Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-22 09:48:46    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (16/11-22/11)

cri

Ran 17 ga wata,an kafa kungiyar wakilan wasannin motsa jiki ta kasar Sin ta zama na 15 na taron wasannin Asiya a birnin Beijing,babban binin kasar Sin.Kungiyar tana kunshe da wakilai 928,wadanda a cikinsu, `yan wasa sun kai 647,shugaban kwamitin wasannin Olimpic na kasar Sin Liu Peng shi ne ya zama shugaban kungiyar.Kwatankwacin shekarun haihuwa na `yan wasan kungiyar ya kai 23.3 ne kawai.Kuma `yan wasan da yawansu ya kai kashi 63.8 cikin dari ba su taba shiga hadaddiyar babbar gasa ta duniya ba.Za a yi zama na 15 na taron wasannin Asiya a birnin Doha na kasar Quatar daga ran 1 zuwa ran 15 ga watan gobe na shekarar bana.

Ran 19 ga wata,an kammala karo na karshe na gasar ba da babbar kyauta ta gasar tsinduma cikin ruwa da kungiyar iyo ta duniya ta shirya a birnin Guadalajara na kasar Mexico,a gun gasar,gaba daya kungiyar kasar Sin ta samun lambobin zinariya 7 da lambobin azurfa 4 da kuma na tagulla 1.

Ran 16 ga wata,an kawo karshen gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon boli ta shekarar 2006 a birnin Osaka na kasar Japan,kungiyar kasar Rasha ta lashe kugiyar kasar Brazil da maki 3 bisa 2,ta zama zakara,kugniyar kasar Brazil ta zama lambatu,kungiyar kasar Sin kuwa ta samun lamba ta biyar.

Ran 18 ga wata,a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kankara da kungiyar wasan kankara ta duniya ta shirya a kasar Jamus,`yar wasa daga kasar Sin Wang Beixing ta samun lambatiri na gasar mita 500 na mata.

Ran 19 ga wata,an kammala zama na farko na gasar cin kofin Asiya ta wasan tennis ta dalibai a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin,`yan wasa daga kasar Sin sun samu nasarar lashe dukkan zakaru na gasa tsakanin mace da mace da gasa tsakanin mata biyu biyu da kuma gasa ta gaurayen mace da nimiji.(Jamila Zhou)