Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-22 09:50:09    
Wasan kankara salo-salo na gaurayen mace da namiji na kasar Sin ya shiga wani sabon mataki

cri

Kwanakin baya ba da dadewea ba,an kammala gasar ba da babbar kyauta ta `kofin Kasar Sin` ta wasan kankara salo-salo da kungiyar wasan kankara ta duniya ta shirya,shahararrun `yan wasa daga kasar Sin Shen Xue da Zhao Hongbo sun sami lambawan wato sun zama zakaru.Shen Xue da Zhao Hongbo sun taba samun lambawan na gasar wasan kankara salo-salo sau biyu a cikin gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 2002 da kuma shekarar 2003.A da ana tsammani cewar za su yi ritaya bayan taron wasannin Olimpic na Turin,amma sun sake komawa filin kankara kuma sun samun sabuwar nasara.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Shen Xue da Zhao Hongbo su ne zakarun duniya na farko na wasan kankara salo-salo na gaurayen mace da namiji na kasar Sin,sun taba shiga taron wasannin Olimpic na lokacin sanyi sau uku,ko a kasar Sin,ko a sauran wuraren duniya,sun samu karbuwa sosai daga wajen `yan kallon wasa.A gun taron wasannin Olimpic da aka shirya a Turin a shekarar 2006,kafar Zhao Hongbo ta ji rauni,sun sami lambatiri kawai,ba su cimma burinsu ba wato ba su zama zakarun taron wasannin Olimpic ba,shi ya sa sun canja tunaninsu,ba su yi ritaya ba,sai su ci gaba da yin kokari a kan filin kankara.

Yayin da suke yin gasar ba da babbar kyauta ta kofin Kasar Sin,Shen Xue ta gaya wa manema labaru cewa:  `Muna so mu samun sabon ci gaba,saboda ana tsammanin za mu yi ritaya ba da dadewa ba,amma ba haka ba ne,za mu ci gaba da yin kokari,dalilin da ya sa haka shi ne domin muna da boyayyen karfi kan wasan.`

A gun wannan gasa wato gasar ba da babbar kyauta ta kofin Kasar Sin,Shen Xue da Zhao Hongbo sun shirya wani sabon shiri na wasan kankara salo-salo wanda ke da lakabin haka:`Tunani`.A cikin wannan shiri,bisa karo na farko ne sun bayyana mana sosai kan yadda suka gamu da juna da yadda suka zama abokai ta hanyar yin rawa.Shen Xue da Zhao Hongbo su kansu sun nuna gamsuwa sosai kan wannan,Shen Xue ta bayyana cewa,rawar da suka taka tana da kyan gani kwarai da gaske,ana iya jin dadi daga wajenta.Kodayake shirin rawar nan na `Tunani` ya ci maki mai faranta ran mutane a gun gasa,amma Shen Xue da Zhao Hongbo ba su daina yin kokari ba,Zhao Hongbo ya ce,  `Zan kyautata salon yin tsalle-tsalle saboda ya kasance da karanci a ciki,shi ya sa kamata ya yi mu ci gaba da sanya matukar kokari domin gasar da za a yi a nan gaba.`

Ban da wannan kuma,Shen Xue da Zhao Hongbo su ma sun shirya sauran sabbin shirye-shirye biyu wato `Tarihin soyayya mai tsanani` da `Hanya`.Don kara kyautata shirye-shiryensu,a cikin watanni shida da suka shige,Shen Xue da Zhou Hongbo sun tafi kasar Canada sau tarin yawa,suna sanya iyakacin kokari.Amma dukkan wadannan suna nuna mana cewa,a kalla a cikin shekara daya mai zuwa,Shen Xue da zhao Hongbo ba za su yi ritaya ba,wato za su ci gaba da taka rawa kan filin kankara,sun riga sun bayyana cewa,tabban ne za su shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kankara salo-salo da za a yi a shekara mai zuwa.

A halin da ake ciki yanzu,a kasar Sin ba `yan wasa wadanda ke yin wasan kankara salo-salo na gaurayen mace da namiji da yawa,musamman fitatun `yan wasa na wasan,ban da Shen Xue da Zhao Hongbo,sai Zhang Dan da Zhang Hao da kuma Pang Qing da Tong Jian,ba saura.Alal misali,Li Jiaqi da Xu Jiankun wadanda suka shiga gasar ba da babbar kyauta ta kofin Kasar Sin da aka yi a shekarar bana,a bayyane ne ba su da isashen fasahar babbar gasa.A karkashin irin wannan hali,ana iya cewar kasar Sin tana bukatar Shen Xue da Zhao Hongbo,wato wasan kankara salo-salo na gaurayen mace da namiji na kasar Sin yana bakatarsu saboda karfin fasaha da karfin nuna fasaha da karfin tasiri a duniya na Shen Xue da Zhao Hongbo suna gaban sauran `yan wasa na kasar Sin.

Ya zuwa yanzu,shekarun haihuwa na `yan wasan kankara salo-salo na gaurayen mace da namiji a duniya ba su zarce 36 ba,Shen Xue ta riga ta kai shekaru 28 da haihuwa,Zhao Hongbo shi ma ya riga ya kai shekaru 33 da haihuwa,yaushe za su yi ritaya?Game da wannan,Zhao Hongbo ya ce:  `Idan matsayin wasana bai kama baya ba yayin da shekaruna da haihuwa ya kai 40,zan ci gaba.`Kila ne Shen Xue da Zhao Hongbo za su kago wata tatsuniya a tarihin wasan kankara na duniya.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)