Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-21 17:28:32    
Wurin shakatawa na Yuexiu

cri

Assalamu alaikun. Jama'a masu sauraro. Barkanku da war haka. A wannan mako ma za mu kawo muku shirinmu na yawon shakatawa a kasar Sin wanda mu kan gabatar muku a ko wane mako. A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan wurirn shakatawa na Yuexiu.

Wurin shakatawa na Yuexiu mai fadin eka 92.8 yana kan dutsen Yuexiushan a arewacin lardin Guangdong na kasar Sin, wurin shakatawa ne mafi girma a birnin Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong.

Kafin shekarar 1949, wurin shakatawa na Yuexiu ya lalace, shi ya sa a kan binne matattu a nan, bugu da kari kuma, 'yan iska su kan taru a nan. Amma bayan shekarar 1949, sabuwar gwamnatin kasar Sin ta yi kira ga mazaunan wurin da su dasa bishiyoyi a kan dutsen, ta kuma gina filin wasa da cibiyar iyo da cibiyar jin dadin jama'a da ma'adanin hotunan zane da dakin nune-nunen furanni da wani babban daki da sauran cibiyoyin al'adu da wasanni don kiyaye da sabunta abubuwan zamanin da da na tarihi.

A cikin wannan wurin shakatawa, akwai hasumiyar Zhenhailou, wadda wani yarima na zamanin daular Ming na kasar Sin ya gina ta don nuna bajimtarsa wajen yin kaka-gida a teku, da dakin tunawa da marigayi Sun Yat-sen, wanda tsohon shugaba ne a lokacin da aka fara yin juya juyin hali a kasar Sin, da mutum-mutumin awaki 5 da sauran wuraren da ke jawo masu yawon shakatawa.

Ban da wannan kuma, an haka tabkuna 3 a wurin shakatawa na Yuexiu. Mutane su kan yi zane-zane a kewayen tabkin Dongxiuhu don kyaun ganinsa. Tabkin Nanxiuhu wuri ne mai kyau wajen kamun kifi da kogiya. Tabkin Beixiuhu ya hada da kananan tabkuna 3, gadojin duwatsu sun hada su tare, ban da wannan kuma, akwai wasu kananan tsibirai a cikin wannan tabki, ta haka wannan tabki mai ni'ima ya zama tamkar zane-zane.

Masu yawon shakatawa su kan yi haya kananan jiragen ruwa don shawagi a tabkuna da kuma jin dadin ganin wurare masu ni'ima da ke kewayensu.

An dasa bishiyoyi fiye da miliyan daya a kan dutsen Yuexiushan. Haka kuma akwai wasu lambuna don noman furanni iri daban daban. A ko wace baraza da lokacin kaka an yi bukukuwan nune-nunen furanni a wannan wurin shakatawa.