Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-22 21:24:49    
Wani mai binciken kayayyakin tarihi na Yinxu na kasar Sin Yan Xizhang

cri

A gun wani babban taron nuna kayayyakin tarihi na duniya da aka kira a kasar Lithuania a kwanan baya, an maido da wurin Yinxu na kasar Sin don ya zama wurin al'adu na gargajiya na duniya. Yinxu muhimmin wurin tarihi ne na wayewar kai na zamanin aru aru na kasar Sin, a wurin, an gano kayayyakin tarihi mafiya yawa da suka bayar da mamaki sosai ga duniya.

Rawayen kogi da mafarinsa ya soma daga fadadan tsaunuka na Qinghai-Tibet shi ne kogin asalin mahaifiyar kasar Sin , a wajen tsakiyar rawayen kogi da karshensa, dayake yanayin sararin samaniya na da kyau sosai, shi ya sa wurin ya zama wurin somawar wayewar kai na zamanin aru aru na kasar Sin. Yinxu da ke da fadin murraba'in kilomita 24 shi ne ke zama a wani kauyen da ke karkarar yankin birnin Anyang na lardin Henan da ke tsakiyar rawayen kogi .

Yinxu shi ne wurin tarihi na daular Shang ta kasar Sin , wato hedkwatar daular Shang da ke da tarihi na shekaru dubu uku wadda ta hada da kauyuka fiye da 20. Tun daga karnin da ya gabata har zuwa yanzu, ba sau daya ba ba sau biyu ba masu binciken kayayyakin tarihi na kasar Sin suka taba yin bincike a wurin nan, sun gano wuraren da aka kafa tushen fadar sarki masu girma da yawa da kaburburan sarakuna da na iyalansu da yawansu ya kai dubu ko fiye, kuma an gano kayayyakin tarihi da yawa kamarsu kayayyakin tagulla da rubuce-rubucen da aka saka a kan kasusuwa da kayayyakin da aka kera ta hanyar yin amfani da lu'u-lu'u da tangaram da dai sauransu, wadannan kayayyaki suna da amfani sosai wajen yin bincike kan wayewar kai na zamanin aru aru na kasar Sin.Yang Xizhang mai shekaru 70 da haihuwa yana daya daga cikin shahararrun kwararrun binciken kayayyakin tarihi na Yinxu.

Mr Yan Xizhang ya kammala karatu a shekaru 50 na karnin da ya wuce a sashen koyar da ilmin binciken kayayyakin tarihi na jami'ar Beijing. A shekarar 1958, ya je aiki a cibiyar kimiyya ta zamantakewar al'umma ta kasar Sin, bayan shekaru hudu da suka wuce, an aika Mr Yan Xizhang zuwa gundumar Anyang don yin aikin binciken kayayyakin tarihi, wato aikin binciken Yinxu, kai, ya yi aiki a gundumar cikin shekaru 40 da suka wuce. Mr Yan Xizhang ya gaya wa manema labaru cewa, shugabanni sun aiko da ni zuwa gundumar Anyang don yin aikin bincike kan Yinxu, sai na yi kokarin bincike a kan Yinxu a kai a kai don fadakar da abubuwan Yinxu ga mutane a kai a kai.

A shekarar 1990, bisa jagorancin Mr Yan Xizhang ne, aka soma haka kabari mai lamba 160 da ke kauyen Guojia. Amma ba a yi tsammani cewa, kabarin nan kabari ne na wani babban mutum, kuma an kiyaye shi da kyau, yawan kayayyakin tarihi iri iri da aka hako daga cikinsa ya kai 349, yana daya daga cikin sabbabin kayayyakin tarihi guda goma da aka yi musu bincike a kasar Sin, amma Mr Yan Xizhang ya bayyana cewa, ayyukan haka kananan kaburbura su ma suna da ma'anar gano abubuwan wayewar kai. Ya ce, an iya samun sakamako wajen haka kananan kaburbura , wato an daidaita wasu matsalolin da ba a taba daidaitawa ba wajen binciken wasu kananan kaburbura, daga nan sai mu iya bincike rukunonin iyalai na wancan zamani bisa layi-layi da aka yi ga kaburburan.

Bayar da rahotannin bincike aiki ne mai muhimmanci kuma ba a iya rasa ba. Ya zuwa yanzu, bayan kowane karon haka kaburbura, Mr Yan Xizhang ya iya bayar da rahotanni masu kyau sosai dangane da bincikensa, bisa sakamakon nan ne ya taba bayar da bayyanai dangane da ilmin binciken kayayyaki tarihi da yawa, dukansu sun ba da tasiri mai muhimmanci sosai, saboda haka ya taba samun lambar yabo bisa matsayin farko da ke da kwar jini sosai a rukunonin binciken kayayyakin tarihi a kasar Sin. Ya bayyana cewa, zan sadaukar da duk rayuwata domin binciken Yinxu, musamman ne wajen gano Yinxu da fahimtar da shi da bincike shi, na ba da gudumuwata ta kaina . Na yi aiki bisa tushen aikin da sauran tsofaffin mutane suka yi , sai mutanen da ke bayanmu za su ci gaba da aikin bisa tushen da muka kafa, to za mu sami sakamako mai kyau sosai.(Halima)