Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-15 16:07:59    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(09/11-15/11)

cri
Ran 12 ga wata Hadaddiyar Kungiyar Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Duniya wato IAAF ta sanar da dukan lambobin yabo na shekarar 2006, dan wasan gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 Liu Xiang na kasar Sin ya sami lambar yabo ta nuna rawar gani ta shekarar 2006, saboda ya karya matsayin bajimta na duniya a Lausanne a watan Yuli na shekarar bana. Sa'an nan kuma, shahararren maguji Asafa Powell na kasar Jamaica ya zama dan wasa mafi nagarta na shekarar 2006, magujiyar gudu mai tsawon mita 400 Sanya Richards ta kasar Amurka ta zama 'yar wasa mafi nagarta ta wannan shekara.

An bude gasar cin kofin Masters ta wasan kwallon tennis ta shekarar 2006 da Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Tennis ta Kwararru Maza ta Duniya wato ATP ta shirya a birnin Shanghai na kasar Sin a ran 12 ga wata. Za a kammala wannan muhimmiyar gasa a ran 19 ga wata.

Ban da wannan kuma, a an 12 ga wata, a birnin Madrid na kasar Spain, sansanniyar 'yar wasa Justine Henin-Hardenne ta kasar Belgium ta lashe 'yar wasa Amelie Mauresmo da ci biyu ba ko daya a cikin zagayen karshe na gasar fid da gwani na wasan kwallon tennis da kungiyar WTA ta shirya, ta haka ta zama zakara a cikin wannan gasa a karo na farko.

Ran 12 ga wata, a birnin Guangzhou da ke kudancin kasar Sin, kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin ta lashe takwararta ta kasar Cameroon da cin daya ba ko daya a cikin wata gasar motsa jiki. Kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin tana share fage ga taron wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing a shekarar 2008.

Akwai wani labari daban game da wasan kwallon kafa, an ce, a ran 12 ga wata, a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, a cikin zagayen karshe na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa kan rairayin bakin teku da Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta Duniya wato FIFA ta shirya a karo na 2, kungiyar kasar Brazil ta lashe kungiyar kasar Uruguay da cin 4 da 1, ta haka ta zama zakara saboda cin nasara a cikin dukan gasannin da ta yi a wannan gami. Kungiyar kasar Uruguay ta zama ta biyu, kungiyar kasar Faransa kuma ta zama ta uku.(Tasallah)