Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-17 16:11:37    
Kyautatuwar yanayin sufurin Beijing a lokacin dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afrika ta samar da fasahohi ga gudanar da taron wasannin Olympic

cri

A duk tsawon lokacin da ake gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a kwanakin baya ba da dadewa ba, an kyautata yanayin sufurin birnin Beijing a bayyane, wato ke nan a da akan samu cunkoson motoci a nan Beijing, amma aka kawar da wannan hali ba zato ba tsammani a cikin wasu kwanaki kawai. To, ina dalili? Wadanne matakai ne gwamnatin birnin Beijing za ta dauka don kawar da matsi daga cunkuson motoci kafin a gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008?

Daya daga cikin kalubale mafi tsanani dake gaban gwamnatin Beijing wajen samun bunkasuwa kamar yadda manyan birane na zamani na sauran kasashe suke, shi ne cunkuson motoci. Yanzu, yawan mutanen birnin Beijing ya zarce miliyan goma sha shida, kuma yawan motoci ya wuce miliyan biyu da dubu dari takwas. Sakamakon haka, kusan dukan mazauna birnin Beijing suna shan wahala a kowace rana saboda gazawar da ake yi wajen warware maganar cunkuson motoci.

A lokacin da ake gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika daga ran 2 zuwa ran 7 ga watan da muke ciki, gwamnatin birnin Beijin ta dauki tsauraran matakai na wucin gadi na kyautata yanayin sufurin birnin domin ba da tabbaci ga shiga harkoki iri daban daban da manyan baki daga ketare suke yi. Wadannan matakai sun hada da takaita zirga-zirgar ababen hawa kan wasu hanyoyin mota na musamman a lokacin musamman, da sa kaimi ga mazauna birnin don su yi amfani da motocin bus na hanya da subway da kuma tsaida lokutan yin aiki da na tashi daga aiki ga wasu sassan gwamnatin birnin. Ko da yake mazauna birnin sun samu cikas saboda wadannan matakai da aka dauka, amma sun ga ana yin tafiye-tafiyen motoci kamar yadda ya kamata kuma iska na da kyau ainun.

Direban taxi Malam Guo Zhiqiang ya fada wa wakilinmu, cewa a duk tsawon lokacin da ake gudanar da dandalin tattaunawar hadi gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, mu direbobin taxi mun kara samun kudin shiga saboda mun kara samun damar daukar fasinjoji ba kamar yadda muka yi a da ba; yawan kudin shiga da muka samu ya karu da kimanin kashi 10 cikin kashi 100 bisa yau da kullum.

Karuwan yawan kudin shiga da direbobin taxi suka samu sun dogaro da wadanda sukan tuka motocinsu na kansu a yau da kullum. A lokacin taron, wadannan mutane sun tafi aiki da bos ko subway maimakon tuka mota. Bisa kididdigar da hukumar kiyaye muhalli ta birnin Beijing ta yi, an ce, a lokacin taron koli na Beijing, kungiyoyi sama da 400 masu sha'awar motoci sun kaddamar da matakin " kebe wata rana daya da ba za a tuka motoci ba" domin amsa kirarin kungiyoyin jama'a masu kiyaye muhalli da kuma wasu kafofin yada labarai. An yi lissafin cewa, akwai mutane da yawansu ya wuce dubu 410 wadanda ba su tuka motocinsu na kansu ba a duk tsawon lokacin dandalin tattaunawar hadin kan kasar Sin da kasashen Afrika.

Madam Tong Shan, babbar jami'ar wani kamfani ta shiga wannan matakin da aka kaddamar. A ganinta, ko da yake ba su samu sauki idan ba su tuka motocinsu na kansu ba, amma sun yi farin ciki matuka saboda sun ba da taimakonsu ga aikin kyautata yanayin sufurin birnin Beijing. Ta kuma yi hasashen, cewa ya kamata a dage ga yin haka cikin dogon lokaci ba wai wasu sa'o'I ko 'yan kwanaki ba. Kazalika, Madam Tong ta yi fatan za a kara samun ci gaba a fannin tafiye-tafiyen motoci da na subway a lokacin da ake gudanar da taron wasannin motsa jiki na Olympic na Beijing a shekarar 2008.

Jama'a masu saurare, a lokacin da ake gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, gwamnatin birnin Beijing ba ta dauki kowane matakin sarrafa tafiye-tafiyen motoci na mahasusin mutane ba, kuma ma'aikata na sana'o'I da dama sun yi hidima mai kyau ga taron kolin bayan aiki balle su yi hutu. A cikin wannan yunkuri, mazauna birnin masu yawan gaske sun dauki bos ko subway maimakon tuka motocinsu na kansu, wannan shi ne dalilin da ya sa aka samu kyakkyawan sufuri a duk tsawon lokacin taron kolin.

Yanzu, gwamnatin birnin Beijing tana kokari matuka wajen share fage ta hanyoyi daban daban ga tafiye-tafiyen motoci na taron wasannin Olympic na Beijing.(Sani Wang)