Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-21 17:44:26    
Cututtukan zuciya su kan haifar da ciwon bakin ciki

cri

Barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili mai farin jini wato "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku wani bayani kan cewa, cututtukan zuciya su kan haifar da ciwon bakin ciki, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka: kasar Sin ta taimaka wa kasashe masu tasowa wajen horar da ma'aikata masu sa ido kan ingancin abinci. To, yanzu ga bayanin

Wani nazari da kasar Amurka ta yi ya bayyana cewa, daga cikin mutanen da ke zuwa asibitoci domin yin musu aiki a zuciya sakamakon cututtukan zuciya, mai yiyuwa ne fiye da rabi daga cikinsu su kan fi saukin kamuwa da ciwon bakin ciki, wato ba su son yin magana da sauran mutane, da kuma rashin sha'awa ga dukkan harkokin da suke shafi rayuwarsu. Amma a waje daya kuma kwararru sun jadadda cewa, muddin aka mai da hankali a kan ciwon bakin ciki, to za a iya magance wannan ciwo.

Wasu kararru na jami'ar California ta kasar Amurka sun buga wani bayani a cikin Mujallar kwamitin kula da ilmin likita ta kasar Amurka, inda suka bayyana cewa, dalilin da ya sa cututtukan zuciya su kan haifar da irin wannan ciwon bakin ciki shi ne sabo da masu fama da cututtukan zuciya su kan fuskanci wani hali na saduda rayuwa yayin da suka samu kansu cikin irin wannan hali, ban da wannan kuma mai yiyuwa ne su sami rauni a kwakwalwarsu yayin da ake yi musu titaya.

Amma kwararru sun nuna cewa, ana iya magancewa da kuma warkar da ciwon bakin ciki da a kan kamu da shi sakamakon cututtukan zuciya. Wani nazari ya taba bayyana cewa, bayan da mutane masu kamuwa da irin wannan ciwon bakin ciki suka sha magungunan shawo kan ciwon, mutane kashi 80 bisa dari da ke cikinsu sun sami sauki.

Bugu da kari kuma kwararrun da abin ya shafa sun yi kira ga likitoci da iyalan mutane masu fama da cututtukann zuciya da su dora muhimmanci kan lafiyar hankalin mutane masu fama da cututtukann zuciya. Idan an fara ganin alamun irin wannan ciwon bakin ciki, ya kamata a gaggauta zuwa asibiti nan da nan, ta yadda za a iya yin musu jiyya tun da wuri. Ban da wannan kuma kwararru sun yi nuni da cewa, idan an warkar da ciwon bakin ciki, to wannan zai ba da taimako ga masu fama da cututtukan zuciya wajen kara yin motsa jiki da kuma amince da jiyya da aka yi musu, ta yadda za su sami sauki wajen cututtukan zuciya da suke kamuwa.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, kasar Sin ta taimaka wa kasashe masu tasowa wajen horar da ma'aikata masu sa ido kan ingancin abinci.