Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-22 20:23:15    
A inganta hadin kai don samun makoma mai kyau tare

cri

Ran 22 ga wata da safe, a fadar Kimiyya wato Vigyan Bhawan da ke birnin New Delhi, babban birnin kasar Indiya, shugaba Hu Jintao na kasar Sin da ke ziyarar aiki a kasar ya yi jawabi mai lakabi haka 'a inganta hadin kai don samun makoma mai kyau tare'. Mr. Hu ya nuna cewa, sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da Indiya yana amfana wa bangarorin 2 duka, kuma dukan kasashen Asiya da duniya suna cin gajiya. Dangantakar da ke tsakanin Sin da Indiya ba ta shafe su kawai ba, har ma tana da muhimmanci ga duk duniya.

A cikin babban dakin taro, mutanen rukunoni daban daban na kasar Indiya sun saurari jawabin da Mr. Hu ya yi. Mr. Hu ya bayyana cewa,'Kasashen Sin da Indiya sun mayar da juna tamkar muhimmiyar kasa mai makwabtaka da juna, suna fuskantar ayyukan raya tattalin arziki da daga matsayin zaman rayuwar jama'a, suna kuma bukatar muhallin duniya mai zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma zaman jituwa tare da kasashe masu makwabtaka da su. A matsayinsu na muhimman kasashen duniya, Sin da Indiya suna daukan babban nauyin ingiza zaman lafiya da kwanciyar hankali na nahiyar Asiya da bunkasa nahiyar Asiya bisa wuyansu. A matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa, Sin da Indiya suna da moriya bai daya kan ciyar da duniya gaba domin samar da rukunoni da yawa da daidaita dangantakar da ke tsakanin kasashen duniya ta fuskar dimokuradiyya da sauran manyan al'amuran duniya.'

A cikin jawabin da ya yi, Mr. Hu ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Indiya ta amfana wajen kyautata karfi da matsayin nahiyar Asiya, ta amfana wajen kara karfin kasashe masu tasowa, da amfanawa a fuskar ingiza zaman lafiya da bunkasuwar wannan yanki da duniya, ta kuma amfana wajen samar da dama mai kyau a fannonin zurfafa hadin gwiwa da zumunci a tsakanin Sin da Indiya da kuma tabbatar da moriyar juna da cin nasara tare.

Don kara ingiza hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2 bisa muhimman tsare-tsare, a cikin jawabin da ya yi, Mr. Hu ya gabatar da muhimman shawarwari 5, ya ce,'Da farko ya kamata kasashen Sin da Indiya su karfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da inganta tushen huldar da ke tsakaninsu. Na biyu, ya kamata su kara yin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki, da habaka abubuwa da suke shafar huldarsu. Na uku, ya kamata su kara yin mu'amalar al'adu da ziyarce-ziyarce tsakanin jama'a, da aza harsashi mai karfi na dankon amincin jama'a a tsakanin kasashen 2. Na hudu, ya kamata su kara yin shawarwarin aminci a tsakaninsu, da gaggauta warware batun iyakar kasa tun da wuri. Na biyar, kamata ya yi su inganta hadin kan bangarori da dama, da kuma kare halaliyar moriyar kasashe masu tasowa tare.'

A karshen jawabinsa, shugaba Hu ya yi kira ga kasashen Sin da Indiya da jama'arsu da su hada kansu wajen ciyar da dangantakar abokantaka da hadin gwiwa bisa muhimman tsare-tsare gaba, da ingiza raya duniya mai zaman lafiya da wadatuwa tare da kuma jituwa cikin dogon lokaci don kara samar wa kasashen 2 da kuma jama'arsu makoma mai kyau tare.

Mataimakin shugaban kasar Indiya Bhairon Singh Shekhawat shi ne ya raka shugaba Hu, ya kuma saurari jawabin da Mr. Hu ya yi a fadar kimiyya. Ya yaba wa ziyarar da Mr. Hu yake yi a kasar Indiya da kuma ci-gaban dangantakar da ke tsakanin Sin da Indiya sosai. Ya ce,'Tabbas ne kasashenmu 2 suna taka muhimmiyar rawa a tsakanin kasashen duniya. Yau tattalin arzikinmu ya sake jawo hankali da kuma samun yabo daga kasashen duniya. Mun yi kusan shiga 'karni na Asiya' da shugabannin kasashen 2 suka kiyasta. Dangantakar abokantaka da hadin gwiwa mai nufin zaman lafiya da wadatuwa da ke tsakaninmu bisa muhimman tsare-tsare za ta kawo wa zuriyoyin Sin da Indiya alheri, har ma za ta kawo wa yankin da muke ciki da kuma duk duniya alheri ta fuskar kwanciyar hankali.'(Tasallah)