Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-14 16:00:39    
Shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium zai rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa ga tsofaffi mata

cri

A cikin shirinmu na yau, da farko za mu yi muku bayani kan cewa, shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium zai rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa ga tsofaffi mata, daga baya kuma za mu karanta muku wani bayani mai lakabi haka: Kasar Sin tana yin kokari domin kyautata sharudan kiwon lafiya na yankunan da ke fama da talauci. To, yanzu ga bayanin.

Manazarta na kasar Australia sun gano cewa, idan tsofaffi mata suna shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium a ko wace rana, to za a iya rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa gare su, amma muhimmin abu shi ne ya kamata a tsaya tsayin daka kan shan magungunan ba tare da kasala ba.

Mata 1460 da shekarunsu ya zarce 70 da haihuwa sun shiga nazarin. Wasu mata daga cikinsu suna shan kwayoyin calcium sau biyu a ko wace rana, kuma yawan kwayoyin calcium da suke sha a ko wane karo ya kai miligram 600, sauran mata kuwa suna shan magunguna marasa illa ga jiki domin taimaka musu wajen samun sauki. Daga baya kuma an gano cewa, shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium zai ba da taimako wajen rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa ga tsofaffi mata.

Haka kuma manazarta sun bayyana cewa, lalle shan magungunan ba da kariya ga lafiya da ke kunshe da sanadarin calcium zai ba da taimako ga tsofaffi mata waje rage hadarin kamuwa da karewar kasusuwa, amma ana fuskantar wata matsala, wato mutane da yawa ba su iya tsayawa tsayin daka kan shan magunguna cikin dogon lokaci ba. Kusan rabi daga cikin matan da suka shiga nazarin ba su iya tsayawa kan shan magungunan da ke kunshe da sanadarin calcium ba. Kuma a cikin mata 310 da suka sha magungunan yadda ya kamata, yawansu da suka samu karewar kasusuwa ya kai kashi 10 cikin dari a cikin shekara guda, amma a cikin matan da suka sha magunguna marasa illa ga jiki domin taimaka musu wajen samun sauki, yawansu da suka samu karewar kasusuwa ya kai kashi 15 cikin dari.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, Kasar Sin tana yin kokari domin kyautata sharudan kiwon lafiya na yankunan da ke fama da talauci.(Kande)