Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-15 16:12:01    
Dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka

cri
Shekarar da muke ciki, wato shekara ta 2006, shekara ce ta cika shekaru 50 da kasar Sin ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasashen Afirka. A kwanan baya, wato daga ranar 3 zuwa ranar 5 ga wata, an yi taron dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a nan birnin Beijing, wanda ya kasance taro mafi kasaita a tsakanin Sin da kasashen Afirka a shekarun nan 50 da suka wuce, kuma manyan shugabannin Sin da na kasashen Afirka 48 sun halarci wannan taro. A gun taron, shugabannin Sin da Afirka sun bi manufar sada zumunta da zaman lafiya da hadin gwiwa da kuma ci gaba, sun tattauna kan yadda za su bunkasa huldar da ke tsakaninsu da kuma kara ingiza hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma sun sami manyan nasarori a wajen kara dankon zumunci da inganta hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka. Bayan da masu sauraronmu suka sami labarin wannan taron kuma, sun turo mana sakonni masu yawa, inda suka bayyana farin cikinsu game da taron da kuma ra'ayoyinsu dangane da hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka.

Malam Salisu Muhammad Dawanau, mai sauraronmu a ko da yaushe da ke zaune a Garki, Abuja, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana wata wasikar da ke da lakabi kamar haka, Sin da Afirka, Tsintsiya, madaurinki guda, inda ya ce, "cikin shekarun da suka gabata, an samu hadin gwiwa mai kyau tsakanin Sin da Afirka. Wannan ya samo asali ne saboda irin namijin kokari da bangarorin biyu ke da shi don neman hadin gwiwa mai dorewa tsakanin juna. Ko shakka babu, wannan hadin kai, ko hadin gwiwa na haifar da niyyar ci gaba da kuma huldar diplomasiyya cikin tsanaki da sanin ya kamata. A sanadin taron da ake shirin gudanarwa tsakanin Sin da Afirka, na tabbata bangarorin biyu za su dada samun moriya mai nagarta da kuma aminci, ta yadda kasashen biyu da kuma al'umarsu zasu samu alheri da kuma riba mai tsoka. A sanadin wannan taro, na tabbata fannonin noma da ilimi mai nagarta da sufuri da sadarwa da dai sauransu za su dada ingantuwa. Hakika, wannan taro zai taimaka kwarai da gaske wajen ci gaban kasa da kuma mutanenta. Zan yi murna idan mutanenmu na Afirka, bayan sun koma kasashensu na asali su yi amfani da abin da za su koyo daga wannan taro wajen koyarwa da kuma bin abin sawu-da-kafa don dada ingancin kasashensu da na al'umarsu. Haka ma su mutanen kasar Sin., ta hakan za a dada fahimtar juna da kuma gyara abota sannan kuma za'a dada amincewa da kuma yarda da juna.

Bayan haka, malam Adamu Mohammed ya rubuto mana cewa, gaskiya na ji dadin jin wannan labari daga gare ku, Allah kuma ya taimake ku tare da fatan za a yi taro a kuma gama lafiya Amin. Bayan haka ra'ayina game da taron shi ne, yana da matukar amfani game damu daku baki daya. Amfanin kuwa shi ne za mu karu da ku ta wajen ala'adu da kasuwanci, kuma ku tuna fa cewa ala'dunmu ta wani fannin namu sun yi kama da juna, sabo da haka wanan taro zai taimaka mana baki daya.

Email da malam Sanusi Isah Dankaba ya aiko mana ya yi nuni da cewa, dandalin hadinkai tsakanin Sin da Africa, wani babban muhimnin cigaba ne da fahimtar juna da aka samu tsakanin Sinawa da mu 'yan Africa. Kasar sin a zahiri tana son bunkasa kasuwanci da kasashen mu na africa kuma faduwa ta zo daidai da zama musamman a wannan karni da kasar sin take samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri, a ko yaushe ra'ayina shi ne bana tunanin duk wata matsala daga wajen Sinawa a kan wannan hadin guiwa, kamar wadansu yadda suke baiyanawa a kan cewa wai kasar sin tanason yin mulkin mallaka a kasashen africa wanda sam sam zancen karya ne.

Sai kuma malam Wadata daga computer center Audu Bako Secretariat da ke jihar Kano wanda ya duba shafinmu na internet ya bayyana mana cewa, wannan hadin gwiwa da aka yi tsakanin kasashenmu na Africa da kasar Sin yana da matukar muhimmanci domin kasar Sin kasa ce da ta dade da ci gaba ta fuskar tattalin arziki da masana'antu da ilmi da kiwon lafiya noma, kai komai da komai ta yi wa kasashen duniya zarra, ina ganin wannan hadin gwiwa yana da matukar muhimmanci kuma ina kira da hukumar kasar Sin, ta bar jama'arta su zo su kafa masana'antu a wannan nashiya tamu fiye da yanzu.

Sai kuma malam Aliyu Yahuza daga Hammaruwa way, Jalingo, jihar Taraba, tarayyar Nijeriya, ya rubuto mana cewa, ra'ayina game da taron hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Africa shi ne, a gaskiya wata hadin kai ne wadda duniya take hange (musamman kasashen Amurka da Europe) kamar China tana dibbar ganima a kasashen. Amma a hakikanin gaskiya ba haka ba ne. Dalilina shi ne Sin tana taimakawa wajen cin gaban kasashen wadda ba wata nahiya da ta damu sai dai a ce Africa sai yunwa.

A game da wannan hadayyar har yaka ga kasar Sin tana kerawa Nijeriya satelite a kasarta; wata kasa ce ta taba yiwa Nijeriya haka ko da dai a kasar Sin din ake yi, amma da inda ta taba tunanin tayi wa Nijeriya wannan taimako.

Bayan haka, malam Mamane Ada da ke aikin jarida a rediyo R&M da ke birnin Yamai na jamhuriyar Nijer, ya rubuto mana cewa, hakika dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, abu ne gagara misali wajen cigaban tattalin arziki na kasashe masu tashi da kuma wani sabon yunkuri da wani salo mai anfanin Afirka da kasar Sin ta kirkiro domin tabbatar da sabuwar hulda kan fannonin tattalin arziki da na kasuwanci. To a gaskiya a nan birnin Yamai, ta hanyar tashar rediyo R&M da ake watsa shirye-shiryen radiyo Sin, al'umar kasar Nijar na ganin cewa wannan taro, wani abu ne da zai mai da hankalin duniya ta hanyar alheri ga kasashen Afirka da sauran wasu kasashe na duniya.

Bayan wadannan sakonnin, akwai kuma malam Mahmud Mohammed Imam daga Ibadan Street, Kaduna, Nijeriya, da Alh Yahaya Shehu daga Bukuru, jihar Plateau ta Nijeriya da malam Harouna Habib daga jamhuriyar Nijer da malam Mahaman Salisu Hamisu da Aliyu alhassan da Abdullahi Baba da dai sauransu, wadanda suka rubuto mana. Mun gode, sabo da sakonnin da kuka aiko mana, kuma daga cikin sakonnin, muna iya gane goyon baya da kishi da wadannan masu sauraronmu suke nuna ga hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka. Mun gode, Allah ya bar zumunci a tsakanin jama'ar kasar Sin da ta kasashen Afirka. (Lubabatu)