyana cewa, idan mutane suna cin karas bayan da aka dafa shi, ya fi amfani ga jikinsu wajen samar da abubuwan gina lafiyar jiki da ake kiransa carotene iri na?da ke cikin karas.

Bisa labarin da muka samu daga wata tashar Internet ta kasar Japan, an ce manazarta na cibiyar nazari ta tsakiya ta Itouen ta kasar Japan da sauran hukumomin nazari sun gudanar da bincike a kan maza takwas a kan samun abin gina lafiyar jiki na carotene iri na? bayan da suka ci dafaffen karas da kuma karas din da ba a dafa ba. Dukkan wadannan mutane da aka yi nazari a kansu shekarunsu ya kai 24 zuwa 41 da haihuwa, an ba wasu daga cikinsu karas wanda ba a dafa ba giram 200, kuma an ba sauran mutane dafaffen karas giram 200.

Daga baya kuma sakamakon nazarin ya nuna cewa, bayan awoyi shida, yawan abin gina lafiya da jiki na carotane iri na?da ke cikin jinin masu cin dafaffen karas ya yi ninki 1.4 na masu cin karas ba tare da dafa shi ba. Haka kuma bayan awoyi takwas, wannan jimla ta karu zuwa 1.6.

Haka kuma a cikin wani nazari daban, manazarta sun sa mutanen da aka yi musu nazari su tsaya kan shan ruwan 'ya'yan itace da aka yi tare da dafaffen karas. Kuma bayan makwanni takwas, an gano cewa, fadin splash da ke fatunsu ya ragu.

Abin gina lafiyar jiki na carotene iri na?yana da amfanin kare fatun mutane daga illar da sinadarin hasken ultraviolet ya ke yi ga fatar mutane. Manazarta sun bayyana cewa, idan lokacin zafi ya yi, cin karas yadda ya kamata ya fi muhimmanci ga lafiyar jikin mutane.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan talebijin na zamani. Kasashe 101 na Turai da Afirka da kuma gabas ta tsakiya suna cikin shirin kawar da talebijin irin na zamanin da da kuma fara yin amfani da talebijin na zamani wato digital talebijin kafin shekara ta 2015, kuma shirin da kasar Sin ke yi wajen habaka talebijin na zamani ya yi daidai da na wadannan kasashe. A hakaki dai, ya zuwa yanzu, mutane masu yin amfani da talebijin na zamani fiye da miliyan hudu suna more shirye-shirye masu kyau da talebijin zamani ya kawo musu. Suna iya zabar shirye-shiryen talebijin da suke so da sayon abubuwa da yin ragistar ganin likita da kuma zuba jari a kasuwannin hada-hadar kudi ta yin amfani da talebijin zamani. To yanzu bari mu yi muku cikakken bayani kan yadda talebijin zamani ya kyautata zaman fararren hula na kasar Sin.(Kande)