Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-24 21:48:24    
Yankunan kudu maso yammacin Sin wurare ne da 'yan kasuwa Sinawa na kungiyar ASEAN ke sha'awar zuba musu jari ainun

cri

Tun daga shekarun 1970, kasar Sin tana ta shigo da kudin jari daga wajen Sinawa 'yan kasuwa na kungiyar tarayyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, kuma sun ba da babban taimako wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin.

Duk fadin wurare na kudu maso yammacin kasar Sin ya wuce muraba'in kilomita miliyan 2.5, yawan mutanensu kuma ya kai kimanin miliyan 250. Wuraren sun hada da lardunan Sichuan da Yunnan, da jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai ikon aiwatar da harkokin kanta, da birnin Zhongqing da ke karkashin shugabancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye da sauransu. Wuraren nan wurare ne masu albarkar makamashin masana'antu da albarkatun kasa. Amma da ya ke abubuwa da suka faru a tarihi, wuraren suna baya-baya, idan an kwatanta su da sauran wuraren kasar Sin da ke a bakin teku. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ba ma kawai gwamnatin kasar Sin ta samar da makudan kudade ga wuraren nan don gaggauta bunkasa harkokin tattalin arzikinsu ba, har ma ta nuna goyon baya ga wuraren da su jawo kudaden jari daga wajen 'yan kasuwa na kasashen waje, musamman na kasashen kungiyar ASEAN.

Madam Li Haifeng, mataimakiyar shugabar ofishin majalisar gudanarwa ta kasar Sin mai kula da harkokin Sinawa da ke zama a kasashen waje ta bayyana cewa, "a cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da manufofin gatanci da dama, ta kara ba da taimakonta don raya wurare da ke kudu maso yammacin kasar da bude wa kasashen waje kofarsu. Hukumomin wuraren nan su ma sun yi ta kara kashe makudan kudade wajen yin manyan ayyuka, don kyautata guraben zuba jari. Ta haka yawan ayyuka da 'yan kasuwa Sinawa na kungiyar ASEAN ke zuba musu jari, yana ta karuwa a ko wace shekara. Haka kuma yawan kudin jari da suke zubawa ma ya karu sosai. Yanzu 'yan kasuwa Sinawa da ke zaune a kasashen waje sun riga sun zama wani babban rukuni da ke raya wuraren kudu maso yammacin kasar Sin."

A kwanakin baya ba da dadewa ba, a birnin Kunming, fadar gwamnatin lardin Yunnan da ke a kudu maso yammacin kasar Sin, an yi taro na karo na hudu a kan ayyuka da aka gabatar wa 'yan kasuwa Sinawa na kungiyar ASEAN don zuba musu jari a wuraren kudu maso yammacin kasar Sin. Wakilan 'yan kasuwa Sinawa sama da 180 wadanda suka fito daga kasashen kungiyar ASEAN da wakilan masana'antun jihohi 6 na wuraren kudu maso yammacin kasar Sin sun halarci wannan gagarumin taro. Malam Qin Guangrong, mataimakin gwamnan lardin Yunnan da ya shirya wannan taro ya bayyana cewa, "taron ya bayar da dama ga lardin Yunnan, wajen kara bude wa kasashen waje kofa, da gaggauta bunkasuwa, da mayar da shi da ya zama babban iyalin 'yan kasuwa Sinawa na nahiyar Asiya da yankin tekun Pacific. Mun hakake, ta hanyar yin wannan taro tare da nasara, tabbas ne, lardin Yunnan zai ba da taimakonsa wajen inganta hadin kan Asiya da yankin tekun Pacific da kara yin ma'amalarsu."

'Yan kasuwa Sinawa da yawa suna nuna himma sosai wajen zuba jari a wuraren nan. Cikin nuna kishin kasa, suna kokari sosai wajen ba da taimakonsu don bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar Sin. Da Malam Gao Xinping, dan kasuwa Basine na kasar Singapore ya tabo magana a kan ra'ayinsa kan zuba jari a wuraren nan na kasar Sin, sai ya ce, "tun wancan lokaci, na taba zuba jari a babban yankin kasar Sin, kuma na dade ina zuba jari a kasar, amma ina zuba jari ne musamman a lardunan Fujian da Jiangsu da birnin Shanghai da sauran wurare da ke bakin teku. Yanzu, na sami damar zuwa wuraren kudu maso yammacin kasar a wannan gami. Mu 'yan kasuwa Sinawa muna fatan za a raya kasar Sin da ta zama wata kasa mai kasaita. "

Sinawa da ke zaune a kasashe daban daban na duniya sun zarce miliyan goma, suna ba da babban taimakonsu wajen bunkasa tattalin arziki da zaman jama'a na kasashe da suke zaune, sa'an nan kuma suna ba da babban taimakonsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin. (Halilu)