Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-20 20:06:25    
An samu sakamako mai kyau wajen hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin ilmin koyar da sana'o'i da fasaha

cri

A 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta gudanar da kwas din horaswa ga kasashen Afirka wajen ilmin koyar da sana'o'i, da aika da malaman kasar Sin zuwa Afirka, da kuma amincewa da malaman Afirka masu koyar da sana'a'o'i zuwa kasar Sin don kara ilminsu, kuma ta wadannan ayyuka, an samu wata sabuwar hanya wajen yin mu'amala tsakaninta da kasashen Afirka a fannin sha'anin ilmi, ban da wannan kuma an ci gaba da inganta hadin gwiwar aminci tsakanin Sin da Afirka wajen sha'anin ilmi da kuma zumuntan gargajiya da ke tsakaninsu.

Hadin kai tsakanin kasashen Sin da Habasha wajen ilmin koyar da sana'o'i wanda ya samu nasara sosai ya zama tamkar wani abin koyi ne na hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka a fannin sha'anin ilmi.

A shekara ta 1991, gwamnatin kasar Habasha ta tsara manufar raya masana'antu a karkashin jagorancin sha'anin noma, kuma ta fara mai da hankali sosai kan ilmin koyar da sana'o'i da fasaha. Kasar Habasha tana ganin cewa, ta iya koyon sakamako masu kyau da kasar Sin ta samu wajen ilmin koyar da sana'o'i da fasaha, shi ya sa tana Allah Allah ta hada kanta tare da kasar Sin a wannan fanni.

A shekara ta 2001, gwamnatocin kasashen Sin da Habasha sun rattaba hannu a kan yarjejeniya a hukunce, da kuma fara hadin gwiwa tsakaninsu a fannin ilmin koyar da sana'o'i da fasaha. Gwamnatin kasar Sin ta dora muhimmanci sosai kan wannan aikin hadin gwiwa iri na sabon salo. Domin tabbatar da gudanar da wannan aiki lami lafiya da kuma samun bunkasuwa mai dorewa, a watan Afril na shekara ta 2003, ma'aikatar ilmi ta kasar Sin ta kafa wani sansanin ba da taimako ga kasashen waje wajen ayyukan koyarwa a birnin Tianjin na kasar Sin. Kuma bisa bukatar da kasar Habasha ta gabatar, bi da bi ne sansanin ya aika da malaman kasar Sin 81 zuwa muhimman makarantu 26 masu koyar da sana'o'i na kasar Habasha domin gudanar da ayyukan koyarwa.

A 'yan shekarun nan da suka gabata, malaman kasar Sin sun bayar da gudummuwarsu wajen ingantawa da bunkasa zumuntan gargajiya da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Habasha bisa kyakkyawar kwarewar aikinsu, da ra'ayoyinsu na zamani wajen ayyukan koyarwa, da hanyoyin koyarwa masu kyau, da kuma ra'ayin gudanar da ayyukansu a tsanake. Sabo da haka gwamnatin kasar Habasha da mutanenta sun nuna yabo sosai gare su.

Domin ba da taimako ga kasar Habasha wajen horar da kwararru masu gudanar da ayyukan ilmin koyar da sana'o'i da fasaha, ma'aiktar ilmi ta kasar Sin ta na samar da sukolashif na gwamnatin kasar Sin iri daban daban ga kasar Habasha a ko wace shekara, ban da wannan kuma ta kira taruruka har sau uku na dandalin tattaunawa tsakanin shugabannin makarantun koyar da sana'o'i da fasaha na kasashe masu tasowa, da kuma shirya kwas din horaswa iri daban daban cikin gajarren lokaci har sau biyar. Ya zuwa yanzu an riga an horar da malamai da kwararru na kasar Habasha fiye da 90 a fannin ilmin koyar da sana'o'i da fasaha.

Haka kuma a cikin shekarun nan da suka gabata, ma'aikatun ilmi na kasashen Sin da Habasha sun rika yin ziyara da mu'amalar aminci tsakaninsu domin inganta sabbin fannoni da hanyoyin hadin gwiwa tsakaninsu ta hanyar yin musanyar ra'ayoyinsu, ta yadda za a sa kaimi ga hadin gwiwarsu. Musamman ma bayan da bangarorin biyu suka hada kansu a fannin ilmin koyar da sana'o'i da fasaha, sun kara fahimtar juna da amincewa da juna. Sau da yawa jami'an gwamnatin kasar Habasha sun nuna yabo ga gwamnatin kasar Sin da jama'ar Sin da su ba da taimako sosai wajen bunkasuwar sha'anin ilmi da ci gaban zamantakewar al'ummar kasar Habasha, kuma sun dauki jama'ar kasar Sin tamkar sahihan abokansu.

Sabo da kokarin da kasashen Sin da Habasha suka yi tare, kasashen biyu sun samu babban ci gaba wajen hadin gwiwa tsakaninsu a fannin ilmin koyar da sana'o'i da fasaha. Bangaren Habasha ta bayyana cewa, zai sake daukar malaman kasar Sin zuwa Habasha domin gudanar da sabbin ayyukan koyar da sana'o'i da fasaha da zai kaddamar da su.

Bisa sabuwar yarjejeniyar da kasashen Sin da Habasha suka rattaba hannu a kai, ma'aikatar ilmi ta kasar Habasha tana cikin shirin shigad da malaman kasar Sin mafi yawa wajen ilmin koyar da sana'o'i da fasaha. Kuma an kiyasta cewa, za ta shigad da malaman kasar Sin fiye da 170 a shekaru 3 masu zuwa. Ma'aikatar ilmi ta kasar Habasha ta gayyaci malamai na kasar Sin da su sa hannu a cikin ayyukan koyarwa da na gudanarwa na makarantunta 15 da aka kafa su ba da dadewa ba. Game da batun, ma'aikatun ilmi na kasashen biyu suna yin shawarwari tsakaninsu a tsanake. Wani abin farin ciki shi ne za a fara aiki da kwalejin koyar da sana'o'i da fasaha na birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha a watan Satumba na shekara ta 2007 wanda gwamnatin kasar Sin ta ba da taimako wajen gina shi. Kwalejin za ta yi amfani da salon zamani na kasar Sin wajen ilmin koyar da sana'o'i da fasaha, ta yadda zai zama wani abin koyi ne na kwalejojin koyar da sana'o'i da fasaha na kasar Habasha da na sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.(Kande Gao)