Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-15 16:10:01    
Musanyar al'adu da Sin da Afirka suke yi

cri

Wata 'yar kallon kasar Sin daban ta kuma bayyana cewa, a ganina, kara wa juna fahimta na da kyau sosai, in ba hakan ba, ba mu san al'adun Afrika da fasahohinsu ba, ko shakka babu wasannin da suka nuna ne daga mafarinsu na yin zaman rayuwa a yau da kullum cikin sahihanci sosai tare da nuna hakikanan abubuwa, ba su nuna fasahohinsu kawai ba, daga wasannin da suka nuna, mu iya fahimci halayen musamman na al'adunsu.

Ban da wannan kuma, gidan baje koli na kasar Sin ya kuma shirya wani nunin nagartattun kayayyakin fasaha na kasashen Afrika da ke da lakabi haka, zuwan nan daga Afrika, a gun nunin, an nuna kayayyakin sassaka da sake-sake da na tangaram fiye da 300 da suka zo daga kasashen Afrika fiye da 20, 'yan kallon kasar Sin suna iya kallon kayayyakin fasaha na kasashen Afrika wadanda ba a canja tsohon salonsu ba sosai.

A gaskiya dai, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tana ta kara bunkasuwa.

Afrika tana da nisa da kasar Sin, ba da sauki ba wajen yin zirga-zirga a tsakaninsu, amma a cikin shekaru 50 da suka wuce, bisa kokarin sa kaimi da goyon baya da kasar Sin da kasashe daban daban na Afrika suka yi tare ne, kullum ma'amalar al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tana kara samun bunkasuwa. Ya zuwa yanzu, yawan shirye-shiryen aiwatar da yarjejeniyoyin al'adu da kasar Sin da kasashen Afrika suka daddale ya kai 156, yawan kungiyoyin wakilan al'adu na gwamnatoci na tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika ya kai kusan 230, sa'anan kuma yawan kungiyoyin nuna wasannin fasaha da suka kai wa juna ziyara ya kai kusan 300. Ban da wannan kuma, kasar Sin da kasashen Afrika sun kuma shirya wa juna bakukuwan al'adu da na nuna wasannin fasahohi da nune-nune, har da yin musanya da hadin guiwa wajen harkokin littattafai da dabi da watsa labaru da gidan rediyo da sinima da kayayyakin tarihi da gidajen baje koli da yin amfani da karfin leburori da dai sauransu.

Ana amince cewa, bayan taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, huldar da ke tsakanin bangarorin biyu tabbas ne za ta kara samun sabon ci gaba, ciki har da ma'amalar al'adu da hadin guiwa a tsakaninsu.(Halima)