Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-21 19:00:21    
UNDP da gwamnatin kasar Sin suna kokarin fama da talauci ta fasahar da ke dace da muhalli

cri

A ran 21 ga wata, cikin hadin guiwa ne a nan birnin Beijing, hukumar tsara shirin neman bunkasuwa ta M.D.D. wato UNDP da gwamnatin kasar Sin suka kaddamar da wani shirin fama da talauci ta fasahar da ke dacewa da muhalli a yankunan da ke yammacin kasar Sin. Bisa wannan shiri, za a yi amfani da fasahar da ke dacewa da muhalli a larduna 5 da ke yammacin kasar Sin domin karuwar yawan kudin shiga na manoma da kuma kyautata yanayin daukar sauti da muhalli na wadannan larduna.

A lardunan Sichuan da Yunnan da Guizhou da ke yammacin kasar Sin, ana da wani tsiron daji da ake kiran shi "Itacen Kuturta" cikin harshen Sinanci a yankunan tsaunakan wadannan larduna. Manoman wurin sun dade suna amfani da shi lokacin da suke yin shingen tsaron gida. Amma yanzu, a karkashin taimakawar wannan shirin da UNDP da gwamnatin kasar Sin suke aiwatarwa cikin hadin guiwa, za a iya samun man dizal daga irin wannan itace. Sakamakon haka, yawan kudin shiga da za su samu zai karu.

Hukumar tsara shirin neman bunkasuwa ta M.D.D. wato UNDP da ma'aikatar kimiyya da fasaha da ma'aikatar kasuwanci na kasar Sin ne suke aiwatar da wannan shiri tare. Malama Alessandra Tisot, mataimakiyar wakilin UNDP da ke nan kasar Sin ta nuna cewa, neman albarkatun da ke dacewa da muhalli da raya sana'o'in da ba za su lalata muhalli ba suna da muhimmanci sosai ga yunkurin rage yawan mutane matalauta a yankunan da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Malama Tisot ta ce, "Lokacin da ake raya tattalin arziki da al'ummar yankunan yammacin kasar Sin, ana kara neman albarkatun halittu a kai a kai. Ta yadda za a kara biyan irin wannan bukatun da ake nema, ya zama wani muhimmin abu daga cikin hanyoyin fama da talauci domin cimma burin rage yawan mutane matalauta. Bisa shirin da muke aiwatarwa, za mu nemi wata sabuwar hanyar da ba ma kawai za ta iya fama da talauci ba, har ma za ta iya kiyaye muhalli."

A cikin shekaru fiye da 20 da suka wuce, tattalin arzikin kasar Sin ya sami cigaba cikin sauri sosai, matsakaicin saurin karuwar GDP na duk kasar Sin ya kai kashi 9.4 daga cikin kashi dari a kowace shekara. Matsakaicin yawan kudin shiga da kowane mutum ya samu ya ninka sau 3. Amma a wasu yankunan da ke yammacin kasar Sin, yawan matalauta yana ta karuwa a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce. Muhimman dalilan da suka haddasa haka su ne, ba su kiwo ko yin aikin gona bisa hanyoyin kimiyya. Hanyoyin kiwo da yin aikin gona da suke bi suna kawo illa sosai ga yanayin daukan sauti.

Bisa shirin fama da talauci ta fasahar da ke dacewa da muhalli da ake aiwatar da shi a lardunan Sichuan da Yunnan da Guizhou da jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta da jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta, za a kara raya albarkatun da za a iya sake yin amfani da su. Jami'in da ke kula da wannan shiri na kasar Sin ya bayyana cewa, ba ma kawai za a nemi man dizal daga ire-iren itacen Kuturta ba, hatta ma za a shuka itacen da ake kiran shi Jarrah Dayun a jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta. Irin wannan itace ba ma kawai za a iya amfani da shi tamkar magani ba, har ma za a iya amfani da shi domin rigakafin iska mai rairayi. Bugu da kari kuma, za a samar wa makiyayan jihar Mongoliya ta gida kananan injunan da ke samar da wutar lantarki ta fuskar karfin iska domin kyautata ingancin rayuwarsu. Mr. Wu Zhong, direktan hukumar yin cudanya da kasashen waje a ofishin shugabancin aikin fama da talauci na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya bayyana cewa, irin wannan tunanin fama da talauci ta hanyar neman bunkasuwa zai yi tasiri sosai ga yunkurin fama da talauci da kasar Sin take yi. Mr. Wu ya ce, "Wannan shiri yana hada fasahohin zamani da yunkurin fama da talauci tare. Kuma yana hada aikin kiyaye muhalli da yunkurin karuwar kudin shiga na matalauta a yankunan da ke fama da talauci. Wannan shiri yana kyautata hanyoyinmu da muke bi wajen yunkurin fama da talauci ta hanyar neman bunkasuwa."

Bisa shirin da aka tsara, a cikin shekaru 5 masu zuwa, za a zuba kudaden da yawansu zai kai kudin dalar Amurka miliyan 8 da dubu 580 domin aiwatar da wannan shiri a larduna 5 da muka ambata a sama. (Sanusi Chen)