Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-27 16:10:11    
Takaitaccen bayani game da kabilar Mongoliya ta kasar Sin

cri

A nan kasar Sin, yawancin mutanen kabilar Mongoliya suna zama a jihar kabilar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta da jihar Xinjiang da shiyyoyi da gundummomin kabilar Mongoliya masu cin gashin kansu na lardunan Qinghai da na Gansu da na Helongjiang da Jilin da na Liaoning. Wasu suna zama a sauran wuraren da ke duk fadin kasar Sin. Bisa kiddidigar da aka yi a shekara ta 2000, yawan mutanen kabilar Mongoliya a nan kasar Sin ya kai fiye da miliyan 5 da dubu dari 8, kuma suna da yare da kalmomin kabilar Mongoliya.

Yau da shekaru aru aru da suka wuce, mutanen kabilar Mongoliya sun yi zama a yankunan da ke bakin kogin Wangjian, wato kogin Erguna. An kuma kafa wata karamar kasar kabilar Mongoliya. Amma bayan aka rasa wannan karamar kasa a shekarar 840, yawancin mutanen wannan kabila sun kaura zuwa yankunan yammacin kasar Sin. Sannu a hankali ne sun hada da sauran kabilu wadanda suke magana da yaren Tukikstan kuma suke zama a tudun Mongoliya.

A shekerar 1206, a gun wani babban taron kabilar Mongoliya, an zabi Tie Muzheng da ya zama sarkin sabuwar kasar kabilar Mongoliya. An kuma ba shi suna mai martaba sarki Chengjisihan. Kafuwar kasar kabilar Mongoliya tana da muhimmanci sosai ga bullowar cikakkiyar kabilar Mongoliya. Tun wancan lokaci, a karo na farko ne kabilar Mongoliya wadda take da karfi kuma cikin halin zaman lafiya ta bulla a arewancin kasar Sin. An kira dukkan mutanen da suke zama a yankunan da ke karkashin mulkin sarki Chengjisihan mutanen kabilar Mongoliya. Ya zuwa shekarar 1260, mutanen kabilar Mongoliya sun ta da yake-yake har sau da yawa sun dinka duk kasar Sin, kuma sun kafa daular Yuan a kasar Sin. Daular Yuan ta bayar da gudummawa sosai wajen tabbatar da iyakar yankunan kasar Sin ta yanzu. Amma a shekarar 1368, an soke daular Yuan. Mutanen kabilar sun koma filayen ciyayi kuma sun ci gaba da sana'arsu ta kiwon dabbobi.

Mutanen kabilar Mongoliya suna bin addinin Lama. Wannan addini ya yi tasiri sosai ga al'adun kabilar Mongoliya. Domin an shigar da addinin Lama a yankunan kabilar Mongoliya daga yankunan kabilar Tibet. Al'adun kabilar Tibet ma sun yi tasiri sosai ga al'adun kabilar Mongoliya.

A da, yawancin mutanen kabilar sun yi sana'ar kiwo da ta farauta. Amma yanzu, ba ma kawai suna ci gaba da bin wannan sana'a ba, hatta ma suna yin sauran sana'o'i da yawa. Mutanen kabilar Mongoliya sun bayar da gudummawa sosai ga bunkasuwar tattalin arzikin duk kasar Sin.

Bugu da kari kuma, mutanen kabilar Mongoliya suna mai da hankali sosai wajen neman ilmi. Sannanun kwararru da shehun malamai da yawa na kasar Sin mutane ne na kabilar Mongoliya.(Sanusi Chen)