Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-17 16:13:54    
Ana da makoma mai kyau wajen hadin guiwar makamashi a tsakanin kasashen gabashin Asiya

cri

A cikin 'yan shekarun nan, kasashen gabashin Asiya sun sha kasance cikin sahon gaba wajen bunkasa harkokin tattalin arzikinsu da sauri. Sa'an nan kuma yawan kudade da Sin da Japan da Korea ta Kudu da sauran kasashen gabashin Asiya ke samu daga wajen cinikayya da ake yi a tsakaninsu ya yi ta karuwa. Ka zalika hadin kansu a fannin makamashi ma kullum sai kara bunkasa yake yi.

Bisa matsayinta na wata babbar kasa a yankin gabashin Asiya, kasar Sin ta yi ta bunkasa tattalin arzikinta da sauri a cikin shekarun nan da yawa da suka wuce. Amma matsalar makamashi da take butaka, tana cima mata tuwo a kwarya.

Yau da shekara 1 da ta wuce, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da manufofinta game da raya zamantakewar al'umma mai tsimin makamashi kuma ba tare da gurbacewar muhalli ba. Malam Xu Dingming, mataimakin shugaban kungiyar shugabancin ayyukan makamashi ta kasar Sin yana ganin cewa, yin amfani da makamashi maras gurbata yanayi hanya ce da ya kamata a bi wajen daidaita batun makamashi a duk duniya. Ya kara da cewa, "a sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin duniya, batutuwan makamashi da na muhalli kullum sai kara tsanani suke yi. Idan ba a iya warware batutuwan nan sosai ba, to, ba ma kawai da kyar dan adam za su cim ma manufar samun bunkasuwa mai dorewa ba, har ma za su sha wahala wajen zaman rayuwarsu da kuma muhallinsu. A kara kokari wajen yin amfani da makamashi maras gurbata muhalli wanda ya yi armashi a duniya, wannan wata hanya ce da ya kamata a bi wajen magance batutuwan makamashi da muhalli wadanda kullum sai kara tsanani suke yi, kuma wata hanya ce da ya kamata a bi don neman samu ci gaba mai dorewa wajen raya zamantakewar al'umma."

Bayan haka Malam Xu Dingming yana ganin cewa, da ya ke kasar Sin da sauran kasashen gabashin Asiya da yankuna suna kara dogara da juna a fannin tattalin arziki, ya kamata, su hada kansu a fannin makamashi. Ya ce, "ya kamata, mu sami sabon ra'ayin ba da tabbaci ga samar da makamashi a duk duniya ta hanyar hadin kai don moriyar juna. Mu da kasashen gabashin Asiya da kasashen arewa maso gabashin Asiya muna yi ta hadin kanmu a fannin makamashi. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, muna ma'amala a tsakaninmu da kasashen Japan da Korea ta Kudu a fannoni da dama, muna maraba da aminanmu na gabashin Asiya wajen yin kokari tare don raya makamashi maras gurbata yanayi, ta yadda za a ba da tabbaci ga samar da makamashi a gabashin Asiya."

A halin yanzu, kasar Sin ba ta sami ci gaba sosai wajen raya makamashi maras gurbata yanayi da yin amfani da shi ba, sabo da haka gwamnatin kasar Sin tana bai wa masana'antun kasashen waje kwarin guiwa wajen zuba jari kan raya makamashi. Shehun malami Akihiro Kuroki wanda ke yin aiki a cibiyar binciken makamashi da tattalin arziki ta kasar Japan yana ganin cewa, kasashen Sin da Japan za su iya hada kansu sosai a fannin tsimin makamashi. Ya ce, " yanzu kasashen Sin da Japan suna gudanar da wani aiki cikin hadin guiwarsu, don daga matsayin yin amfani da makamashi. Kasar Sin kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen daga matsayin yin amfani da makamashi a gabashin Asiya. A kwanakin baya ba da dadewa ba, jama'ai masu kula da harkokin tattalin arziki na kasashen biyu sun taba shirya wani taro a birnin Tokyo na kasar Japan, inda suka sami ra'ayi daya a kan hadin guiwarsu a fannin fasahar yin amfani da makamashi da sauransu."

Tsimin makamashi da raya makamashi maras gurbata yanayi yana dacewa da moriyar kasar Sin, kuma yana samar da dama ga masana'antu masu yawa na kasashen gabashin Asiya da yankuna wajen gudanar da harkokinsu a kasar Sin.(Halilu)