Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-23 15:41:27    
Wani sabon yunkurin harkokin waje da Iran ke yi kan matsalar nukiliya

cri

Matsalar nukiliya ta Iran kullum ta zama wata muhimmiyar matsala ce da ke jawo hankulan kasashen duniya. Kwanan baya, bisa matsayinta na mai taka muhimmiyar rawa kan matsalar Iran, ita kasar Iran kuma ta kara daukar wasu matakai masu jawo hankulan mutane wajen harkokin waje.

Matakin farko da Iran ta dauka shi ne, ta roki hukumar makamashin nukiliya ta kasashen duniya da ta gabatar mata da gudummawa wajen fasaha domin samar da na'urar sarrafa makaman nukiliya. An ce, yanzu wannan hukuma ta yarda da nuna mata goyon baya wajen fasaha domin samar da na'urar sarrafa nukiliya da ake kira Light-water nucler reactor kawai, amma ba ta yarda da nuna mata goyon baya wajen fasaha domin samar da na'urar sarrafa nukiliya ta heavy-wata ba, sabo da mai yiwuwa ne za a iya yin amfani da irin wannan na'ura domin sha'anin soja.

Kowa ya sani, kasar Iran kullum tana jaddada magana cewa, shirinta na bunkasa makamashin nukiliya ba don kome ba illa domin manufar shimfida zaman lafiya, ba ta da nufin yin bincike da kera makaman nukiliya ko kusa.

Mataki na 2 da Iran ta dauka wajen harkokin waje shi ne, lokacin da shugaba Mahmoud ahmadinejad na kasar yake yin shawarwari da Choe Thae Bok, shugaban majalisar koli ta jama'ar Korea ta arewa wanda yake halartar taron Asiya da aka yi a ran 18 ga wata, ya yi kira ga Korea ta arewa da ta yi watsi da ayyukan makaman nukiliya da take yi, kuma ya tsaya kan ra'ayinsa cewa, ya kamata a kawar da makaman nukiliya daga yankin teku na Korea. Ra'ayoyin jama'a sun bayyana cewa, aikin nan da Mahmoud Ahmadinejad yake yi makasudinsa shi ne domin nuna ra'ayoyinsa 2 ga kasashen duniya, na farko shi ne, babu hadin gwiwa da amincewa juna a tsakanin Iran da Korea ta arewa kan matsalar nukiliya. Na 2 kuma shi ne, ayyukan nukiliya da Iran ke yi makasudinta shi ne domin yin amfani da makamashin nukiliya cikin lumana, wato a hakika ta sha bamban da Korea ta arewa kan wannan matsala.

Mataki na 3 da Iran ta dauka kuma shi ne dogara da matsalar Iraq don jan ragamar kasar Amurka, ta yadda Amurka za ta kasa karfin matsa mata lamba kan matsalar nukiliya. Iran tana gani cewa, yanzu matsalar Iraq ta zama kadagaren bakin tulu. Wani muhimmin dalilin da ya sa Jam'iyyar Republic ta Amurka ta sha kaye a zaben shugaban kasa na lokacin tsakiya shi ne, matukar hasalar da jama'ar kasar ke nuna wa gwamnatin Bush sabo da manufar da take gudanarwa kan kasar Iraq. Bisa matsin majalisar dokokin kasa wadda Jam'iyyar Democratic ke yi mata ginshiki, mai yiwuwa ne za a daidaita wannan manufa. Daga wani fanni daban kuma, kwanan baya Mr. Tony Blair, firayim ministan kasar Ingila ya fito fili ya yi kira ga kasar Iran da Syria da su shiga ayyukan daidaita matsalar tsaro na kasar Iraq. Duk wadannan sun bayyana cewa, Iran tana fuskantar wani irin zarafi mai kyau.

Ra'ayoyin jama'a na Turai sun bayyana cewa, sabo da Iran ba ta cika bukatar da aka tanada cikin kuduri mai lamba 1696 na kwamitin sulhu na M.D.D.ba, wato ta daina shirin tace sinadarin Uranium kafin ran 31 ga watan Agustan, shi ya sa wani sa'i ta taba samun kanta cikin halin saibanci, kila za a sanya mata takunkumi. Amma da akwai alamomi iri daban-daban sun bayyana cewa, bayan da kasar Iran ta dauki jerin matakai kan matsalar nukiliya, kuma ta yi kokari wajen harkokin waje, ta riga ta juya matsayinta daga tsaron kai zuwa bugun gaba a hannu, wato ta sake kama matsayin daidaita matsala cikin ganin damarta. Matsalar nukiliya ta Iran ta kara samun mafita mai haske. (Umaru)