Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 65 da kafa rediyon kasar Sin, wato CRI, kuma idan ba ku manta ba, don taya murnar al'amarin, a watan Mayu na shekarar da muke ciki, mun gabatar da wata gasar kacici-kacici dangane da 'Ni da CRI' a tsakanin masu sauraronmu. Ga shi a karshen watan Satumba da ya wuce, mun riga mun kawo karshen gasar, kuma muna farin ciki sabo da akwai masu sauraronmu da dama da suka nuna kwazo kuma suka fice a cikin gasar. Amma kafin mu bayyana muku sunayen wadanda suka ci nasara, bari mu dan maimaita gasar tukuna.
Da farko dai, ga tambayoyinmu a gasar. A cikin gasar, mun ba ku tambayoyi shida gaba daya, wato su ne, yaya ake kiran gidan rediyon kasar Sin a da, wato a wajen watan Afrilu na shekara ta 1950? yanzu kasashe nawa ne rediyon kasar Sin ke da wakilai? Sa'an nan, yanzu cikin harsuna nawa ne gidan rediyon kasar Sin ke watsa shirye-shiryensa ga masu sauraro na kasashen duniya? A wace kasa ce gidan rediyon kasar Sin ya kafa tashar rediyo na FM na farko? Mene ne sunan tashar internet ta gidan rediyon kasar Sin? A shekarar 2005, yawan wasikun da CRI ya samu daga masu sauraro ya kai nawa? To, yanzu bari mu amsa wadannan tambayoyi bi da bi.
Da ma, wato a shekarar 1950, muna watsa shirye-shiryenmu ga kasashe daban daban ne da sunan 'Radio Peking' sabo da haka, game da yaya ake kiran gidan rediyon kasar Sin a shekara ta 1950, amsa ita ce Radio Peking..
A kan tambayar nan ta kasashe nawa ne Gidan Rediyon kasar Sin ke da wakilansa, ya zuwa yanzu, gidan rediyon kasar Sin ya riga ya kafa tasoshin wakilansa a kasashen waje 27. Tun daga shekarar 1980, gidan rediyon kasar Sin ya fara kafa tasoshin wakilansa a kasashen waje a kai a kai. Da farko dai an kafa wani ofishin wakilansa a birnin Tokyo na kasar Japan da wani daban a birnin Belgrade na tsohuwar Tarayyar Jamhuriyar Yugoslavia. Su wadannan wakilanmu suna aiko mana da rahotanni dangane da muhimman al'amuran da ke faruwa a duk fadin duniya zuwa hedkwatar rediyonmu cikin lokaci.
Sannan kuma, yanzu gidan rediyon kasar Sin yana watsa shirye-shiryensa da harsuna 48 a kowace rana. Sakamakon haka, harsunan da gidan rediyon kasar Sin ke amfani da su yana kan gaba a tsakanin gidajen rediyon kasashen duniya 3 mafi girma.
Sai kuma ga tambayarmu ta hudu, wato a wace kasa ce Gidan Rediyon kasar Sin ya kafa tashar Rediyo na FM ta farko? Ranar 27 ga watan Fabrairu na shekara ta 2006, wata muhimmiyar rana ce a tarihin rediyon kasar Sin. A wannan rana, a birnin Nairobi na kasar Kenya, gidan rediyon FM a kan zango 91.9 da gidan rediyon kasar Sin ya kafa wanda kuma ya kasance gidan rediyo na FM na farko da gidan rediyon kasar Sin ya kafa a ketare, ya fara aiki.
Gidan rediyon kasar Sin yana mai da hankali sosai a kan raya shafinsa na Internet. Yanzu, idan ka shiga shafin Internet namu, wato CRI Online, za ka iya samun shirye-shiryenmu iri iri, kuma mutane fiye da miliyan 8 daga duk fadin duniya suna shiga shafinmu na Internet na gidan rediyon kasar Sin a kowace rana. Amma kada ku manta, sunan shafinmu na Internet shi ne 'CRI Online'.
