Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-17 17:20:59    
Kasar Sin da Afrika suna hadin kansu a fannin kiyaye muhalli don moriyar juna

cri
A cikin 'yan shekarun nan da suka gabata, hadin kan kasar Sin da na Afrika a fannin kiyaye muhalli, ya zama wani sabon fanni ne mai muhimmanci ga hadin kansu. A lokacin da ake zaman taron majalisar dinkin duniya kan sauye-sauyen yanayi, hadin kan kasar Sin da na Afrika a fannin kiyaye muhalli ya sake zama wani babban batu da ake tattaunawa a kai.

Ya zuwa yanzu, an riga an shafe kimanin makonni biyu ana yin taron nan a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya. Kasashe daban daban da ke halartar taron suna mai da hankali sosai ga yadda za a taimaki kasashen Afrika wajen dacewa da sauye-sauyen yanayi, da kare muhalli da rage yawan iska mai dumama yanayi da ake fitarwa. Malam Su Wei, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin yarjejeniyoyi na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin wanda ke halaratar taron ya bayyana cewa, "kasar Sin da Afrika suna iya hadin kansu wajen kiyaye muhalli a fannoni da dama. A gun taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwa tsakanin Sin da Afrika, kasar Sin ta dauki alkawarin ba da gudummuwar kudi cewa, za ta samar da rancen kudi da darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 5, wannan ya aza kyakkyawan harsashi ga hadin kan Sin da Afrika a fannin kiyaye muhalli. Sakamako da nasarori masu yawa da kasar Sin ta samu wajen kiyaye muhalli, suna da muhimmanci sosai ga kara inganta hadin kansu, ta hanyar musanyar sakamakon da horar da kwararru domin nahiyar Afrika da sauransu."

A hakika dai, a cikin shekarun nan da suka wuce, hukumomin kiyaye muhalli na Sin da kasashen Afrika sun riga sun hada guiwarsu sosai. Malam Tomyeba Komi, wakilin kasar Togo kuma jami'in ma'aikatar kare muhalli ta kasar ya ce, " ya kasance da kyakkyawar dangantakar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afrika da yawa. Alal misali, kasar Togo ta aiko da mutanenta da yawa zuwa kasar Sin don koyon fasahar aikin gona da sake sarrafa juji da sauransu. Muna da ra'ayi iri daya, kuma muna cudanya sosai a tsakaninsu a kan batun sauye-sauyen yanayi, muna da ra'ayi iri daya, muna tsayawa a kan matsayi daya, muna hadin kanmu don yaki da sauye-sauyen yanayi, kuma muna tattaunawa kan manyan tsare-tsaren magance sauye-sauyen yanayi."

Malam Bubaka Raja, wakilin kasar Tanzaniya kuma sakataren ofishin mataimakin shugaban kasar shi ma ya nuna ra'ayinsa daidai da na Malam Tomyeba Komi. Ya ce, "kullum muna tsayawakafada da kafada da kasar Sin, mun amince da cewa, za mu sami ci gaba tare, jama'ar kasar Sin suna fahimtar mu, dalilin da ya sa haka shi ne domin mu aminansu ne. Wani muhimmin abu da ya kamata mu fahimta shi ne, sai da kare muhalli da kyau, za a iya bunkasa tattalin arziki."

Wakilin kasar Kenya mai masaukin taron nan kuma shehun malami na Jami'ar Nairobi Richard Odingo ya ce, yana fatan za a kara inganta hadin kai da yin musaye-musaye a tsakanin Sin da Afrika a fannin kiyaye muhalli. Abin da ya sa haka shi ne domin ba ma kawai irin wannan hadin kai yana ba da taimako ga kiyaye muhallinsu da samun ci gaba mai dorewa ba, har ma yana ba da taimako wajen kiyaye muhalli da magance sauye-sauyen yanayi a duk duniya.

Bayan haka ya kara da cewa, dangantakar hadin kai a tsakanin Sin da Afrika tana da inganci. Mun hakkake, za a ci gaba da inganta irin wannan dangantaka. Muna fatan gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga yin ma'amala da ziyare-ziyarce a tsakanin Sin da Afrika, kuma ta sa kaimi ga kasashen Afrika da su kawo ziyara a kasar Sin, ta hanyar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hakin kai a tsakanin Sin da Afrika da aka shirya a makonni da suka wuce. (Halilu)