Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-14 16:10:38    
Hasumiyar Zhenhailou

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu bayyana muku wasu abubuwa a kan wata hasumiya mai suna Zhenhailou, daga bisani kuma za mu karanta muku wani bayanin da ke cewa, shiyyar wurare masu ni'ima ta Mulan de ke birnin Wuhan.

Hasumiya ta Zhenhailou tana kan dutse na Yuexiushan a arewacin birnin Guangzhou na lardin Guangdong na kasar Sin. An gina ta a farkon zamanin daular Ming na kasar Sin, ta yi suna ne a birnin Guangzhou. Ma'anar wannan hasumiya a Sinance ita ce yin kaka-gida a teku. An ce, yarimar Yongjia wai shi Zhu Liangzu ya gina wannan hasumiya don nuna bajimta wajen yin kaka-gida a teku da ke arewacin kasar.

Tsayin hasumiya ta Zhenhailou ya kai mita 28 tare da benaye 5. Idan masu yawon shakatawa suka shiga cikin bene na 5, to, za su gane cewa, suna kan bishiyoyi, bishiyoyi suna tsayawa a karkashin kafarsu, za su kuma iya hangen dukan birnin Guangzhou. A zamanin da, an mayar da wannan hasumiya a matsayin wurin shakatawa ne mai ba da nishadi ga manyan jami'ai da madugun sojoji da masu kudi da kuma masu karfi.

An gina hasumiya ta Zhenhailou da katako da kuma tubali, amma a shekarar 1928, an yi mata kwaskwarima, kankare masu karfi sun maye gurbin wadannan kayayyakin gini. Bayan da Japanawa mahara suka mamaye birnin Guangzhou a shekarar 1938, hasumiyar nan ta zama yankin da sojojin kasar Japan suka haramta kowa ya shiga, sannu a hankali hasumiyar ta lalace.

Bayan da aka kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, sabuwar gwamnatin kasar Sin ta yi kwaskwarima kan hasumiyar Zhenhailou sau da yawa, har ma ta tanadi wannan hasumiya a kan takardar sunayen wuraren tarihi na kasar Sin. Yanzu wannan hasumiya ta zama dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na birnin Guangzhou, wanda aka raba shi zuwa kashi 2.

A cikin wani kashi na wannan dakin nune-nunen kayayyaki tarihi, an nuna tarihi da kuma wayewar birnin Guangzhou. A cikin wani kashi daban kuma, an nuna kayayyakin tarihi da tsoffin hotuna da takardu kan wasu muhimman juyin juya hali, wadanda suka nuna jaruntakar birnin Guangzhou da kuma ta jama'arta a fannin yin gwagwarmaya da 'yan mulkin mallaka da mahara a zamanin kusa da na yanzu.(Tasallah)