Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-28 17:26:37    
Dutse na Siguniangshan

cri

Da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan tsaunuka na Siguniangshan, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, ziyarar Aljannar da ke duniyarmu---kai ziyara ga kwarin Jiuzhaigou da kuma wurin shakatawa na Huanglong.

Tsaunukan Siguniangshan mai tsayin mita 6,250 suna cikin gundumar Xiaojin ta shiyyar kabilun Zang da Qiang ta Aba mai cin gashin kanta da ke yammacin lardin Sichuan na kasar Sin, yana da nisan kilomita misalin 220 daga birnin Chengdu. Idan an hango su daga nisa, wadannan tsaunuka sun yi kama da kyawawan 'yammata 4 'yan kabilar Zang, wadanda suka sa 'yan kwali a kansu. Saboda haka ana kiran wadannan tsaunuka da suna 'Siguniang', wato dutse na 'yammata 4.

Akwai wata almara game da asalin wadannan tsaunuka. A can can can da, wani abun bauta da ke kan tsauni wai shi Balang yana da 'ya'ya mata 4. wadannan 'yammata 4 suna da kyan gani sosai, kuma karamar daga cikinsu ta fi tsayi, kuma ta fi kyan gani. Wani shaidan ya yi sha'awar wadannan 'yammata 4, yana son ya aure su duka. Shi ya sa ya shawarci Balang da su yi fada a tsakaninsu, idan ya ci nasara, zai auri dukan 'yammata 4. Abin bakin ciki shi ne a karshe dai shaidan ya kashe Balang. Wadannan 'yammata 4 sun gudu, sun mutu saboda sanyi. Gawawwakinsu sun zama tsaunuka na Siguniangshan, kuma gawar babbansu Balang ta zama dutsen Balangshan.

Amma a wani labarin kuma, an ce, wani mafarauci ya ceci wadannan 'yammata 4 daga bisani, inda suka zama abubuwan bauta. Siffar tsaunukan Siguniangshan ta yi kama da wadannan abubuwan bauta mata 4, wadanda suka sa fararen tufafi, kuma sun kada hannu ga bakin da suka zo daga wuraren nisa.

Kankara mai taushi ta rufe kan tsaunukan Siguniangshan a duk shekara. A karkashin sararin sama mai launin shudi da fararen gajimare, furanni iri daban daban da koren ciyayi da ganyaye masu launi zinariya da babban hazo da farar kankara mai taushi da kuma kankarar da ta yi kama da daimun sun lullube bakaken duwatsu da koguna masu tsabta.

Ban da tsaunukan Siguniangshan kuma, masu yawon shakatawa su kan ziyaraci kwaruruwan Shuangqiao da Changping da Haizi a nan.(Tasallah)