Yanzu zamu karanta muku sanarwar da aka bayar a gun taro na 5 na wakilan Kwamitin tsakiya na 16 na JKS . Sanarwar ta ce , a cikin shekaru 5 masu zuwa , Za a aiwatar da manyan sassan tattalin arziki cikin halin karko. Matsakaicin yawan GDP da za a samu zai karu da kashi 7.5 bisa 100 a kowace shekara, wato matsakaicin yawan GDP da kowane mutum zai samu zai ninka sau 2 bisa na shekarar 2000. Yawan mutanen da za su samu aikin yi zai karu da miliyan 45 a birane da garuruwa, yawan manoman da za su yi aikin kodago a birane shi ma zai kai haka, yawan mutane marasa aikin yi ba zai wuce kashi 5 bisa 100 ba.
Za a kyautata tsarin masana'antu da hawan matakinsa. Tsarin sana'o'i da na kayayyaki da na shirin kungiyar masana'antu za su kara samun daidaituwa, yawan karuwar kudin da za a samu wajen sana'ar yin hidima zai karu da kashi 3 cikin 100 bisa na dukkan GDP, yawan mutanen da za su samu aikin yi zai karu da kashi 4 cikin 100 bisa na dukkan mutane masu samun aikin yi na kasar. Karfin yin kirkire-kirkire cikin 'yanci zai karu, yawan kudin da za a ware domin yin bincike da gwaje-gwaje zai karu da kashi 2 cikin 100 bisa na dukkan GDP, ta yadda za a kafa wasu masana'antu wadanda za su kam matsayi mai rinjaye wajen samun ikon mallakar fasaha na kansu da yin gasa tsakanin kasashen duniya.
Yawan albarkatun kasa da ake yin amfani da su zai karu-karuwar gaske. Yawan makamashin da za a aiwatar da su domin aikin kawo albarka zai ragu da kashi 20 bisa 100, yawan ruwan da za a yi amfani da su domin aikin masana'antu kuma zai ragu da kashi 30 bisa 100, za a kara yin amfani da ruwa don shaya da gonaki, yawan tattakar makera da za a yi amfani da su domin samun bola jari zai karu har zai kai kashi 60 bisa 100.
Za a bunkasa birane da garuruwa bisa daidaici. Za a samu babbar nasara wajen raya sabbin kauyukan gurguzu, yawan alkaryu da garuruwan kasar Sin da za a mai da su irin na zamani zai kai kashi 47 bisa 100. Za a kafa tsarin bunkasa shiyya-shiyya masu halayen musamman, bambancin da ke tsakanin alkaryu da garuruwa wajen sana'ar yin hidima ga jama'a, da yawan kudin shiga da za a samu da kuma matsayin zaman rayuwar jama'a zai ragu.
Za a kara mai da hankali kan sana'ar yin hidima ga jama'a sosai. Tsawon lokacin ba da ilmin tilas ga jama'a zai karu zuwa shekaru 9. Za a kafa cikakken tsarin kiwon lafiya da yin hidima ga jama'a a fannin likitanci. Yawan jama'a da za su samu tabbacin taimako zai karu, yawan mutanen biranen da za su samu inshorar tsufa zai kai miliyan 223, yawan sabbin kauyukan da za su aiwatar da tsarin likitanci bisa turken gama karfi zai kai fiye da kashi 80 bisa 100. Yawan mutane masu fama da talauci zai ragu. Za a kara karfin yin rigakafi da fama da bala'o'i, kuma za a kara kyautata halin kiyaye zaman lafiya da yin aikin kawo albarka cikin lumana.
Abin da kuka saurara dazu nan shi ne Sanarwar da aka bayar a gun taro na 5 na wakilan Kwamitin Tsakiya na 16 na Jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin . Yanzu bari mu yi 'dan bayani kan sanarwar da aka bayar a gun taro na 4 na wakilan Kwamitin Tsakiya na 16 na JKS . Kwanan baya gwamnatin kasar Sin ta kira taron aiki kan yadda za a yi tsimin makamashi . Zeng Peiyan , wakilin Ofishin siyasa na Jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin ya yi jawabi kan aikin tsimin makamashi . Mr. Zeng ya jaddada cewa , za mu yi kokari don mai da kasar Sin da ta zama kasa mai tsimin makamashi kuma mai kasancewa da muhalli mai kyau da kuma tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin dogon lokaci . Ya karfafa magana cewa , kwamitin tsakiya na jam'iyyar da gwamnatin kasar Sin sun tsai da kudurin cewa , za a rage yawan makamashin da za a yi amfani da su har zuwa kashi 20 cikin 100 . Dole ne masana'antu daban daban da hukumomi daban daban na gwamnatocin matakai daban daban su tabbatar da wannan kudurin a cikin manyan kamfanoni masu yin amfani da makamashi mai yawa. (Ado)
|