Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-16 15:18:38    
An yi taron manyan jami'ai na M.D.D. kan sauye-sauyen yanayi

cri
A ran 15 ga wata, an yi taron manyan jami'ai, wato wani muhimmin taro ne na babban taron sauye-sauyen yanayi na M.D.D. da ake yi a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya. A gun bikin bude taron manyan jami'ai, wakilai masu halartar taron sun yi kira ga kasashe daban-daban, musamman ma ga kasashe masu sukuni da su yi hakikanin kokari su nuna goyon bayansu ga kasashe masu tasowa wajen fasaha, ta yadda za su iya magance matsalar sauye-sauyen yanayi na duk duniya. 

Mr. Kofi Annan, babban sakataren M.D.D., da Mr. Mwai Kibaki, shugaban kasar Kenya da ministoci fiye da 100 da wakilai fiye da 6000 wadanda suka zo daga kasashe daban-daban na duniya sun halarci bikin bude taron manyan jami'ai da aka yi a wannan rana. Mr. Annan ya yi jawabi a gun bikin cewa, "Bari mu kara nuna jan hali wajen siyasa. Wannan babban taron sauye-sauyen yanayi na Nairobi ya bayyana sosai cewa, shugabannin duk duniya za su fuskanci matsalar sauye-sauyen yanayi cikin tsanaki. Matsalar da ke kasancewa yanzu ba matsalar ko za a yi sauye- sauyen yanayi ba, amma matsala ce da ta kasance jarrabawa gare mu, wato ko za mu iya canja manufarmu a daidai lokaci cikin irin wannan halin gaggawa."

An ce, a gun taron manyan jami'ai da aka shafe kwanaki 3 ana yin sa a wannan gami, wakilai masu halartar taron za su ci gaba da tattauna matsalar "Kyoto ta nan gaba" wadda ta jawo hankulan mutane sosai, wato matsalar yadda za a kara rage yawan gurbatacciyar iska da aka fitar daga dakuna masu dumi bayan shekarar 2012. Mr. Kivutha Kibwana, shugaban babban taron, kuma ministan muhalli na Kenya ya ce, tun kwanaki 10 da suka wuce bayan da aka fara yin babban taron sauye-sauyen yanayi na M.D.D. bangarori daban- daban masu halartar taron sun riga sun samu ra'ayi daya kan matsalar dacewa da sauye-sauyen yanayi, da nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa wajen kudi. Ya ce, "Har zuwa yanzu, taron Nairobi ya riga ya samu babban ci gaba, an riga an daidaita muhimman matsaloli da yawa, kuma an samu ra'ayi daya kan wasu muhimman matsaloli daban. Halin hadin gwiwa da bangarori daban-daban masu halartar taron suka nuna ya faranta ran mutane sosai".

Amma sa'an nan Mr. Kibwana ya bayyana cewa, tsatsauran ra'ayin da wasu kasashe suka nuna kan muhimmiyar matsala kila zai jawo hadari ga samun nasarar babban taron. Cikin jawabin da Mr. Kibaki, shugaban kasar Kenya ya yi ya bayyana cewa, sauye-sauyen yanayi yana jawo mugun tasiri ga kasashe masu tasowa ciki har da kasashen Afirka har dogon lokaci, ya yi kira ga kasashe masu ci gaba da su ba da taimako ga kasashe masu tasowa domin magance sauye-sauyen yanayi. Ya ce, "Kan kasashe masu tasowa, idan ba su samu goyon baya wajen kokarin da suke yi domin rage yawan gurbatacciyar iska da aka fitar daga dakuna masu dumi, ba za su iya daidaita matsalar sauye-sauyen yanayi ba. Wani muhimmin abu daban shi ne, ya kamata kasashe masu ci gaba su kara rubanyan kokari domin nuna goyon baya ga kasashe masu tasowa wajen fasaha da kudi, ci gaban da aka samu wajen fasahar sadarwa da sarrafa lamurra daga nesa kan labarin kasa zai samar da sabuwar mafita domin fuskantar kalubalen da za a yi a nan gaba."  (Umaru)