Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-24 21:28:32    
'Yan wasan harbe-harben kasar Sin suna himmantuwa wajen shirin shiga taron wasannin Olympics na Beijing

cri

A cikin shirinmu na baya dai, mun karanta muku wassu gajerun labarai na wasannin motsa jiki. Yanzu kuma za mu karanta muku wani bayani mai ban sha'awa game da wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008.

Aminai masu sauraro, kuna sane da, cewa za a yi taron wasannin motsa jiki na 29 a shekarar 2008 a birnin Beijing da kuma sauran biranen kasar Sin. Yanzu 'yan wasa na ayyukan wasanni iri daban daban suna nan suna huimmantuwa wajen horaswa don shiga taron wasannin. To, a cikin shirinmu na yau, za mu dan gutsura muku wani bayani game da yadda ' yan wasan harbe-harbe na kasar Sin suke shirin shiga taron wasannin Olympics cikin himma a kwazo.

Saboda akan kayyade yawan kungiyoyin wasanni da kuma 'yan wasa dake shiga taron wasannin motsa jiki na Olympics, don haka akan gudanar da gasannin samun iznin shiga taron wasannin a tsakanin ayyukan wasanni iri daban daban cikin shekaru hudu kafin a shirya taron wasannin Olympics, ta yadda za a tabbatar da yawan kujerun da kungiyoyi mahalartan taron wasannin za su samu a karshe.

Ana tune da, cewa a gun taron wasannin motsa jiki na Olympics na shekarar 2000, kungiyar harbe-harbe ta kasar Sin ta samu kujeru 26 na shiga gasannin wasan harbe-harbe ta kuma samu lambobin zinariya guda uku a karshe. Ban da wannan kuma, bayan shekaru hudu, a Aden na kasar Girka, ' yan wasa 26 na kasar Sin sun shiga gasa kamar yadda suka yi a wancan gami, inda suka samu lambobin zinariya guda hudu a karshe. Bayan taron wasannin Olympics na Aden, kwamitin wasannin Oympics na kasa da kasa ya yanke shawarar rage ayyukan wasanni guda biyu, wato ke nan yawan tikitocin shiga gasar wasannin harbe-harbe ya ragu zuwa 28 daga 31 na da. Sakamakon haka, tun daga farkon shekarar bara, 'yan wasan harbe-harbe na kasar Sin ta kama hanyar neman samun tikitocin shiga taron wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008.

Kwanakin baya ba da dadewa ba, , 'yan wasan harbe-harbe na kasar Sin suna nan sun nuna himma da kwazo wajen yin horaswa domin halartar gasar cin kofin duniya ta 49 ta wasan harbe-harbe da ake yi a birnin Zagreb, hedkwatar kasar Croatia. Gasar nan, gasa ce ta karshe a wannan shekara wadda ake iya samun tikitocin shiga gasar wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing daga wajenta.

Babban mai koyar da 'yan wasan harbe-harbe na kasar Sin Mr. Wang Yifu ya furta, cewa muhimmin makasudin shiga gasar cin kofin duniya, shi ne domin neman samun tikitocin shiga gasar wasannin Olympics na Beijing a shekarar 2008.

Kawo yanzu, kungiyar wasan harbe-harbe ta kasar Sin ta rigaya ta samu kujeru 23 a gasar wasannin Olympics, wato sauran kujeru 5 ke nan da suka rage da kungiyar kasar Sin za ta yi namijin kokarin samunsu idan tana so ta kwashi dukkan tikitocin shiga irin wannan gasa.

A shekarar bara, kungiyar wasan harbe-harbe ta kasar Sin ta samu tikitoci 8 na shiga wasannin Olympics, lallai ta yi rawar gani idan an kwatanta ta da sauran kungiyoyin wasan harbe-harbe na kasashe daban daban. Kuma tun daga farkon shekarar 2006 har zuwa yanzu kungiyar kasar Sin ta fi nuna gwaninta wajen yin wasan harbe-harbe. Alal misali : a gun gasar zango-zango ta cin kofin duniya da aka yi a birnin Guangzhou na kasar Sin a farkon wannan shekara, shahararriyar 'yar wasa mai suna Ren Jie ta kasar Sin ta samu lambar zinariya yayin da ta samu kujera ta farko a gun wasannin Olympics na Beijing a fannin wasan harbe-harben bindiga na mata. Miss. Ren Jie ta fada wa wakilinmu, cewa ta yi farin ciki matuka da samun wannan kujerar shiga wasannin Olympics na Beijing.

Ko da yake ana gudanar da yunkurin shirin shiga wasannin Olympics da kungiyar wasan harbe-harbe ta kasar Sin take yi lami-lafiya, amma duk da haka, kawo yanzu dai babu wata kungiyar wasan harbe-harbe da ta kwashi dukkan tikitocin shiga gasar wasannin Olympics. Mr. Wang Yifu ya ce, 'yan wasan kasar Sin za su yi kokari gwargwadon iyawa wajen cimma babban burinta. Ya kuma kara da, cewa jami'an sashen kula da harkokin wasan harbe-harbe ba su matsa musu lamba ba wajen samun kujerun shiga wasannin Olympics, amma ko 'yan wasa ko masu koyar da su dukkansu sun ce za su sanya matukar kokari wajen cimma wannan kyakkyawar manufa.

To, madalla jama'a masu sauraronmu, kun dai saurari shirinmu mai ban sha'awa na ' Wasannin Olympics na Beijing' dangane da yadda ' yan wasan harbe-harbe na kasar Sin suke yin namijin kokari wajen horaswa domin shiga taron wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a nan Beijing a shekarar 2008. To, shirin ' Wasannin Olympics na Beijing' da za mu iya kawo muku ke nan a yau daga nan Sashen Hausa na Rediyon kasar Sin. Ni Sani Wang ne ya shirya kuma ya karanta muku. Da haka, muke muku sallama tare da fatan alhari. Sai makon gobe war haka, ku zama lafiya. ( Sani Wang )