Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato shirinmu na "Me Ka Sani Game da Kasar Sin ". A cikin shirinmu na yau za mu karanta muku wani bayani mai lakabin haka: Hukumomi da Cibiyoyi masu kula da harkokin Afrika na kasar Sin .
A cikin wannan Bayyanin kan Hukumomi da Cibiyoyi masu kula da harkokin Afrika na kasar Sin , za mu bayyana muku Sashen harkokin Afrika na Ma'aikatar Harkokin waje ta kasar Sin da Sashen al'amuran harkokin Afrika na Cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta Kasar Sin da Cibiyar nazarin al'amuran Kasashen Afrika ta Jami'ar Beijing ta kasar Sin.
Da farko dai bari mu tabo magana kan daya daga cikin wadannan hukumomin da cibiyoyin . Sashen harkokin Afrika na Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin yana nazari da kula da al'amuran kasashen dake kudancin Sahara . Wannan sashen yana kula da ma'amala da harkokin diflomasiya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika . Kuma ya tsara manufofin harkokin waje na kasar Sin kan wadannan kasashen Afrika . Bugu da kari kuma wannan sashen yana kula da harkokin sulhunta al'amuran bangarori biyu na wannan babban yanki da kasashen . Aiki na karshe na wannan Sashen shi ne yana jagorancin ayyukan diplomasiya na Ofsoshin jakadanci da Ofsoshin kananan jakadu wato consulate na kasar Sin dake kasashen Afrika daban daban . abin da kuka saurara dazu nan shi ne Sashen harkokinn Afrika na Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin . Yanzu bari mu yi 'dan bayani kan shugabannin wannan Sashen . Madam Xu Jinghu ta zama shugabar Sashen Afrika . Mataimakanta su ne Li Qiangmin da Gu Xiaojie da Cao Zhongming , dukanninsu maza ne .
A ran 4 ga watan Yuli na shekarar 1961 an kafa Sashen nazarin al'amuran Afrika na Cibiyar nazarin kimiyyar zaman al'umma ta kasar Sin bisa nakalin da Mao Zedong , marigayin
shugaban kasar Sin ya yi . A farkon lokacin da aka kafa wannan sashen , Zhang Tiesheng , shahararren masani mai nazarin al'amuran duniya ya zama shugaba na farko na wannan sashen . A shekarar 1964 ? Wu Xueqian tsohon ministan harkokin waje kuma tsohon mataimakin shugaban Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya zama shugaban wannan sashen . Tun daga shekarar 1966 zuwa shekarar 1974 , Sashen Afrika ya daina harkokinsa Tun daga shekarar 1975 zuwa shekarar 1977 an farfado da wasu ayyukansa . A shekarar 1978 an farfado da dukannin ayyukansa a hukunce , kuma Liao Gailong shahararren 'dan siyasa ya zama shugaban wannan sashe . Tun daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1992 , Madam Ge Jie ta zama shugabar Sashen . Tun daga shekarar 1993 zuwa shekarar 1998 , Malam Zhao Guozhong ya zama shugaban wannan sashen . Shugaban Sashen na yanzu shi ne Frofesa Yang Guang .
|