Ga kuma tambaya ta karshe, wato a shekara ta 2005, yawan wasikun da CRI ya samu daga masu sauraro ya kai nawa? Masu sauraro na rediyon kasar Sin ya yi ta karuwa a cikin shekaru 65 da suka wuce bayan da aka kafa rediyon din. Yawan wasikun da muka samu ya karu har ya wuce miliyan 2 da dubu 170 a shekarar 2005. A sakamakon ci gaba da aka samu a cikin shekaru 65 da suka gabata, masu sauraronmu sun riga sun game ko ina cikin duniya. Kulob-kulob din masu sauraronmu ma sun yi ta karuwa. Yanzu, yawansu ya riga ya kai 3,600, kuma mu kan shirya bukukuwa masu kayatarwa a tsakaninmu da wadannan kulob-kulob a ko wace shekara.
Ga wadanda suka zo farko a gasar
Bello Abubakar Malam Gero
Wada Riyojin Dan Umma Bayan Rima Radio
P.O.Box 4039 Sokoto
Sokoto State
Nigeria
Mohammed Idi Gargajiga
Government House Street
Jeka Da Fari Quarters
P.O.Box 1444 Gombe
Gombe State
Nigeria
Mustapha Gumal
P.O.Box 9 Gumal
Jigawa State
Nigeria
Hamza Yusuf
P.O.Box 114
Akwanga
Nasarawa State
Nigeria
Wadanda suka zo na biyu su ne
Aisha Ja`afar
P.O.Box 911
Zaria
Kaduna State
Nigeria
Haruna Aminu Yiraso
P.O.Box 41 Numan
Adamawa State
Nigeria
Ikramatu Adam
P.O.Box 2896 Kano
Kano State
Nigeria
Shugaba Ahmadu Jauro Sule
Zumunta Socal Club
Unguwar Makera D Ga`anda Road
P.O.Box 215 Gombi Town
Adamawa State
Nigeria
Aboubakar Ali
P.O.Box 40
Tignere Galim
Adamaoua
Cameroon
Haruna Ibrahim
P.O.Box 249 G.P.O
Dugbe Ibadan
Oyo State
Nigeria
Ejike Chizoba Amaka
No.12 Nnobi Street Uwani
Enugu
Enugu State
Nigeria
Haladu Wakili Lushi
Nitel LTD Southeast Zone
HQS Enugu
PMB 01244 Enugu 400001
Enugu State
Nigeria
Wadanda suka zo na uku su ne
Aliyu Labaran
P.O.Box 5920
Garki 900001
Abuja FCT
Nigeria
Gombawa CRI Listenners Club
Shugaba Yahuza Alhassan
Bank of the North LTD
PMB 26 Gombe
Gombe State
Nigeria
Zainab Bashir
No.8 Temple Street
Lokoja
Kogi State
Nigeria
Aminu Abubakar
P.O.Box 169 Argungu
Tudun Wada Argungu
Kebbi State
Nigeria
GNR Abubakar Nohammed
323 Adar Akure
P.M.B.770 Owena Barracks
Ondo State
Nigeria
Hafsat Alhassan Dantata
P.O.Box 2428 Jos
Plateau State
Nigeria
Nuhu Fari Mai Tumatur Onitsha
No.14 Nnebisi Road
Cable Point Asaba
Delta State
Nigeria
Bunu Bulama Katarko
P.O.Box 95 Damaturu
Yobe State
Nigeria
Umaru A.Bakari Jalingo
P.O.Box 181
Unguwar Majidadi
Jalingo Muri
Taraba State
Nigeria
Mustapha Galadiman Kudu
P.O.Box 1355 Katsina
Katsina State
Nigeria
Bashar Kwana Mariga
P.O.Box 31 Kagara
Niger State
Nigeria
Balarabe Abdu Tela
P.O.Box 2483 Bau
Bauchi State
Nigeria
To, madallah, muna taya wadannan masu sauraronmu murnar cimma nasarar gasar, gaskiya kun yi kokari kun nuna kwazo. Wadanda ba su yi nasara ba kuma, kada ku yi kasa a gwiwa, kun yi kokari, kuma muna fatan za ku kara yin kokari a nan gaba. Muna kuma fatan gasar nan da muka shirya ta taimaka wajen fadakar da masu sauraronmu a kan tarihin rediyonmu da kuma kara dankon zumunci a tsakaninmu da masu sauraronmu. Muna kuma kira ga masu sauraronmu da ku ci gaba da sauraronmu, ku ci gaba da ba mu goyon baya kuma ku ci gaba da shiga gasar kacici-kacici da za mu shirya a nan gaba. (Lubabatu)
|